
Da’awa: Yara na bukatar karin shan sukari kafin su samu damar girman jikinsu da kwakwalwarsu.

Hukunci: Yaudara ce! Duk da cewa bincike-bincike da bayanan masana sun bayyana cewa jikin dan Adam na bukatar sukari samfurin Glucose don gudanar da ayyukansa da ci gaba da girman kwakwalwa , wannan abu ne da a cikin halitta ake samunsa daga ajin abinci na carbohydrates ba kayayyakin zaki ba.
Cikakken Sako
Rainon kananan yara na iya zama abu mai wahala musamman ga iyayen da suka yi haihuwa ta farko, kasancewar basu san me ya kamata su yi ba, Iyayen ana samu sun zaku da samun bayanai ko ma neman shawarwari daga mutane “da suke da yara” da kakanni.
A Najeriya mai jego ko mai sabuwar haihuwa na samun tallafi daga ‘yanuwa da suka manyanta misali daga ‘Kaka’ wacce kan ziyarci wacce ta haihu a karon farko don bata kulawar da ta dace wajen kula da yaron da ma ayyuka na cikin gida.
Wannan kuwa a wasu lokutan kan hadar da ba da wasu shawarwari ko yin wasu abubuwa da ka iya zama za su taimaka ko kuma su cutar.
Babban kalubale da iyaye kan fuskanta bayan kammala watanni shida na shayarwa da nonon uwa shine, da me za su fara bawa yaransu, wasu na hadawa da dan kunu da ake hadawa a gida da wasu nau’ikan lemon marmari na kwalba ko roba da sauransu. Yayin da wasu yaran sai sun ga dama za su ci abincin wasu kuwa na sauri-sauri, wasu kuma duk abin da aka basu za su yi amfani da shi.
Tambaya da ke zama sananniya ga irin wadannan iyaye itace, wane adadin sukari yaran ke bukata don kwakwalwarsu ta girma da samun kuzari, musamman ga yaran da suke rarrafe ko wadanda suka fara tsayawa ko ma tafiya su kadai.
Wasu iyaye na da’awa ba tare da samun wata hujja ba a kimiyance cewa yara na bukatar karin sukari a cikin abincinsu musamman don kwakwalwarsu ta girma.
Wannan kuwa ya hadar da iyayen da ke zama tsofaffi wadanda ke dogara da gogewarsu wajen kula da yara.
Irin wannan na sanyawa sabbin iyaye su shiga yanayi na rudani , DUBAWA ta lura cewa sau tari a baya-bayan nan iyaye na zuwa shafukan sada zumunta don neman karin haske ko shin yaransu suna bukatar sukari kafin kwakwalwarsu ta girma.
Don warware wannan matsala DUBAWA ta ga dacewar gudanar da bincike.
Tantancewa
Nazarce-nazarce (Studies) sun nunar da cewa shan sukari da yawa a farkon rayuwar mutum na jawo matsalar samun kiba da hawan jini sannan mutum na iya samun cutar sukari mataki na biyu wato (Type 2 diabetes) nan gaba a rayuwa. Don haka (Therefore), ana shawartar amfani da sukari kadan idan ana hada abinci mai cike da sinadarai da ake bukata wadanda za su inganta rayuwar mutum.
Masu aikin bincike (Researchers) sun nunar da cewa akwai shedu kadan a kimiyance da suka nunar da cewa akwai alfanu a kara sukari a abinci ko sha amma mafi akasari na bincike da aka yi sun nunar da cewa shan sukari da yawa tsawon lokaci na haifar da illa.
Wasu nazarce-nazarce a baya-bayan nan sun nunar cewa wasu lokutan bukatar amfani da sukarin samfurin glucose kan iya tasowa ga wasu mutane, wasu wuraren da ake iya samun wannan samfur na glucose sun hadar da kayan marmari da kayan ganye da wasu nau’ika na hatsi.
Sun kara da cewa duk da babu wasu shedu da suka nunar da cewa adena shan sukari, akwai bukatar a rika lura ana shan daidai misali, idan za a yi duba da shawarwari kungiyar masu lura da masu cutikan zuciya ta (American Heart Association) AHA. AHA dai ta ba da shawarar cewa kada namiji ya sha sukari sama da cokali 9 a rana. yayin da mace ake ba da shawarar kada ta sha sama da cokali 6 a rana.
