Site icon Dubawa

Shin ana dawo da kudin beli? Abubuwan da ya kamata a sani game da bayar da beli a Najeriya 

Can bail be refunded? All you need to know about bail in Nigeria

Shekaru masu yawa ‘yan Najeriya da ‘yansanda suka kama su kan jira hukuncin kotu, wasu lokutan su kan nemi a ba da su beli na wucingadi kafin a kammala shari’a karkashin doka.

A baya-bayan nan wani mai amfani da shafin X @Chudy_jnr, yayi tambaya da cewa me zai faru idan mutum na gaban shari’a sai aka gano cewa bashi da laifi aka wanke shi bayan kuwa a baya ya biya kudin beli naira miliyan 5.

Mai amfani da shafin na X ya kara da cewa ko za a iya dawo masa da kudinsa ko dai kudin zai ci gaba da kasancewa a hannun kotu ko kuwa shi wanda yayi karar tasa shi zai biya kudin?

A wani bangaren aikin DUBAWA na samar da ilimi kan abubuwan da suka shafi yada labarai da samar da bayanai ingantattu, mun yi wannan rubutu don warware zare da abawa kan wannan batu da ma tanadin doka a akai.

Me doka ta ce a game da batun na ba da beli? 

Beli ana bayyana shi a matsayin sakin mutum na wucin gadi bayan kama shi aka tsare saboda wani laifi da ya aikata aka tsare shi a hannun ‘yansanda ko kuma tsarewar kotun shari’a. Ana ba da shi ne bayan an biya wasu kudade ko ta dalilin yin wani alkawari ko ba da tabbaci cewa wanda ake sharia a kansa zaa kawo shi a duk lokacin da aka bukaci yin hakan lokacin da ake shari’a ko ake gudanar da bincike. Idan wanda ya biya belin ya gaza dawo da mutumin ana iya rike wadannan kudade. 

Duk sanda aka ce an ba da belin mutum, ana sakinsa ta dalilin wanda ya tsaya masa da ba da tabbaci ko yin alkawari a kotu ya danganta da ka’idoji da ‘yansanda ko kotu suka shimfida.

Beli ya kasu kashi uku: Akwai wanda ‘yansanda ke bayarwa kafin a kammala bincike da wanda kotu ke bayarwa kafin a kammala shari’a da wanda kotu ke bayarwa gabanin daukaka kara.

DUBAWA ta nazarci tanade-tanade da kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999 ya tanada karkashi Sashi 34 da 35 kan dokar walwalar dan’Adam da ‘yanci na mutum da duk dan Najeriya ke da shi.

Nazari a wasu makalu ma ya tabbatar da cewa ‘yanci na ba da beli ya samu ne daga kundin tsarin mulkin kasa musamman Sashi 36(5), wanda ya bayyana cewa ko da an samu mutum da aikata laifi za a dauka bashi da laifi har sai kotu ta kama shi da tabbatar masa da laifin.

A amsar da aka bawa mai amfani da shafin na X DUBAWA ta kara zurfafa bincike inda ta gano cewa duka nau’ikan belin ko da na ‘yansanda ko na kotu da zarar an kammala shari’a aka gano mutum ba shi da laifi, aka kuma wanke shi to ya zama wajibi a mayar da kudaden da aka karba na belinsa.

Don haka wannan mutumin sai ya tuntubi shugabancin na ‘yansanda ko bangaren shigar da sharia a kotu a dawo masa da kudadensa.

Me lauyoyi ke cewa

Ifeoluwa Olayiwola, wata lauya da ke zaune a Abuja ta ce dokar Najeriya ta tanadi cewa mutumin da aka kama ba tare da sammaci ba a lokacin bincike akwai iya wa’adin da ya kamata a tsare shi.Ifeoluwa tace lokacin baya wuce sa’oi 24 zuwa 48.

“Ya zama kusan abin da za a iya cewa da wahala ya yiwu, a tsare mutum da aka kama cikin lokacin da doka ta tanada, idan ‘yansanda suka kama mutum sai su kai shi kotu idan ba ta da nisa daga ofishin ‘yansanda, idan ba haka ba kuma dole ‘yansanda su ba da belinsa,” kamar yadda ta fadawa DUBAWA.

Lauyar ta kara da cewa beli a hannun ‘yansanda ba a ba da kudi, idan ana gudanar da bincike kamar yadda doka ta tanada, sai dai a aikace ba haka abun yake ba.

