Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya yada wani bidiyo video yana mai da’awar cewa Mudashiru Obasa shugaban majalisar dokokin jihar Legas ya fada wa al’umma su zabi dantakarar da a baya aka taba kama shi da babban laifi.

Hukunci: Yaudara ce! Da fari an yada shi a shafin TikTok, bidiyon ya nuna yadda Obasa ke ba da umarni ga masu goyon bayan APC da su zabi dantakara da jam’iyya ta amince da shi kada a yi masa hamayya ko da wane irin hali yake da shi.
Cikakken Sako
Wani mai amfani da shafin X @Omoelerinjare, wanda ke da magoya baya sama da 50,000 ya yada wani bidiyo inda yake da’awar cewa Mudashiru Obasa, shugaban majalisar dokokin jihar Legas ya bukaci magoya baya da su zabi duk dantakarar jam’iyyar APC ko da kuwa yana da wani tarihi na aikata babban laifi.
Wannan bidiyo da ke da tsayin dakika 30, an yada shi a ranar 14 ga watan Yuni,2025, “Duk dantakarar da APC ta gabatar ko da kuwa yana da tarihin aikata wani babban lafifi ko kuma babu , muddin APC ta tsayar da shi ba ku da wani zabi sai ku zabe shi ko kuma ku bar jam’iyyar.”
Lokacin da DUBAWA ta nazarci wannan bidiyo a ranar Laraba 18 ga watan Yuni, 2025 ya samu wadanda suka kalla 126,000 (views) da masu nuna sha’awarsu 360 (likes) da wadanda suka sake yadawa su 385 (repost) da wadanda suka nuna alamar za su sake nazartarsa su 170 (bookmarks) da masu kafa hujja 89 (quotes).
A wani bangaren kuwa da aka nazarci sashin masu tsokaci wasu masu amfani da shafin na X sun caccaki jam’iyar ta Obasa saboda irin wadannan kalamai, wasu sun yi fatali da su inda suke cewa ba haka yake nufi ba.
“Bai ce ko mai laifi ko akasin haka ba, yace ne ko me kyau ko mara kyau malam!!!wannan shine abin da yake nufi “a cewar @Phemoragh.
Wani mai amfani da shafin, @Ashman_babane, yayi nasa tsokaci ne da cewa “Najeriya ta tafi. Kalli yadda mutane ke rawa suna jinjina ga wadanda suka wargaza masu rayuwa.”
“Kalmar C a jam’iyyar APC na nufin masu aikata laifi ,” a cewar @Occiandiaali.
DUBAWA taga cewa ya dace ta gudanar da bincike kan wannan da’awa saboda irin yadda za ta iya haifar da rudani a siyasa da yadda take da mabanbantan fassara. Tantancewa
Ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi a Google mun duba ko za mu samu wata kafa da ta ba da wannan rahoto a Najeriya amma babu ko da guda daya.
DUBAWA ta lura cewa bidiyon da aka dora a shafin na X na da alamar cewa daga shafin TikTok yake sai muka yi bincike kuma muka gano cewa bidiyon daga TikTok ne wanda Bodeolabisi ya yada shi a ranar 13 ga watan Yuni,2025 da taken: “Tinubu 2027: Obasa ya bude Orisun House, ofishin yakin neman zabe na Alimosho da Ejigbadero ya bayar.”
Mun lura cewa asalin bidiyon na TikTok footage babu inda yayi maganar da ake dangantawa da Obasa sai dai maganar kaddamar da Orisum House wanda Abiodun Ejigbado jagora a jam’iyyar APC a Legas ya gina saboda Tinubu.
DUBAWA ta fassara bidiyon da aka furta kalamansa a harshen Yoruba, “Jam’iyyar ta zabi wani da kuke cewa shi ko ita basu cancanta ba: Kuna son sauya matsayar jam’iyya ko kuna so ku tafi wata jam’iyyar?” Ko mutum na da halin kwarai ko akasin haka, ita jam’iyyar shi ta ga yafi dacewa.”
Daga fassarar babu inda Mista Obasa ya furta kalamai cewa ko da mutumin mai aikata babban laifi ne, sabanin abin da mai da’awar a shafin na X ya nunar.
A Karshe
DUBAWA ta gano cewa bayanin da aka yi kan bidiyon, ba haka abun yake ba, kasancewar fassara daga Yoruba kan kalaman na Mista Obasa ba haka suke nufi ba, don haka wannan da’awa yaudara ce.