Site icon Dubawa

Ƙarya ce! Sarkin Musulmi bai ziyarci Nnamdi Kanu a gidan yari na Sakkwato ba

Sarkin Musulmi. Mallakar hoto: Sultanate Council/FB.

Sarkin Musulmi. Mallakar hoto: Sultanate Council/FB.

Da’awa: Wani mai amfani da Facebook ya yi ikirarin cewa Sarkin Musulmi ya ziyarci Nnamdi Kanu a gidan yari domin tattauna daukaka ƙarar hukuncinsa tare da roƙonsa ya yi watsi da batun ballewar Biafra. Wannan lamarin ya ja hankalin masu bibiyar nnamdi kanu news.

Ƙarya ce! Sarkin Musulmi bai ziyarci Nnamdi Kanu a gidan yari na Sakkwato ba

Hukunci: Ƙarya ce. DUBAWA ba ta samu wata shaida da ke nuna cewa Sarkin Musulmi ya ziyarci Nnamdi Kanu a gidan yari ba. Wani mamba na Majalisar Fadar Sarkin Musulmi ya karyata ikirarin.

Cikakken Bayani 

Shari’ar da ta shafi shugaban ƙungiyar ƴan awaren Biyafara, Nnamdi Kanu, na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin shari’un da suka fi ɗaukar hankalin jama’a a Nijeriya.

Haka kuma, Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar III, na da muhimmanci sosai a matsayinsa na jagoran addinin Musulunci a Nijeriya, kuma an san shi da ƙoƙarin samar da zaman lafiya, tattaunawa da haɗin kan ƙasa.

Kanu, wanda ke fuskantar tuhume-tuhumen da suka shafi ta’addanci daga gwamnatin tarayya, ya kasance cikin ce-ce-ku-ce na siyasa da shari’a tun bayan kama shi da kuma dawo da shi Nijeriya daga Kenya a shekarar 2021.

Bayan shekaru ana gudanar da shari’a, an same shi da laifukan da suka shafi ta’addanci tare da tsare shi a Cibiyar Gyaran Hali ta Sakkwato a ranar 20 ga Nuwamba, 2025, inda yake ci gaba da zaman hukuncinsa yayin da ake ci gaba da shari’o’i da daukaka ƙarar da ke gaban kotu.

A wannan yanayi ne wani mai amfani da Facebook ya wallafa wani bidiyo yana ikirarin cewa Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya ziyarci Nnamdi Kanu a gidan yari domin tattauna batun daukaka ƙarar hukuncinsa.

A cikin rubutun da aka wallafa da bidiyon, wanda aka adana a nan, mai ikirarin ya kuma ce Sarkin Musulmin ya roƙi Kanu da ya yi watsi da kiran ballewa tare da goyon bayan haɗin kan Nijeriya.

Zuwa ranar 11 ga Yuni, 2026, sakon ya samu masu kallo sama da 42,000, an yi sharhi 217 da kuma yaɗawa sau 421 cikin sa’o’i shida kacal.

Ikirarin ya haifar da ra’ayoyi mabambanta daga masu amfani da shafukan sada zumunta.

Wani mai amfani da shafin, Don Ben Ikele Benedict, ya nuna kamar ya yarda da ikirarin.

“Lokacin yin hakan ya wuce. Mazi Nnamdi Kanu ya gaya musu tun da farko cewa irin wannan lokaci zai zo” in ji shi.

Sai dai wani mai amfani da shafin, Yusuf Ismail, ya nuna shakku kan sahihancin labarin.

“Labarin kafafen sada zumunta ne kawai. Kana tare da su ne?”

Saboda yadda ikirarin ya shafi manyan mutane kuma zai iya yaudarar jama’a, DUBAWA ta binciki gaskiyarsa.

Tantancewa

DUBAWA ta bincika rahotanni daga manyan kafafen yaɗa labarai na Nijeriya da kuma hanyoyin sadarwa da ke da Fadar Sarkin Musulmi domin tabbatar da ikirarin.

Binciken bai gano wani sahihin rahoton labari, sanarwa a hukumance, hoto ko bidiyo da ke nuna cewa Sarkin Musulmi ya ziyarci Nnamdi Kanu a Cibiyar Gyaran Hali ta Sakkwato ba.

Idan har irin wannan ziyara ta faru, kasancewar mutanen biyu fitattun mutane ne a Nijeriya, da tabbas za ta jawo hankalin jama’a tare da samun rahoto daga kafafen yaɗa labarai.

DUBAWA ta kuma tuntubi wani mamba na Majalisar Fadar Sarkin Musulmi, Sa’in Kilgori, Muhammad Jabbi, wanda ya bayyana ikirarin a matsayin ƙarya.

A cewarsa, Sarkin Musulmi bai ziyarci Nnamdi Kanu a gidan yari ba, kuma babu wata ganawa makamanciyar haka da ta gudana.

A ƙarshe 

Ikirarin cewa Sarkin Musulmi ya ziyarci Nnamdi Kanu a gidan yari na Sakkwato domin tattauna batun daukaka ƙarar hukuncinsa tare da roƙonsa ya yi watsi da kiran ballewa daga Najeriya ƙarya ce.

Exit mobile version