Kananan yara (Children) daga shekaru biyu zuwa 18 an ba da shawara su sha sukari giram 25 ko kimanin cokali 6, sannan yara da ke kasa da shekaru biyu ba a basu shawarar shan sukari.
Dr. Kayode Alabi, kwararren masanin kula da lafiyar yara a asibitin Garki Hospital, Abuja, ya fadawa DUBAWA cewa rashin fahimtar ta samo asali ne daga kalmar ta ‘Sukari’ wannan bai kamata ta kawo rudani ba.
Ya kara da cewa sukari fari ko launin makuba (brown) da garin dabino ko ruwansa da zuma da sauransu dukkaninsu kayan zaki ne ko da kuwa sun fito daga asalin halitta ko kirkirarsu aka yi wato (artificial)
Kayode yace ba zai taba dakushe gwiwar mutane ba wajen amfani da wadannan kayan zaki don abincinsu yayi kyau ko yayi dadi musamman ga yaran da suke son cin abinci , sai dai ina ba da shawarar a rika daidaitawa wajen amfani da su.
Ya kara da cewa sukari wanda ke taimakawa wajen ci gaba da girma a tsakanin yara da manya dukkanisu abune da ake samu daga abinci nau’in carbohydrates wanda shi ne glucose. Yace idan yara suka ci abinci nau’in carbohydrates yadda ya kamata da sauran nau’ikan abinci yadda za a samu abinci mai gina jiki, jikin ne ke sauya abincin nau’in carbohydrates zuwa glucose wanda ke taimakawa wajen bunkasar kwakwalwa.
Ya shawarci iyaye da su guji gabzawa yaransu abinci ko lemo mai zaki da yawa don kawai sun amince cewa sukari na taimakawa kwakwalwa ta girma, sukari da suke bukata na cikin abincin da suke ci na (carbohydrate food sources.)
Sai ya kara da cewa idan mutum ya samu karancin sukari a jikinsa (hypoglycemia) ana iya shawartarsu su kara yawan sukari da suke sha don ya koma yadda ya dace. Ya kara da cewa idan mutum na da wannan cuta yana kuma son kulawar jami’an lafiya ana iya kara masa a asibiti.
A wata tattaunawa (interview) da aka yi da shi a baya-bayan nan, Dr. Ayodele Renner, kwararren likitan yara ya bayyana cewa Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) da sauran hukumomi na lafiya sun ba da shawarar cewa yara da suke da shekaru kasa da biyu su guji shan sukari.
Ya kara da cewa idan yara suna amfani da sukari a farkon rayuwarsu wannan na iya yi masu illa kuma ya jawo lalacewar hakura da wasu cutika na dasashi..
A cewarsa idan yara suka fara amfani da abubuwa masu zaki a farkon rayuwa yana sawa su rika kin abinci mai amfani da jikinsu ke bukata, wanda kuma bashi da zaki. Idan aka hori yaro da kin abubuwa masu zaki a shekarun farko na rayuwarsa zai ba shi dama dandana abubuwa da dama.
“Domin samun lafiyar hakora da baki a kaucewa bawa yara kayan zaki. Idan aka fara ba wa yaro kayan zaki tun yana da shekaru biyu, zai fi son su, ana iya ba su horo su rika cin abubuwa da dama don samun damar banbance dandano, su kuma saba da abubuwa marasa zaki.”
Likitan ya kuma ba da shawara cewa a guji ba wa kananan yara da basu kai shekara daya ba zuma, kasancewar ana iya saamun kwayoyin bacteria a cikinta.
Yace amfani da garin dabino yafi lafiya, ya kuma ja kunne cewa a guji ba wa kananan yara ‘yanshekaru biyu sukari zalla, kasancewar wannan na iya zama sanadi na yara su zama masu teba nan gaba a rayuwarsu.
A Karshe
Sabanin abin da ake fada kananan yara basa bukatar sukari ko kayan zaki don girman kwakwalwarsu . Shi jiki na dan Adam na sarrafa nau’ikan abinci samfu rin carbohydrate su koma su zama glucose wanda ke samar da cikakken amfani ga jiki.