Site icon Dubawa

Hoton bidiyon da ke nuna ‘yan ta’adda yayin da suke daukar ma’adinai da wani jirgin saman Turkiyya yaudara ce

Video showing terrorists moving minerals through Turkish Aircraft, misleading

Da’awa: wani mai amfani da shafin X @JezebelReborn, ya wallafa wani bidiyo inda ya ke da’awar fallasa yadda ‘yan ta’adda Filani  ke safarrar ma’adinan da suka kwashe a cikin wani jirgin saman Turkiyya.

Hoton bidiyon da ke nuna ‘yan ta’adda yayin da suke daukar ma’adinai da wani jirgin saman Turkiyya yaudara ce

Hukunci:  Yaudara ce! Bidiyon bai nuna ‘yan ta’adda suna safarar ma’adinai a jirgin Turkiyya ba. Jirgin na Rasha ne kuma an dauki bidiyon ne a Sudan

Cikakken bayani

Mai amfani da shafin X, JezebelReborn, ya wallafa wannan batun ranar 3 ga watan Yunin 2026 ya wallafa bidiyon da ke da’awar cewa ‘yan ta’adda sun yi amfani da wani jirgin saman Turkiyya wajen yin safarar wasu ma’adinai daga kasar wadanda suka samu ta haramtattun hanyoyi.

Wannan bidiyon (wanda aka adana a  nan) ya nuna wani jirgin sama yayin da wasu sojoji wadanda ke sanye da kayayyakinsu suna guda za su shiga jirin yayin da wasu kuma suke dauke da wasu buhuna masu nauyi.

“BIDIYO: ‘Filani ‘yan ta’adda suna safarar ma’adimai daga kasar a cikin jirgin saman Turkiyya. Me ya sa gwamnatin ba ta yin komai?” a cewar taken da aka yi wa bidiyon.

Daga 4 ga watan Yunin 2026, labarin ya riga ya dauki hankali sosai, an kalla sau 78,500, mutane 683 sun yi tsokaci sa’annan an sake rabawa sau 4,100, wasu 1,400 sun adana shi dan sake dubawa nan gaba. Yawancin wadanda suka yi tsokaci sun yi bayanai daban-daban. 

Wani mai amfani da shafin  X, Balogun Joseph (@balogin) ya rubuta cewa, “Ku na marmarin kurkuku saboda kudin Elon Musk. Ku yi ta wallafa bidiyoyin bogi. Wannan ba Najeriyaba ne. Ana iya ganinku duk inda kuke.”

“Wato dalilin da ya sa Gumi ya ce gwamnatin Najeriya ta nemi tallafi daga gwamnatin Turkiyya ke nan, wadda yanzu muka san cewa ta na daukar nauyin ta’addanci. Ke nan gwamnatin Tinubu ta je ta nemi tallafi wajen su ke nan,” a cewar ” Omenka (@C_Omenka).

Wani shi ma mai amfani da shafin, Emeka Ezeanya (@EmekaEzeanya), ya rubuta cewa, “Filani ‘yan ta’adda suna daukar ma’adinai da rana tsaka suna sanyawa cikin jiragen kasashen waje kuma muna da gwamnati. Haka suke badakala da Najeriya yayin da talakawa ke wahala. A shekarar 2027 za mu sauya duk wannan rashin mutuncin.”

Wannan da’awar ta yadu sosai a Facebook ana iya ganin ta a nan, nan, nan, nan, nan, da nan.

Ganin yadda ra’ayoyin suka banbanta suka kuma kasance da sarkakiya ne ya sa DUBAWA ta dauki nauyin tantance batun.  

Tantancewa 

DUBAWA ta yi amfani da manhajar tantance sahihancin bidiyoyi na InVid dan yin nazarin hotunan. Wannan binciken ne ya nuna cewa wannan bidiyon ba daga Najeriya ba ne. 

Haka nan kuma ha da mu da wani labari da aka wallafa a mujallar Tell, wand ya nuna cewa sojojin da ke bidiyon kayan sojojin dakarun Chadi nesuke sanye da su. Bacin haka mujallar ba tayi wani karin bayani ba.

Mun kuma sanya lambar jirgin “RA-25659” wanda shi ne aka rubuta a jikin jirgin cikin shafin da ke bayyana lambobin jiragen Rasha Russiaplanes.net a nan ne muka gano ainihim lambar da aka yi rajistan jirgin da shi: Mil Mi-8MTV-1 Registration Number: RA-25659.

Hoton bidiyon da ke nuna ‘yan ta’adda yayin da suke daukar ma’adinai da wani jirgin saman Turkiyya yaudara ce

Screenshot of the aircraft details found.

Mun yi amfani da google wajen fassara dan fahimtar bayanan da muka gani a  nan. Daga fassarar mun fahimci cewa an sarrafa jirgin ne ranar 30 ga watan Disemba a shekarar 1981 kuma a wannan shekarar ne aka fara amfani da shi.

Bayanan sun nuna inda aka sarrafa jirgin, a kamfanin sarrafa jirage masu saukar ungulu na Kazan Helicopter Plant, wannan kamfanin ne ke sarrafa duk jiragen Rasha. Lambar da aka baiwa jirgin sadda aka sarrafa shi shi ne: 93219, sa’annan kuma serial number: 32-19.

The details revealed that the aircraft, which had been “In Service” since 1988, had been operated by an unknown airline since July 18, 2017. 

“A shekarar 1988, jirage 280 irin shi, wato kirarar OVP na aiki a Kandahar. Bisa tanadin kuduri mai lamba 799 ta gwamnatin Jamhuriyar Kazakhstan mai kwanan wata 11 ga watan Yunin 2001, daga nan ne aka tura shi zuwa kamfanin fitar da kayayyaki na kasa dan saidawa. UNO-755 Sudan,” Fassarar bayanin da ke karkashin teburin shafin ke nan.

A Karshe 

Da’awar cewa ‘yan ta’adda ne ke daukar makamai cikin jirgin Turkawa yaudara ce. Hujjoji sun nuna cewa jirgin Rasha ne. 

Cibiyar samar da sabbin dabaru da ci-gaban aikin jarida (CJID) ke aiwatar da wannan shirin na horas da ‘yan jarida tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.

Exit mobile version