Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook, @Celebrity Blogger, ya rubuta cewa shugaban kasar Afurka ta Kudu Cyril Ramaphosa, ya bukaci gwamnatin Najeriya ta saki Nnamdi Kanu don samun zaman lafiya a kasar.

Hukunci: Karya ce. Shirin DUBAWA ya fahimci cewa babu wata sheda sahihiya da ta tabbatar da wannan da’awa. Bayanan da aka tattara daga dukkanin bangarorin kasashen sun tabbatar da cewa babu inda aka gabatar da wannan bukata.
Cikakken Bayanin
A ranar 20 ga watan Nuwamba, 2025 shugaban haramtacciyar kungiyar ‘yan awaren Biafra Nnamdi Kanu, an yanke masa hukunci bisa laifuka bakwai da aka same shi da su masu alaka da ta’addanci inda aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai a wata kotun Najeriya. Ya dai ki amincewa da daukaka kara, sannan kotu ta fada masa cewa duk wani yunkuri na neman shari’a a wajen Najeriya hakan haramun ne ya saba kundin tsarin mulkin kasa.
Ko bayan yanke wannan hukunci an ci gaba, da cece-ku-ce kan batun, tare da wasu da’awowi da DUBAWA ta fayyace.
Wani mai amfani da shafin Facebook @Celebrity Blogger yayi da’awar cewa Shugaban kasar Afurka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya bukaci a saki Nnamdi Kanu. Mai da’awar ya kara da cewa neman kare kai ba laifi ba ne karkashin dokar kasa da kasa kuma kowa yana da hakki a saurare shi a kotu.
Wallafar ta kammala da cewa ci gaba da rike Kanu zai iya kara dagula lamura abin da zai zubar da kimar Najeriya a kokarin da ake na samun sulhuntawa.
Wani bangare na wallafar yayi nuni da cewa “Labari da Dumi-Dumi: Shugaban kasar Afurka ta Kudu Cyril Ramaphosa, yayi kira ga gwamnatin Najeriya ta saki Nnamdi Kanu ba tare da sanya wani sharadi ba don samun zaman lafiya a kasar.”
Ya zuwa ranar 7 ga Disamba,2025 wannan wallafa ta samu masu nuna sha’awa wato (Likes) 53 da wadanda suka sake yada labarin su 27 (shares) da masu tsokaci su biyu.
Daga cikin masu tsokaci @Chibuzo Aku yace, “ da Allah a sake shi. Shi danfafutuka ne, ya lura cewa Najeriya bata tafiya yadda ya dace shi ya sanya yake fafutuka saboda al’ummarsa.”
@Master Gold ya kara da cewa “Da Allah a kyale shi ya tafi.”
Babu tantama Nnamdi Kanu lamarinsa na ci gaba da daukar hankali,inda a lokuta da dama a ke fadin abin da ba haka yake ba a game da shi, munga dacewar gudanar da bincike kan wannan da’awa dukmda cewa babu martani sosai a kanta.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da bincikar shafin Fadar shugan kasa a Afurka ta Kudu
Ciki kuwa har da sahihin shafin Shugaba Cyril Ramaphosa sai babu inda aka ga shugaban na bukatar Najeriya ta saki Nnamdi Kanu
Sannan mun binciki wasu kafofin yada labarai na kasar ta Afurka ta Kudu ciki kuwa har da News24 da TimesLIVE da Eyewitness News (EWN), haka kuma kafafan yada labarai na Najeriya duka cikin wadannan babu inda fadar shugaban aka ga ta bayyana wannan bukata. Babu kuma inda aka ga wani bayani ko tattaunawa ko wallafawa ko wani rahoto sahihi.
DUBAWA a tattaunawa da Lebo Tlhabi, wata fitacciyar ‘yarjarida a Afurka ta Kudu kan wannan da’awa tace babu tantanma tana bibiyar labarai na siyasar Najeriya ciki kuwa har da batun na Nnamdi Kanu.
“Tabbas ya kamata kasa ta samu kulawa daga wata takwararta ba kawai don harkar diflomasiya ba don ma zaman lafiyar nahiyar, da duniya da ma al’ummarta. Batun Nnamdi Kanu abu ne da babu wata kasa da za ta sanya bakinta akansa, musamman idan bata da wata bukata a kai, ina tabbatar maka da cewa irin wannan wallafa ana yinta ne don kawai a jawo cece-ku-ce mara dalili a jawo tsana,” a cewarta.
Ta kara da cewa Afurka ta Kudu na da manyan batutuwa da ke gabanta da kalubale don haka babu wani dalili da ma shugabanta zai kutsa kai cikin al’amuran wata kasa.
Tare da taimakon Lebo DUBAWA ya tuntubi Sipho Mbele jami’i mai hulda da kafafan yada labarai a fadar shugaban kasa, mun tuntubi Sipho ta hanyar WhatsApp don neman karin haske amma dai babu wani bayani da aka samu.
Mun kuma yi kokari na tuntubar shafi na gwamnatin shima anan babu wata amsa da muka samu.
A Karshe
Da’awar cewa Shugaban kasar Afurka ta Kudu Cyril Ramaphosa yayi kira na a saki Nnamdi Kanu karya ce babu wata hujja da ta tabbatar da haka.