Da’awa: Wani mai amfani da shafin X, AKSMILE911, ya yada wani bidiyo inda yayi da’awar cewa dakarun sojan Najeriya sun yi wata taho mu gama da musayar wuta da wasu ‘yan bindiga.

Hukunci: Karya ce, bidiyon da aka yada bashi da wata alaka da bata-kashi da sojojin Najeriya a baya-bayan nan. Wani akin atisaye ne na soja wanda a baya ma an yada shi tare da ba da labarai kala-kala a kansa.
Cikakken Labarin
A ranar 6 ga watan Yuni,2026,wani mai amfani da shafin X mai suna AKSMILE911, ya yi zargi cewa dakarun sojan Najeriya sun yi taho mu gama da ‘yanbindiga kamar yadda yake a (nan), inda aka hada da bidiyo da ke nuna yadda sojan Najeriya suke fafatawa.
” Ga abin da taken labarin ke cewa “ Yanzu-yanzu: Sojoji sun shiga fatatawa da wasu ‘yanbindiga, babu dai labarin takamaimai a ina ne ake fafatawar, sai dai akwai fargaba mai yawa da ke karuwa.”
Wannan wallafa ta samu wadanda suka kalla 35,000 (views) da wadanda suka nuna sha’awarsu 110 (likes) da masu tsokaci 53 (comments) da wadanda suka sake yadawa a Twitter 24(retweets).
Wani mai amfani da shafin Adrenalinej004, wanda ya aminta da da’awar ya rubuta cewa “Kowace rana a Najeriya kamar wasan kwaikwayo kashi-kashi a idanuna.”
Wani mai amfani da shafin, @yourwriterpro, yace, “kullum jijjiga kai nake kan yadda labaran Najeriya ke zagayawa abin da ke faruwa a kullum.”
Ganin halin da ake ciki a Najeriya dangane da batun tsaro da kokari na dakile irin wadannan bayanai , mun ga dacewar gudanar da bincike kan wannan da’awa.
Tantancewa
Ganin cewa wannan wallafa bata ba da bayanai da za a iya tantancewa ba a dangane da wannan batu mun yi amfani da muhimman kalmomi don gano labari mai kama dahaka, haka nan shima bidiyon an tantance shi.
A binciken babu wata kafar yada labarai sahihiya da ta ba da rahoto cewa sojojin Najeriya sun yi gaba da gaba da ‘yanbindigar a lokacin da aka wallafa labarin.
Babu wani bayani da ya fito daga dakarun sojan na Najeriya da ya tabbatar da labarin hakan.
Da aka zurfafa bincike an ga wannan bidiyo da aka sanya a shafin Youtube daga Voice TV Nigeria, wata kafar yada labarai a Najeriya.
Bidiyon da aka wallafa a ranar 22 ga Mayu,2023 karon farko an masa taken “Dakarun sojan Najeriya na atisayen harba bindiga babu kakkautawa.”
Asalin bidiyon na makon horon sojoji ne da aka yi a Bauchi shekarar 2023.Wanda ya nuna horon aikin soja mai zafi da harba bindiga ba kakkautawa da aka yi a Bauchi, abin da ke nuna sabbin dabaru na tunkarar abokan gaba, horon soja ne ba fafatawa da abokan gaba ba kamar yadda aka nuna a wallafar ba.
Kafar yada labarai ta Defence News Nigeria ta yada bidiyo a shafin X. Taken labarin da aka yada a ranar 23 ga watan Mayu,2023 ya nuna cewa “Atisayen harba bindiga a zahiri mai kayatarwa.” Wannan taken labari ya ci karo da da’awar bidiyon wacce a bayan nan tace taho mu gama aka yi tsakanin soja da ‘yanbindiga.
Karshe
Da’awar cewa dakarun sojan Najeriya sun yi taho mu gama a fafatawa da ‘yanbindiga karya ce. Bidiyon da aka wallafa na sojojin Najeriya ne a lokacin da suke atisaye a Bauchi a 2023 a makon sojoji.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.