Da’awa: Wani shafin Facebook mai suna (Nigerian Armed Forces & Military News,) yayi da’awa inda ya nuna sojojin sama na Amurka sun kaddamar da hari kan mayakan IS na yankin Afurka ta Yamma (ISWAP).

Hukunci: KARYA CE. Hoton bidiyon ya nunar da cewa dakarun hadaka ne suke samun horo a Indonesiya daga ranar 31 ga watan Agusta, 2023 zuwa 13 ga Satumba, 2023 kuma jirgin saman mai saukar ungulu da aka nuna a bidiyo na AH-64 Apache ne sabanin Black Hawk da aka yi da’awa.
Cikakken Sako
Najeriya ta shiga kanun labarai tun bayan da’awar cewa ‘ana yi wa Kirista kisan kiyashi a kasar’ dalilin da ya sanya Amurka karkashin Shugaba Donald Trump ta ayyana kasar a matsayin wacce ya kamata a sa idanu akanta, cikin barazar da ta biyo baya har da batun cewa Amurka za ta kai hari a Najeriya, lamarin da ya jawo cece-ku-ce tsakanin kasa da kasa a dangane da Najeriyar, wannan ya sanya mahukunta a yankin suka bukaci shiga tsakani na diflomasiya tsakanin kasashen biyu.
Ana tsaka da wannan ne aka ga wannnan shafin Facebook mai suna Nigerian Armed Forces & Military News ya yada wani bidiyo mai tsawon dakika 20 inda yake nuna sojojin sama na lugudan wuta ta sama. Mai yada bidiyon yayi da’awar cewa jirgin sama ne mai saukar ungulu mallakar sojan Amurka na Balck Hawk inda suke ruwan bama-bamai a kan mayakan IS da ke lardin Afurka ta Yamma ISWAP a kusa da Tafkin Chadi .
Ya zuwa ranar 17 ga watan Disamba, 2025 wannan wallafa ta samu martani sama da 10,200 akwai masu tsokaci wato (comments) 370 da wadanda suka sake yadawa (reshares) 500.
Wani mai amfani da shafin X ya yada irin wannan bidiyo a ranar 14 ga Disamba,2025 wanda ya samu martani sama da 7,400 da akwai masu tsokaci (comments) 556 da mutane sama da miliyan 1.8 da suka kalli wannan bidiyo.
Mun kuma lura cewa akwai sama mutane 1,900 da suka nuna alama ta cewa za su sake kallon bidiyon a gaba, sananan akwai sama da mutane 1400 wadanda suka kalla suka sake yada bidiyon.
Yanayi na tsokacin mutane ya nuna cewa an samu mabanbantan ra’ayoyi ciki kuwa har da wadanda suka nuna cewa basu amince da abin da suka gani ba.
Oyon Chineme yace, “ Zan iya amincewa da abin da na gani ne kawai saboda shafin da ya fitar da wallafar, ina da wahalar bude shafin shafukan sada zumunta don ganin labarai.”
Mohammed Murtala yace “aiki na kyau Allah Ya albarkaci dakarun sojan Najeriya Ya basu kariya.”
Solomon Olofu yace, “Wannan jirgin shi ake kira Apache mallakar sojan saman Amurka.”
Divine Nwaeze tace, “Wannan atisaye ne na dakarun soja, ba na sojan Amurka ba, Sojan Amurka na amfani da jirgin saman mai saukar ungulu da ake kira Black Hawk ba da jirgin Apache.
Moses Tamara-Ekpezude yace, “Ban ga wani dan ta’adda da aka harba ba, ina ga suna asarar harsashi ne kawai a yayin atisaye.”
Ganin mabanbantan martani dama yanayi na matsalar tsaro da ake fama da ita a kasa shirin na DUBAWA ya ga dacewar gudanar da bincike.
Tantancewa
Wannnan bidiyo ya nuna cewa an gudanar da harin ne a wajen da ke zama daji ne wanda ke dauke da tarin duwatsu, da muka nazarci bidiyon sai muka lura wannan bidiyo da yadu an hada shine daga wasu bidiyo guda biyu.
”Mun bibiyi bidiyon da aka samu a shafin YouTube daga kamfanin dillancin labarai na Associated Press (AP) a ranar 16 ga watan Satumba,2023, wannan bidiyon da ke da tsawon mintuna 2 da dakika 59 an ba shi take na “ Sojojin Indonesiya da Amurka da Ostareliya da wasu kasashe na gudanar da atisaye a wani yanki na Java.”
Hoton bidiyon. Tushe: Associated Press (AP)
A takaice DUBAWA ya lura da cewa wannan jirgin ba na Balck Hawk ba ne kamar yadda ake ikirari, amma ta hanyar kallon bidiyon kawai ya nunar da cewa jirgin samfurin Boeing AH-64 Apache ne.
Boeing AH-64 Apache. Wanda ya dauki hoton: EDR Magazine.
Karin bincike da aka gudanar ya nunar da cewa wannan nau’in atisaye an kira shi da sunan Super Garuda wanda ke zama na hadakar sojoji ne na kasa da kasa da aka yi a Gabshin Java daga ranar 31 ga Agusta zuwa 13 ga Satumba, 2025.
A takaice akwai kimanin sojoji 5000 da suka shiga wannan atisaye daga kasashe daban-daban na duniya da suka hadar da na Amurka da Indonesiya da Ostareliya.
A wannan atisaye ya hadar da atisaye na harba bindiga kai tsaye (CALFEX), da nuna manyan kayan aiki irin na tankokin yaki na M1A1 Abram da jiragen na AH-64 Apache da aka gani wanda ya saba da jiragen Black Hawk da aka ce sune a da’awar.
Black Hawk. Tushe: Forbes
A hoton mun lura cewa AH-64 Apache yana tsaye ne ana kallonsa karara, a zahiri idan a irin wannan yanayi na “zafi” na wajen da ke zama kewayen Tafkin Chadi inda mayakan na ISWAP ke gudanar da ayyukansu wannan na iya zama abu mai hadarin gaske.
A fagen aikin sojan sama matukin jirgin na bin kaidoji “na dadabarun kaucewa hari da tseratar da rayuwa”don gudun kada a harbo jirginsa ta hanyar amfani da dabarun soja na kakkabo jirgi da tsarin da ake kira (MANPADS) ko amfani da makaman roka (RPGs), Matukan jirgin na kai hari ne a yanayi a lokacin da kuma jirginsu ke tafiya a guje, tsayawar jirgi a waje guda na zama abin da za a iya kakkabo shi, duk sakacin da ke iya jawo baro jirgi ba za a so shi ba a wannan yanayi na yaki da mayakan sari ka noke.
Har ila yau shi wannan samfurin jirgi na AH-64 Apache an tsara shi ne yadda yana bayyana ne cikin dakikoki ya kai hari ya bace, don haka ganin yadda aka ga jirgin na tsaye a bidiyon ya nuna cewa a tsari ne na atisaye da ake harba bindiga kai tsaye da ake kira (LFX).
Yanayin kuma ya nuna cewa ba a musayar wuta da abokan gaba don haka yanayi ne na atisaye da aka yi na Super Garuda Shield a 2023, ba yanayi ne na fagen yaki ba a filin daga.
A Karshe
Wannan yanayi da aka gani yanayi ne na atisayen sojoji da aka yi a Indonesiya a 2023 ba fagen yaki ba ne da mayakan ISWAP a yankin Tafkin Chadi.Kuma yanayin jirgin da aka gani samfurin AH-64 Apache,ba wai Black Hawk ba, don haka wannan da’awar karya ce.