Cikakken Sako
A ranar biyar ga watan Agusta, 2024 wani mai amfdani da shafin X mai suna The_Bearded_ yayi bayani kan cuta da sauro ke yadata, “ELEPHANTIASIS” Cutar Dundumin Kafa ko Cutar Goshi. Wannan wallafa ta samu mutane sama da dubu dari biyu da suka kalla (208.6K) da masu tsokaci 15 da wadanda suka sake wallafawa 551. Ya zuwa lokacin da aka hada wannan rahoto.
Wannan wallafa ta samu martini na mutane da dama da tsokaci na mutane da dama wasu na nuna sun yi mamaki wasu kuma na ganin abun a matsayin mataki na samun wayewar ilimi. Wani mai amfani da shafin mai suna Iampelumi (@Itzpelumi), yayi tsokaci yana mai cewa “Abin da sauro ba zai yi ba, ba a halicce shi ba.”
Wani kuma mai amfani da shafin mai suna Timeless Empyrean (@ricyofficial @SageOrhis), ya bayyana mamakinsa (expressed) da cewa “Abin mamaki na ga irin wannan cuta wasu lokuta, ban san cewa sauro ne ke zama sanadi ba.”
Wata ma mai amfani da shafin Duchess_Beeyah (@KhadijaGarba19) ta mayar da martani (reacted) da cewa “Dama ba cutar malaria kadai ke zama gare mu ba daga sauro? Ya kamata na mayar da hankali wajen kwana a cikin gidan sauro don kaucewa wannan cuta,” Shi kuma BolaTITO (@mirab_clothiers) yayi nasa martani (responded) da cewa Aaa tayaya sauro kuma?”
Ganin yadda ake da tarin tambayoyi da rudani game da wannan wallafa DUBAWA ta ga dacewar neman karin bayani game da wannan cuta .
Menene ma’anar cutar Dundumin Kafa?
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya World Health Organization (WHO) wannan cuta ta elephantiasis, ko Dundumin Kafa an kasafta ta cikin ajin cutika da ba a mayar da hankali a kansu ba na yankuna masu bishiyu da koramai da ake kira Neglected Tropical Disease (NTD) a Turance. Cutar Dundumin Kafa ana samunta ne dalilin wasu tsutsotsi da ake kira nematodes, ko roundworms, da suka fito daga nau’in iyalan tsotsotsin Filariodidea family. Akwai tsutsotsin masu kama da zare kashi-kashi uku.
- Wuchereria Bancrofti wacce ke zama sanadi na cutar da kaso 90 cikin dari.
- Brugia Malayi ita ke zama sanadi na sauran cutikan.
- Brugia timori, ita ma kan yi sanadi na cutar.
Shin cutar Dundumin Kafa Sananniya ce?
A cewar asibitin Cleveland Clinic, Cutar Dundumin wacce kuma ake kiranta da lymphatic filariasis a Turance, na iya shafar kusan mutane miliyan 120 a fadin duniya,wato kaso daya da rabi cikin dari na al’ummar duniya.
Wannan cuta sananniya ce a yankin da ke da koramai da bishiyu da ake kira Tropical region, cutar da ke zama sananniya kamar a yankin Asia da Afurka da Amurka ta Kudu. Bayanai da aka tattara daga WHO ya nuna cewa mutane miliyan 882 a kasashe 44 na fuskantar barazanar cutar, suna kuma bukatar daukar mataki na kariya daga kamuwa daga wannan cuta da kwayoyin tsutsa ke haifar da ita.
A cewar kididigar da Sightsavers ta yi Najeriya na da kalubalen wannan cuta da ake samu a wannan yanki na (NTDs).
A bisa kiyasi ana iya cewa kaso daya bisa hudu na wadanda wannan cuta ke kamawa a yankin na NTDs suna zaune ne a Najeriya. A bisa kiyasi kimanin mutane miliyan (100 million) ‘yan Najeriya na fuskantar barazanar kamauwa da daya daga cikin wadannan cutika yayin da wasu miliyoyi ke dauke da sama da guda daga cikin cutikan.
Dundumin Kafa abu ne da ke wahalar gani a Amurka ta Arewa kasancewar tsutsar da ke haddasa wannan cuta ba a samunta a Amurka. Ba abu ne mai sauki ba idan mutum ya ziyarci wata kasa da ke da cutar cikin karamin lokaci ya kamu da cutar ba, amma idan mutum zai dauki lokaci kamar watanni masu yawa ko shekaru yana iya kamuwa da cutar.
Wace irin alaka ke akwai tsakanin cutar Dundumin Kafa da Sauro?
