A duk lokacin da ake muhawara kan addini da siyasa a Najeriya wani abu da za ka yi taji shine bayyanar ra’ayoyi mabanbanta ba tare da hujja ba, irin haka ce ta faru yayin da Vivian Rora, mai amfani da shafin X ta bayyana cewa (nan) a Najeriya mabiya addinin Kirista suke da kaso “57% “ kuma yin amfani da tikitin Musulmi da Muslmi yayin takarar zabe kokari ne na Musuluntar da kasar” wannan da’awa ta yadu kamar wutar daji inda aka shiga muhawara wa ke da rinjaye a kasar.

Hoton da’awar Vivian a shafin X.
Kafar gano gaskiyar labarai ta FactCheckHub ta bayyana da’awar da zama “karya” bisa dauko misali na nuna yawan jama’a da ake amfani da shi a yayin irin wannan muhawara amma ita wannan da’awa da ta bazu , dama binciken da aka yi akanta, ya kara fito da wata tambayar, shin daga ina ne aka samu cewa wannan addini na da kaso kaza wancan na da kaso kaza ? Wa kuma ya tabbatar da cewa wannan adadin haka yake.
Bayanin yayi kokari na fito da yadda Najeriya ke kokarin fito da irin wannan bayani na fitar da kididdiga da ta shafi addini da bayanan da aka tattare me suke cewa da sanin shin bisa wace hujja aka zo da da’awar cewa Kirista na da kaso “57% “ wannan ya canci kallo na tsanaki.
Shin Najeriya na da masaniya kan adadi na Musulmai da Kiristoci da kasar ke da su?
Bayanai da Najeriya ke da su kan adadin yawan al’umma da take da su akwai rudani a ciki, ballanatana ayi maganar addini anan ne ma rudun yafi yawa.
A hukumance Najeriya bata kirga yawan Musumai da Kiristocvi da take da su ba a tsawon shekaru 62 . Lokaci na karshe da hukumar kidaya ta kasa a Najeriya ta yi tambaya kan addinin mutum a lokacin kidaya shine a 1963, wannan tambaya an cire ta a 1991 da 2006 lokacin kidayar da aka yi a shekarun. Magana ta gaskiya ma hukumar ta NPC ta nunar da cewa ba za ta duba batun ba ma’ana ta tambaya a 2023 ko da ma ace shirin kidayar na NPC ya yiwu.
A tsawon gwamman shekaru mahukunta na kokari su kaucewa tattara bayanai da suka shafi addinin saboda sanin taka tsantsan da ake bukata kan abin da ya shafi addini don gudun wata hatsaniya. Wannan ya bude kafar da wasu ke hasashe da kiyasi da zuwa da bayanai da babu cikakkun hujjoji a cikinsu.
Don haka ya zuwa 2025 ba kawai Najeriya ba tana da hakikani na yawan al’umma da ke kasar ba, a hukumance babu wasu bayanai da suka bayyana hakikanin yawan Musulmi ko Kirista a kasar ko ma masu bin addini na gargajiya a kasar.
Daga ina ne wannan adadin kiyasi ya fito?
Saboda kasancewar Najeriya a tsawon sama da shekaru 60 bata nemi bayani da ya shafi yawan mabiya addini ba, adadin da ake yadawa za a iya cewa kiyasi ne kawai saboda babu wani adadi daga bangaren gwamnati. Suna samun bayanai ne daga wasu kungiyoyi da ke kafa hujjarsu bayan daukar samfur na wasu al’umma sabanin kafatanin al’umma da za a tattara bayanansu a fitar da sakanako. Bayanansu bai nuna hakikanin adadi ba.
Misali ana kafa hujja da cibiyar bincike ta Pew Research Centre, wata cibiya a Amurka ana kafa hujja da ita kan bayanan da take fitarwa a game da yawan mutane da addinin da suke bi a Najeriya, ana kafa hujja da cibiyar cewa tace yawan Musulmi ya kai kaso 56.1 cikin dari yayin da adadin Kirista ya kai kaso 43.4 cikin dari da kuma kaso 0.6 cikin dari da ke bin wani addini na daban.
A wani bangaren kuma Kungiyar tattara bayanai da suka shafi addini ta Association of Religion Data Archives (ARDA) ta fitar da nata kiyasi cewa Musulmi na da kaso 46.3 cikin dari yayin da Kirista ke da kaso 45.8 cikin dari ,kamar yadda ake gani nan.
Haka ita ma, Statista tace kamar (anan) Najeriya na da kaso 53.5 cikin dari Musulmi haka kuma kaso 45.9 cikin dari mabiya addinin Kirista yayin da take da kaso 0.6 cikin dari na mabiya wani addinin.