“A tsarin dokar Najeriya beli kyauta ne, bai kamata ka ba wa kowa kudi ba sai dai a Najeriya komai an siyasantar da shi, zai wahala a ce mutum ya je ofishin ‘yansanda ba tare da ya ba da ko sisi ba.”

Lauya Ifeoluwa ta kara da cewa mutumin da ake masa shari’a ana iya ba da belinsa, idan ya cika ka’idoji na beli a sammacin da aka kai masa, idan kuma mutum ya tsallake sharudan na beli kotu na da damar rike kudaden da ya biya a matsayin na beli, kuma za a iya kama wanda ya tsaya masa.

“Ma’ana kudaden sun zama na kasa ko gwamnati, idan mutum yaki mutunta sharudan beli kuwa, wadannan kudade ba za su je aljihun kowane jami’in kotu ba face asusun gwamnati.” Kamar yadda tayi karin haske.

Wane lokaci ne ake dawo da kudin beli ko a karba? 

A nasa tsokaci Mustapha Toheeb, lauya mai zaman kansa a jihar Legas yace mutumin da aka wanke yana da damar karbar kudaden da ya bayar beli  da zarar an cika sharuda na dalilan da ya sa ya ajiye kudaden.

Yace dalilin biyan kudadensa ba na yin hukunci ba ne ga wanda ake zargi ko don neman kudade da zaa tarawa gwamnati ne, ana karba ne don a tabbatar da ganin cewa wanda ake zargi na halartar zaman kotu.

“Da zarar yana halartar zaman kotu kuma zaman sauraren shari’ar lefin ya kawo karshe ko alkali ya wanke shi ko ya sallame shi, ko wani abu haka , kudaden da aka bayar a matsayin na beli za a mayarwa wanda ya kamata a bashi kudinsa, muddin ba alakali ne ya ba da umarni a kwace ba, saboda shi kudin na beli ba fata ake ya zama mallaki na gwamnati ba”, a cewar lauyan.

Mustapha ya kafa hujja da Sashi na 32(2) na dokar aikata laifuka ta (ACJA); Jim-Jaja da Kwamishinan‘yansanda da Augustine Eda da kwamishinan ‘yansanda a (1982), inda kotunan Najeriya a lokuta da dama suka ci gaba da yin Allah wadarai  da batun karbar kudade kafin ba da beli a fadin kasa.

Sai dai lauyoyin sun fadawa DUBAWA cewa a wasu lokutan kudaden beli su kan zama mallakin gwamnati idan an ba da umarni na a kwace.

A cewar lauyoyin wannan kudaden na beli ana kaiwa ga karbarsu ne idan wanda ake shari’ar da shi ya gaza cika sharudan da aka gindaya masa a cikin belin.

Suka nunar da cewa kotunan Najeriya na da dama karkashin tsarin doka mai lamba ACJA 2015 su karbi kudaden beli idan aka karya sharudan da aka gindaya na belin. 

Wata lauyar mai suna Kawthar Omisore, da ke aiki da kamfanin lauyoyi na Afe Babalola & Co., ta bayyana cewa idan aka nemi wani ya ba da kudin beli to ya koma ya karbi kudinsa kasancewar karbe kudaden ya saba dokoki na shari’a.

Wannan ya hadar da: Neman umarnin kotu na neman ‘yansanda su dawo da kudaden da suka karba ba bisa ka’ida ba, ana iya kai kara zuwa hukumar da ke kula da ‘yansanda  a kai kara sashen kai korafi na (PCRU) na hukumar.

“Al’adar neman karbar kudade a hannun mutum da sunan beli da ‘yansanda ke yi wannan ya saba doka, kuma a tsarin doka idan aka yi wani abu ba daidai ba akwai mafita” a cewar Kawthar.

A karshe 

Binciken DUBAWA ya gano cewa a karkashin dokar Najeriya ba da beli kyauta ne, don haka babu inda aka ce a ba da wasu kudade ba tare da umarnin hukuma ba. Kwararrun a fannin shari’a suka ce mutumin da aka karbi kudade a hannunsa ba bisa ka’ida ba da sunan beli, yana iya ya nemi a dawo masa da kudadensa daga ofishin ‘yansandan da aka karba ko zai iya kai korafi a sashin karbar korafi na rundunar ‘yansandan. 

Har ila yau bincikenmu ya gani cewa kudaden da aka ajiye na beli idan aka cika sharudan belin ya kamata a mayar da su ga me su baki daya.

Exit mobile version