Labaran ƙarya da bayanan da ba su da tushe sun ci gaba da yaɗuwa a kafafen sada zumunta a wannan makon, musamman kan batutuwan mulki, addini, tsaro da tattalin arziki.
A cikin wannan makon, DUBAWA ta binciki iƙirari daban-daban da suka karaɗe kafafen sada zumunta, inda ta yi amfani da bayanan hukuma, rahotanni masu inganci da kuma fasahohin tantance sahihancin labarai na zamani domin rarrabe gaskiya da ƙarya.
Ga wasu daga cikin manyan iƙirarin da muka tantance a wannan makon:
1. Wike ya ce ya gaji kuɗin shiga na FCT a biliyan ₦9 kacal a wata
Ministan Babban Birnin Tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi iƙirarin cewa kafin ya karɓi mulki, FCT na tara biliyan ₦9 kacal a matsayin kuɗin shiga na cikin gida (IGR) a kowane wata, yana mai cewa yanzu kuɗin sun haura biliyan ₦40.
Sai dai binciken DUBAWA kan bayanan da hukumar ƙididdiga ta Najeriya NBS ya nuna cewa tun kafin Wike ya hau mulki, FCT na tara sama da biliyan ₦10 a matsakaici duk wata.
Karanta cikakken rahoton a nan.
2. Bidiyon dake cewa ana bautar da Kiristoci a Arewacin Najeriya
Wani bidiyo da ya bazu a Instagram ya yi iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci tare da bautar da su a Arewacin Najeriya.
DUBAWA ta yi amfani da manhajar binciken hotuna ta reverse image search, inda ta gano cewa bidiyon ya fito ne daga Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo (DRC), kuma yana da alaƙa da kama wasu mutane a lardin Ituri.
Rahotanni masu inganci sun tabbatar da cewa bidiyon ba shi da wata alaƙa da Najeriya ko hare-haren da ake kai wa Kiristoci a ƙasar.
3. Alƙalin da ya ayyana Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen 2023 ya makance?
Wani rubutu a Facebook ya yi iƙirarin cewa alƙalin da ya ayyana Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wanda ya lashe zaɓen shugaban ƙasa na 2023 ya rasa ganinsa bayan tiyatar ido da aka yi masa a Landan.
Binciken DUBAWA ya gano cewa iƙirarin hoton da aka yi amfani da shi na tsohuwar Babbar Alƙaliyar Ghana, Gertrude Torkornoo ne.
Haka kuma, babu wani alƙali mai suna Tsamma Abubakar cikin waɗanda suka saurari ƙarar zaɓen shugaban ƙasa na 2023, kuma babu wata hujja mai inganci da ke nuna cewa wani daga cikinsu ya makance.
Karanta cikakken bayani a nan.
4. Kasar Canada ta kafa dokar haramta ambaton Littafin Bible
Wani saƙo da ya bazu a kafafen sada zumunta ya yi iƙirarin cewa sabuwar dokar Yaƙi da Ƙyama ta Kanada ta haramta faɗi ko ambaton ayoyin Bible, lamarin da ake cewa ya tauye ‘yancin addini.
DUBAWA ta binciki dokar, inda ta gano cewa ba ta haramta karantawa, wa’azi ko koyar da Littafin ba.
Abin da dokar ta yi shi ne yin wasu gyare-gyare ga dokokin yaɗa ƙiyayya ta ƙasar, tare da ci gaba da sanya ƙaƙƙarfan sharudda kafin a ayyana wani da laifi.
Karanta ƙarin bayani a nan.
5. Kwatanta Najeriya da Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE) ya yi kuskure
Wani mai amfani da X ya yi iƙirarin cewa duk da Najeriya ta gano man fetur kafin Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa (UAE), yanzu UAE tana da arzikin dala biliyan 700, yayin da Najeriya ke bin bashin dala biliyan 500.
DUBAWA ta tabbatar da cewa Najeriya ta fara gano man fetur na kasuwanci shekaru biyu kafin UAE.
Sai dai bayanan hukumomi sun nuna cewa bashin gwamnatin Najeriya ya kai kusan dala biliyan 111 ne, ba dala biliyan 500 ba. Haka kuma, kimar dukiyar UAE ta zarce dala tiriliyan uku, wanda ke nuna kwatancen da aka yi ba daidai ba ne.
Karanta cikakken rahoton a nan.
6. Bidiyon rikicin Sudan da aka danganta da harin Zamfara
Wani bidiyo ya bazu yana nuna Hausawa da Fulani ‘yan ta’adda suka kai wa hari tare da raba da muhallansu a ƙaramar hukumar Bungudu ta jihar Zamfara.
DUBAWA ta yi amfani da manhajar binciken hotuna ta reverse image search, inda ta gano cewa bidiyon ya fito ne daga garin El Fasher da ke yankin Arewacin Darfur na ƙasar Sudan.
Kungiyar Amnesty International da wasu ƙungiyoyi sun ruwaito cewa bidiyon yana da alaƙa da fararen hula da suka tsere daga rikicin da dakarun Rapid Support Forces (RSF) suka haddasa.
Babu wata hujja da ta nuna cewa bidiyon yana da alaƙa da Zamfara, don haka iƙirarin yaudara ne.