Hoto daga Statista da ke ba da bayanai da ya shafi addini a Najeriya. Tushe: Statista
Wannan banbanci da ake gani na da alaka da rashin bayanai na hukumar kidaya kiyasin ya banbanta saboda dalilai da dama da suka hadar da yawan adadin mutane da aka yi bincike akansu da yanki da hanyar tattara bayanan da yawan haihuwa da batun yin kaura da yin kirdado ko kiyasi da rashin shigar da wasu gungun mutane da ma yanayi na lokacin da aka gudanar da aikin binciken ko tattara bayanan.
Idan aka kalli kuma yadda aka tattara bayanan na sake nuna akwai ma wasu karin matsalolin ga misali a Statista, sun ba da hujja da bincike da suka bawa sunan “Najeriya- littafin hujjoji na duniya ”Nigeria – The World Factbook” wanda ya fito daga cibiyar leken asiri ta (Central Intelligence Agency (CIA)) a matsayin tushen samar da bayananta.
Bayan sake nazartar bayanan mai sunan “survey,” mun gano cewa bayanan da aka tattara ba da lambobi aka kaffa hujja ba, sai dai bayanai ne da ya tattara labarin kasa a kan Najeriya da gwamnati da tattalin arziki da sauran abubuwa, wannan bayanan kuma ba a ba da bayanan hanyar da aka bi, ba da yawan mutane da aka yi aiki akansu da neman tushen bayanan nasu.
A wani binciken kuma ARDA na kafa hujja da bayanan addini daga (World Religion Database) a matsayin tushe na hujjarta, sai dai irin wadannan bayanai ba a bune da kowa zai iya gani ba, wanda yayi amfani da bayanansu ya samu ne ta hanyar wata kafa ko amfani da wasu kalmomi na sirri, kasancewar bayanan na addini da (WRD) ba abu ne da kowa zai samu ba hakan na nufi cewa ba duka danjarida zai samu wadannan bayanai ba, masu aikin binciken gano gaskiya irinsu DUBAWA su ma na diga ayar tambaya don gano hanyar da aka bi don tattara bayanan. Kuma bayanai da ake taka tsantsan irin na batu na yawan mabiya addini a Najeriya, ana ganin alamu na cewa babu fayyaceccen bayani sosai.
Hoto daga matattarar bayanai na shafin World Religion Database .
Mun kuma nazarci hanyar da PEW ta bi wajen tattara bayananta wanda sabanin Statista da ARDA, cibiyar binciken ta ce ta yi amfani da ‘hanyoyin tattara bayanai 2,700 “ a binciken da ta gudanar a duniya.
”Wadannan tushe ya hadar da: kidaya; bincike kan mutane masu yawa wanda sau tari ya haure mutane 10,000 da bincike na kafatanin al’umma wanda aka yi bincike da ke farawa daga mutane 1,000 zuwa 3,000 ; bayanai daga rijistar al’umma; bayanai da ya shafi addini da rahotanni daga gwamnati” kamar yadda ta rubuta.
Cibiyar ta yi amfani da bayanai daga kidaya na wasu kasashe, tana mayar da hankali musamman bayanan al’umma da bayanan lafiya (2013) da bayanan al’umma da bayanan lafiya (2018), da bincikem kan dabi’u na ( Pew Research Centre’s Global Attitudes Project (2024) saboda Najeriya ba ta gudanar da bincike ba a baya-bayanan nan.
Abin da aka yi tarayya akai shine tattatra bayanai na yawan al’umma da batun lafiyarsu. Wannan na duba batu ne na addini na mambobin iyali da suke cikin shekaru na baligai, sai dai kuma don gano addini na kananan yara da wadanda suka dade da balaga da sauran mambobin iyali Pew ta bayyana cewa ta yi amfani da shekaru da jinsi da yanayin hayayyafa don kiyasin na addinin wadannan mutane.
Yayin da abin da Vivian ta wallafa a shafin X ke cewa kaso 57 cikin dari na ‘yan Najeriya mabiya addinin Kirista ne za a iya cewa an zage kan lamarin, babu wasu bayanai daga bangaren gwamnatin Najeriya kan adadin al’ummar kasar da za a iya amfani da shi don kalubalantar abin da take da’awa. Saboda kasancewar Najerkiya ba ta yi wata kidaya ba da ta shafi addini a sama da shekaru 60, ace ga wani adadi na mabiya wani addini Musulinci ko mabiya addinin Kirista don duk wata da’awa a wannan layi abar yasarwa ce kiyasi ne kawai ba za a kafa hujja da su ba kamar bayanai daga bangare na gwamnati.