Round-Up: Peter Obi, harin Gwoza, Biafra da sauran manyan ikirarin da aka tantance a wannan makon

Batun siyasar Najeriya da rikice-rikicen kasa da kasa ne suka fi daukar hankalin mutane a kafafen sada zumunta a wannan makon.

Yayin da rikici ke ci gaba a Gabas ta Tsakiya, mun lura da yunkuri da dama na danganta tsofaffin bidiyo da abubuwan da suka faru a kasashen waje da labaran Najeriya.

Daga kirkirarrun kalaman siyasa zuwa bidiyon tsaro da aka fassara ba daidai ba, DUBAWA ta binciki wasu daga cikin da’awar da aka fi yadawa. Ga wasu daga cikinsu da kuma abin da bincikenmu ya gano.

  1. Peter Obi ya ce dole ne tsadar abinci ta ci gaba domin kare manoma

Yayin da Najeriya ke fuskantar manyan kalubalen tattalin arziki da hauhawar farashi, wani bayani ya yaɗu a kafafen sada zumunta da aka danganta ga dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour a zaben 2023, Peter Obi.

Sakon ya yi ikirarin cewa Obi ya ce tsadar abinci dole ne ta ci gaba domin tabbatar da cewa manoma suna samun riba kuma ana kare su.

Bincikenmu ya nuna cewa ikirarin yaudara ce. Mai amfani da Facebook din ya fassara maganar Obi kan shigo da abinci daga kasashen waje da tasirinsa ga manoma a matsayin kira da a bar farashin abinci ya yi tsada domin ceton manoma.

Ga cikakken bayani a nan.

  1. Bidiyon kisan gilla a Burkina Faso an danganta shi da Gwoza, Borno

Batun tsaro na ci gaba da daukar hankali a arewa maso gabashin Najeriya. Kwanan nan wani mummunan bidiyo ya bazu a Facebook, inda wasu suka ce sabon harin ta’addanci ne da aka kai a Gwoza, jihar Borno.

Bidiyon ya haifar da fargaba sosai a tsakanin mazauna yankin da masu bibiyar al’amuran tsaro. DUBAWA ta gudanar da binciken ta manhajar Google da kuma nazarin kan bidiyon.

Mun gano cewa an dauki bidiyon ne a harin da aka kai kauyen Solhan a Burkina Faso a 2021, inda ‘yan bindiga suka kashe fararen hula da dama tare da tilasta wa mazauna kauyen tserewa daga gidajensu. Bidiyon ba shi da wata alaka da Gwoza ko wani sabon lamari a Najeriya.

Latsa nan don cikakken bayani.

  1. Kiristocin Najeriya sun yi gangami don nuna goyon baya ga Amurka da Isra’ila

Yayin da rikicin soji ke karuwa tsakanin Amurka, Isra’ila da Iran, wani sako ya bayyana a shafin X yana cewa Kiristocin Najeriya sun gudanar da gangami a Abuja domin nuna goyon baya ga kawancen Amurka da Isra’ila. Sakon ya nuna cewa gangamin martani ne kai tsaye ga rikicin da ke faruwa a Gabas ta Tsakiya.

Sai dai binciken DUBAWA ya nuna cewa ikirarin mai yaudara ne.

Ko da yake bidiyon gaske ne, mun gano cewa gangamin mambobin kungiyar masu rajin ballewar Biafra ne suka shirya shi, kuma ba ya wakiltar Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ko mafi yawan Kiristocin kasar.

Karanta cikakken rahoto a nan.

  1. An yaɗa tsohon bidiyo shi a matsayin sabuwar zanga-zangar Biafra

Wani bidiyo ya sake bayyana a intanet da ikirarin cewa yana nuna sabuwar zanga-zangar masu goyon bayan Biafra da ke neman Amurka da Isra’ila su shiga cikin batunsu. Sakon ya nuna cewa zanga-zangar ta faru ne sakamakon sabbin sauye-sauyen siyasar duniya.

Ta hanyar binciken bidiyon, DUBAWA ta gano cewa an fara wallafa bidiyon a intanet tun 2019, sannan ya sake bayyana a 2024, shekaru kafin rikicin da ya kunno kai a 2026 tsakanin Iran, Isra’ila da Amurka.Duba cikakken rahoton a nan.

Exit mobile version