Site icon Dubawa

Tsohon bidiyo ‘yan ta’adda suka yi amfani da shi don sanya fargaba a zukatan al’umma

Old video of bandits used to incite fear

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X @MR__Sulaiman1 ya yada wani bidiyo wanda ya nuna yadda ‘yanta’adda ke halaka mutane su bar wani ya ba da labari don sanya fargaba a zukatan ‘yan Najeriya.

Tsohon bidiyo ‘yan ta’adda suka yi amfani da shi don sanya fargaba a zukatan al’umma

Hukunci: Yaudara ce. Bincike da DUBAWA ta gudanar ta gano cewa bidiyon da ake nunawa ba sabo ba ne, yana nan a shafin intanet tun a watan Janairu,2025.

Cikakken Labarin 

Ganin yadda ake ci gaba da samun karuwar masu garkuwa da mutane dama sakin bidiyo na mutanen da suke garkuwa da su a kokarinsu na karbar kudaden fansa, wannan yanayi ya kara haifar da fargaba a tsakanin ‘yan Najeriya.

Ana tsaka da wannan sai wani mai amfani da shafin X @MR__Sulaiman1, ya yada wani bidiyo kamar yadda aka ajiye shi (nan) bisa da’awar cewa wasu ‘yanta’addar sun kama wasu inda suka umarce su da su fadawa ‘yan Najeriya cewa sun kashe daya daga cikinsu kuma a shirye suke su kashe dukkansu muddin ba a biya kudin fansa ba a kan lokaci. 

An yada wannan bidiyo a ranar 9 ga watan Yuni,2026 an nuna wasu mutane biyu jikinsu na bari aka umarce su su tabbatar da cewa ko abokinsu ya mutu bayan da aka kashe shi a gabansu.

Ga bin da aka rubuta a game da bidiyon, “ Ga wani bidiyo da ‘yanta’adda suka saki, za a ga yadda aka umarci wadanda aka kama su yi magana da kamera a kansu, ‘yanta’addar sun bukaci mutanen da aka kama su fada wa ‘yan Najeriya cewa su biya kudin fansa ko kuma su ma za a kashe su.Kuma idan ma ba a biya kudin fansa a kan lokaci ba suma da suka yi saura zaa kashe su.” 

A wannan bidiyo ya nuna matasan guda biyu wadanda aka nuna masu cewa suma za su mutu kamar abokinsu, wannan ya kara haifar da fargaba da rashin kwarin gwiwa a wajen wadanda aka kama din.

Ya zuwa ranar 12 ga watan Yuni,2026 wannan bidiyo ya samu mutane masu tarin yawa da suka kalla 44,900 da masu nuna sha’awa 271 da wadanda suka sake yadawa 175 ga kuma masu martani mabanbanta.Yayin da wasu daga ciki ke ganin abin da aka fada haka ne wasu kuma na ganin wannan bidiyo ma tsoho ne. 

Wani mai amfani da shafin na X, Akaaza (@akaazaayila), ya rubuta cewa , “Ku wadannan dabbobin mutane ne. Wannan abin ya faru shekaru da suka gabata.”

Wani mai amfani da shafin ÓMÒÉLÉRÍNJÁRÉ (@omoelerinjare), ya mayar da nasa martani da cewa “abin takaici da tada hankali.”

DUBAWA ta kuma gano irin wannan bidiyo wanda yafi tsayi, wanda ya nuna yadda aka ce an halaka mutumin.

Ganin yadda wannan bidiyo ya yadu da ma fargabar da ke akwai a Arewa maso Yammacin Najeriya, mun ga dacewar gudanar da bincike akai.

Tantancewa 

Mun nazarci bidiyon muka ga ‘yanta’addar suna magana da Hausa abin da ya tabbatar da abin da mai da’awar yace sun fadi, sai dai wannan bidiyo bashi da wata alama ta lokaci ko na ranar da aka dauka abin da zai nuna cewa ko akwanannan aka yi shi.

DUBAWA ta tsakuro wasu daga cikin bangarori na bidiyon don sake nazarinsu a gano asalin inda suka fito, sai kawai bincike ya kai ga ganin wannan bidiyo da aka sa a shafin Facebook a ranar 5 ga watan Janairu,2025. Wannan bincike har ila yau ya kaimu ga wata wallafa a ranar 4 ga Janairu,2025 wanda ya nuna wuraren da ke cikin bidiyon. 

Domin dai ganin ko da’awar sabuwa ce, DUBAWA ta kuma lalubawa ko za a ga wata kafar yada labarai sahihiya ko kafar jami’an tsaro da ta tabbatar da hakan. Babu wani rahoto da ya fita a 2026 da 2025 da ya tabbatar da asalin bidiyon.

A karshe

Da’awar yaudara ce! Bincikenmu ya nuna cewa bidiyon ba sabo ba ne. Wannan bidiyo ya taba bayyana tun a watan Janairu,2025.

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.  

Exit mobile version