Site icon Dubawa

Shin sabon tsarin WhatsApp zai zama ƙofar damfara da yaɗa bayanan ƙarya?

WhatsApp Username: Could new feature aid impersonation, disinformation?

Shafin sunan da za a neme ka da shi a WhatsApp. Mallakar Hoto: TechCrunch.

,

Lokacin da kamfanin WhatsApp ya sanar da cewa nan ba da jimawa ba masu amfani da shafin za su iya yin magana da juna ta amfani da sunan da za a neme su da shi maimakon lambar waya, mutane da dama sun yi maraba da sabon tsarin saboda yadda zai ƙara kare sirrinsu.

Sai dai cikin ƙanƙanin lokaci bayan sanarwar, aka fara nuna damuwa cewa masu damfara, masu kwaikwayon mutane da masu yaɗa bayanan ƙarya za su iya amfani da wannan tsari wajen ƙirƙirar sunayen bogi, yaudarar jama’a da kuma yaɗa bayanan da ba su da tushe.

Tuni wasu fitattun mutane suka fara korafin cewa wasu sun riga sun mallaki sunaye masu kama da nasu tun kafin a fara amfani da sabon tsarin gaba ɗaya, lamarin da ya haifar da tambayoyi kan yadda kamfanin Meta zai hana amfani da tsarin ba dai dai ba.

DUBAWA ta yi nazari kan irin barazanar da sabon tsarin sunan da za a neme ka da shi na WhatsApp zai iya haifarwa wajen yaɗa bayanan ƙarya, abin da masana ke cewa, da kuma matakan kariyar da WhatsApp ta tanada.

Fargabar yaudara da yaɗa bayanan ƙarya

Sanarwar ta haifar da damuwa a tsakanin mutane a sassa daban-daban na duniya game da yiwuwar kwaikwayon wasu da damfara. Alal misali, ƙasar Indiya ta bukaci WhatsApp ya dakatar da ƙaddamar da sabon tsarin, tana mai cewa hakan na iya ƙara yawaitar damfarar yanar gizo da kutse.

Mahukuntan Indiya sun kuma bukaci WhatsApp ya bayyana dalilin da zai hana a ɗauki matakin shari’a a kansa saboda ƙaddamar da wani tsari da zai iya ƙara yawaitar laifukan yanar gizo.

A Najeriya ma, an fara bayyana fargabar cewa idan aka fara amfani da sabon tsarin gaba ɗaya, masu aikata laifuka za su iya amfani da shi wajen damfarar mutane.

Ɗaya daga cikin misalan hakan shi ne abin da fitaccen mai tasiri a kafafen sada zumunta na Hausa, Abubakar Bello, wanda aka fi sani da Abisfulani, ya wallafa a shafinsa na X.

Abisfulani ya bayyana wa mabiyansa cewa wani ya riga ya mallaki sunan da yake son amfani da shi a WhatsApp, lamarin da ya sa ya nuna fargabar cewa masu damfara za su iya amfani da sunansa wajen kwaikwayonsa ko yaudarar jama’a.

Saboda haka ya gargadi mabiyansa cewa masu damfara na iya neman kuɗi, yaɗa bayanan ƙarya ko kuma yin mu’amala da mutane suna kwaikwayonsa.

“Kada ku danna kowace mashiga (link) ko ku amsa saƙonnin da aka turo daga asusun da ke amfani da sunan da nake amfani da shi,” in ji shi.

A wani misalin kuma, fitacciyar jarumar Ghana Nadia Buari ta wallafa a shafinta na Instagram cewa mutane sun riga sun mallaki kusan dukkan nau’ikan sunanta duk da cewa har yanzu ba a fara amfani da sabon tsarin gaba ɗaya ba.

Yayin da take bayyana lamarin a matsayin abin damuwa, ta ce: “Yanzu dai a bayyane yake cewa masu damfara da masu kwaikwayo don yaudara suna ko’ina, suna jiran damar mallakar komai domin su yaudari mutane. Ku yi taka-tsantsan, domin idan har sun yi wannan cikin sauri game da sunayen wasu, ku yi tunanin abin da za su iya yi nan gaba.”

Abin da masana ke cewa

Masana sun ce babban abin damuwa ba damfara kaɗai ba ce, har ma da yiwuwar amfani da sunayen bogi wajen kwaikwayon ‘yan jarida, jami’an gwamnati, fitattun mutane, kamfanoni da kuma cibiyoyin tantance gaskiya.

Abdullah Tijani, Manajan Darakta na kamfanin PolicIQ, wani kamfani mai zaman kansa da ke Abuja mai aiki a fannin fasahar ƙirƙirarriyar basira, ya ce masu aikata laifukan yanar gizo za su iya amfani da sabon tsarin idan ba a samar da ingantattun hanyoyin tabbatar da ainihin masu sunayen ba.

“Mun ga irin wannan a shafuka irin su X, inda mutane ke ƙirƙirar shafi mai amfani da sunan wani domin damfara, yaudara ko kwaikwayonsa. Sabon tsarin WhatsApp ba zai bambanta da wannan ba,” In ji shi.

Sai dai ya bayyana cewa duk da irin waɗannan haɗurran, sabon tsarin yana da amfani sosai wajen kare sirrin masu amfani saboda ba sai sun ba baƙi lambobin wayarsu ba kafin su fara tattaunawa.

Shi ma Muhammad Auwal, wanda ya kafa kamfanin Flowdiary, wani kamfanin fasahar ilimi da ke Kano mai amfani da fasahar AI, ya ce damfarar kwaikwayon wasu da yaɗa bayanan ƙarya sun ƙaru musamman bayan da wasu shafuka irin su X suka fara ba da alamar tantance shafuka ta hanyar biyan kuɗi, wanda hakan ya bai wa shafukan bogi damar bayyana kamar na gaskiya.

Muhammad ya shawarci masu amfani da su rika tabbatar da sahihancin shafukan fitattun mutane ta hanyar duba shafukansu na hukuma ko gidajen yanar gizo da aka tabbatar.

Ya kuma gargadi mutane da kada su ba da bayanai masu muhimmanci kamar lambobin asusun banki, lambobin tantancewa, kalmomin sirri ko PIN ga duk wani mutum a WhatsApp da ke ikirarin wakiltar kamfani, wani mai tasiri ko wata hukuma.

Matakan da WhatsApp ya ce ya ɗauka

WhatsApp ya yi bayani kan koke-koken wasu da suka kasa mallakar wasu sunayen da za a neme su da su.

Kamfanin ya bayyana cewa wasu daga cikin waɗannan sunaye na iya kasancewa an riga an yi amfani da su a shafukan Instagram ko Facebook, saboda haka an tanade su ne domin masu su na hakika.

Kamfanin ya ce: “Idan kana son amfani da sunan da za a neme ka da shi iri ɗaya da na Instagram ko Facebook, dole ne ka haɗa waɗannan asusun.”

WhatsApp ya kuma bayyana cewa ya ware sunayen fitattun mutane, jami’an gwamnati, hukumomi a duniya da kuma asusun da Meta ta tabbatar da sahihancinsu domin rage kwaikwayo da damfara.

Bugu da ƙari, kamfanin ya tabbatar da cewa ya ƙara wani matakin kariya mai suna “username key”, wanda masu amfani za su iya kunnawa, ta yadda duk wanda zai fara magana da su dole ne ya san sunan da za a neme su da shi tare da maɓallin sirri kafin ya iya tuntuɓarsu.

Exit mobile version