Site icon Dubawa

Sashen yaɗa labarai na Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa bayan binciken DUBAWA kan ikirarin goyon bayan Tinubu

Sultan’s media team issues clarification after DUBAWA fact-check on viral Tinubu endorsement claim

Sarkin Musulmi. Hakkin Mallakar Hoto: FB/Mataimakin Gwamnan Jihar Sokoto

Bayan DUBAWA ta wallafa binciken tantance gaskiya kan ikirarin cewa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya bayyana goyon bayansa ga wa’adin mulki na biyu na Shugaba Bola Ahmed Tinubu, sashen yaɗa labarai na fadar Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa a hukumance tare da ƙaryata ikirarin da jaddada cewa Sarkin Musulmi ba ya goyon bayan wani ɗan takara na siyasa.

A binciken nata, DUBAWA ta gano cewa wani bayani da ya yaɗu a kafafen sada zumunta ya karkatar da ma’anar jawabin da Sarkin Musulmi ya gabatar a wajen Taron Ƙasa na shekarar 2026 na Ƙungiyar Makiyaya ta Najeriya (MACBAN).

Binciken ya nuna cewa Sarkin Musulmin yana yabon Shugaba Tinubu ne saboda kafa Ma’aikatar Raya Kiwo ta Tarayya da kuma goyon bayan sauye-sauyen da ake yi a fannin kiwo, ba wai yana goyon bayan sake tsayawarsa takara ko kuma yana kira ga ‘yan Najeriya su zaɓe shi a shekarar 2027 ba.

Sa’o’i kaɗan bayan wallafa rahoton DUBAWA, sashen yaɗa labarai na fadar Sarkin Musulmi ya fitar da sanarwa mai ɗauke da kwanan watan 4 ga Agustan 2026, inda ya yi watsi da rahotannin da ke ikirarin cewa Sarkin Musulmi ya goyi bayan takarar Shugaba Tinubu ta wa’adi na biyu.

Sanarwar, wadda Prince Bashir Adefaka ya sanya wa hannu a madadin sashen yaɗa labarai na fadar Sarkin Musulmi, ta jaddada cewa, “Sarkin Musulmi, a matsayinsa na uba ga kowa, ba shi da wani ɗan takarar da ya fi so a zaɓen 2027.”

Sashen na yaɗa labarai ya kuma bayyana cewa sarautar Sarkin Musulmi ba ta bashi damar nuna ɓangare a siyasa, sai dai ci gaba da ba wa dukkan ‘yan Najeriya shawarwari, sanya albarka da jagoranci ba tare da la’akari da bambancin ra’ayin siyasa ba.

Exit mobile version