A cewar WebMD, sauro ba kawai matsalarsa haifar da maleriya ba; yana kuma iya haifar da cutar Dundumin Kafa. Yana kuma samuwa idan aka harbu da tsutsar da kan haifar da cutar. A lokuta da dama ana harbuwa da kwayoyin cutar tun daga yarinta sannu a hankali yaro yana girma cutar na samun maboya ta illata wani bangare na jikin dan Adam.
Cutar Dundumin na yaduwa idan sauro ya ciji mutum sai ya ajiye kwayar cutar a jikin mutum, kwayar da ya ajiye ita za ta ci gaba da girma har ta zama babbar tsutsar, wannan shine sannu a hankali ke iya sawa kafa ta rika girma ya sauya mata halitta. Abun da ya kamata a lura shine wasu da suka harbu da kwayoyin cutar ba sa nuna wata alama.
Ra’ayin Kwararru
Mataimakain manaja kan shirin wadannan cutika na yankin Tropics da ake watsi da su (NTDs), Mista Jacob Ilemobayo, ya bayyana rashin fahimta da ake wa cutar ta Dundumin Kafa inda ya jaddada cewa akwai bukatar a fadakar da jama’a su fahimta.
“Muna bayyana wasu cutika a matsayin wadanda aka yi watsi da su kuma cutar Dundumin Kafa na daga cikinsu,”a cewar Mista Ilemobayo
“Muna kiransu da wadanda aka yi watsi da su saboda yadda mutane suka yi wasarairai, da dama daga cikin al’ummarnu sun yi amanna cewa ba cutika ne da ke kama mutum daga Allah ba sai dalilin maita wanda kuma jahilci ne ke kawo haka.”
Mista Ilemobayo ya sake fayyace bayani da cewa Dundumin Kafa wata tsutsa ke kawo ta wacce ake kira Wuchereria Bancrofti, sabanin sauro. “Ba sauro ke haifar da cutar Dundumin Kafa ba”. Sauro na daukar cutane daga wanda ke da ita ya kaiwa wanda bai da ita a cewarsa. Idan sauro ya ciji mai cutar yana daukar kwayoyin cutar ya kaiwa wani mutumin abin da ke haifar da cutar kenan.”
Ya kara da cewa kwayoyin cutar na zama a cikin jini. Don haka idan ana so a gano jinin da ke dauke da cutar ana daukar samfurin jinin ne sai a kai dakin gwaji a gudanar da bincike,” a cewarsa.
Da yake karin bayani kan yadda cutar ke bazuwa Mista Ilemobayo ya fayyace cewa kwayar cutar ba ta bazuwa ta hanyar abinci da ruwa ko wata hanyar, “Ita kwayar halittar da kan haddasa wannan cuta tana bazuwa ne sanadin cizon sauro na mai dauke da cutar yana daukar kwayar cutar a cikin jini sai ya zuba wa wani lokacin da ya cije shi.
Farfesa Tanimola Akande, masanin kiwon lafiya a jami’ar birnin Ilorin ya jaddada cewa “hanyar da ake bi wajen kare kai daga wannan cuta ya hadar da amfani da magunguna da ke kashe halittar kwayar cutar. Wannan magani na tasiri ya kashe tsutsar da kwanta da kananan cutakan da ke tare da ita, ana kuma amfani da su a matakin kandagarki ko kariya a kasashe da wannan cuta ta zama annoba ta yadu tsakanin al’umma.”
Yace yadda cutar ke girma wanda kan jawo girman kafafu da sassauya halittarsu “Abu ne mai muhimmanci al’umma su sani cewa yayin da ake gani a zahiri yadda cutar ke bayyana a wasu lokutan ko alamu ba a gani.” A cewar Farfesa Akande.
Farfesan ya ja hankali kan muhimmancin zuwa gwaji a gano cutar da wuri don daukar matakan kariya don kada cutar ta girmama ta zama babbar barazana ta lafiya.
Ya kara da cewa cutar na sassauya halittar dan Adam ta jawo wa mutum kyama da rashin samun abincin mai gina jiki da matsalar da kan shafi kwakwalwa wanda kan jawo tarin matsaloli da na zamantakewa da tattalin arziki da jin nauyi na daukar wahalhalun masu dauke da cutar.
A Karshe
Yadda wannan cuta ta Dundumin Kafa ke samuwa na da alaka da cizon sauro wanda ke sanya kwayar halittar cutar a jikin dan Adam, ba cuta ce da za a ce ‘Mayu’ ke sawa mutane ba, kamar yadda a wasu al’adu aka aminta da haka.
Wannan bincike an yi shine karkashin shirin gano gaskiya na DUBAWA 2024 bisa lamuncewa ta shirin kwararru na Kwame Karikari da hadin gwiwar Crest 91.1FM, Ibadan, da News Verifier Africa, don dabbakawa da tabbatar da “Gaskiya” a aikin jarida da bunkasa ilimin aikin jarida a fadin kasa.