A ranar 2 ga watan Mayu,2026 wani jirgin ruwan daukar fasinja dauke da mutane 147 da masu aikin jirgin sun samu matsalar rashin lafiya da ta shafi numfashi a cikin jirgin.
Ya zuwa ranar 4 ga watan na Mayu, Hukumar Lafiya ta Duniya World Health Organisation (WHO) tace gwajin da aka yi a dakin binciken lafiya ya nunar da cewa mutane biyu an tabbatar da cewa suna dauke da cutar ta Hanta virus yayin da wasu uku kuma ake zaton suna dauke da cutar.
Wannan ya hadar da mutane uku da suka rasu sanadin cutar da wani mutum guda da ke cikin yanayi na matsanancin rashin lafiya yayin da wasu mutane uku suka nuna alamu na cewa suna dauke da cutar.
Hakanan, akwai bukatar a ci gaba da wayar da kan mutane game da illolin da hanta virus ke haifarwa a jikin dan Adam.
Duk da cewa hukumar ta WHO a nazarinta bata nuna girman barazanar cutar ga duniya ba, fahimtar yadda kwayoyin cutar ke aiki da yadda ake yada ta da sanin dalilin da ya ake ganin muhimmancin sannin illarta na da muhimmanci.
Wace cuta ce Hantavirus?
Hukumar ta WHO ta bayyana cutar da zama cuta wacce ke bazuwa a cikin dabbobi, daga dangin beraye wani lokacin ta bazu cikin al’umma tana jawo ciwo mai tsanani, a wasu lokutan ma har ta kan jawo sanadi na rasa rayuka, cutar ta kan banbanta, dama wuraren da ake samunta.
Kwayoyin cutar ta Hantavirus sun fito ne daga dangin Hantaviridae, daga ajin Bunyavirales. Kowace cutar ta hantavirus na da alaka da wani nau’i na dangin beraye, wacce idan ta harbu mutum tana jawo tsawon lokaci na kamuwa da kwayar cutar ba tare da ta nuna wata alama ta rashin lafiya ba.
Duk da cewa akwai nau’ikan cutar ta Hantavirus da dama a fadin duniya amma wasu kadan ne ke jawo cutuka a cikin al’umma.
Yaduwar cutar
Ana samun yaduwar wannan cuta ta hantavirus a cikin al’umma lokacin da aka samu mutane sun yi cudanya ta hanyar taba fitsari ko yahu na beran da ya harbu da kwayoyin cutar, ana kuma iya samun harbuwa da kwayoyin cutar ko da yake ba ko da yaushe ba ta hanyar cizon bera, hanyoyin da ake iya cudanya da beran ya hadar da goge wurin da babu gudanarwar iska da aikin gona da aikin gandun daji da kwana a wajen da ke da tarin beraye na bude hanyar barazanar kamuwa da cutar.
Har zuwa wannan lokaci yadda ake samun cutar na bazuwa daga mutum zuwa mutum an samu ne kawai a Andes virus a Amurka, wanda bai zama sananan abu ne.Idan kuma an samu a mutum samar da cutar daga mutum zuwa mutum na faruwa ne a tsakanin iyalai da suka dade suna tare ko wadanda ke da kusanci na auratayya , Ana gano cutar a lokaci na farko na rashin lafiyar inda anan ne ake yawan yada cutar.
Alamun cutar
A cikin mutane alamun cutar na farawa ne daga mako na farko zuwa na takwas bayan haduwa da beran ko abin da ke alaka daga shi, ya danganta daga irin kwayar cutar, kuma mutum na iya samun zazzabi da ciwon kai da ciwon gabobi da ciwon ciki da tashin zuciya ko amai ko kumallo.
Gwaji
Abu na farko a gwajin hantavirus na iya zama da kalubale kasancewar akwai kamanceceniya da wasu cutuka da sukan shafi numfashi kamar mura da cutar Covid-19 da cutar sanyi da zanzabin dange, don haka sanin tarihi na cutukun mara lafiyar na da muhimmanci, musamman wajen mayar da hankali wajen ganin ko yana haduwa da beraye da barazana a wajen aiki ko muhalli da tarin tafiye-tafiye da jin labarin ko ya taba haduwa da masu cutar ko an taba samun wanda ya kamu da cutar ta hantavirus a yankin.
Yadda ake tabbatar da cutar ta hanyar gwaji ya hadar da yin gwajin da ake kira serological don gano alamomi na kwayoyin cutar ta hanyar gwajin (IgM antibodies ko IgG titres), ko wata hanyar gwajin da masanan ke kira (RT-PCR) a lokacin farko-farko na cutar a lokacin da ake gano kwayar RNA a cikin jini.
Samfur na kwayar na da hadari sosai, abin da ya sanya ake bukatar taka tsantsan sosai musamman idan za a dauki kwayar cutar daga wani waje zuwa wani, jigilar a cikin kasa ne ko kuwa a tsakanin kasa da kasa.
Magani
Babu wani maganin wannan cuta da ke da lasisi ko wata allura ta rigakafin wannan cuta ta hantavirus, ana mayar da hankali ne kan kula da yadda mara lafiyar ke numfashi da lura da bugun zuciyarsa da wasu sarkakiya da ke da alaka da koda. Ba da kulawa ga mara lafiya cikakkiya tun da fari na taimakawa a samu sakamako mai kyau, musamman idan aka lura alamun cutar ta fito ne daga ajin hantavirus da ke sarke numfashi ya gagara sai da taimakon masana.
Rigakafi da Kariya
Kare kai daga Hantavirus ya dogara ne da daukar matakai na kare kai daga haduwa da beraye ko muhallin da ya baci da su.Masana a harkar lafiya na ba da shawara a rika zama a gidaje masu tsafta da rufe duk wasu ramuka da beraye kan iya shiga su samu mafaka da rufe kayan abinci ta yadda dabbobin ba za su iya shiga ba.
Idan za a tsaftace wurin da ake ganin akwai kwayar wannan cuta ta dalilin fitsarin berayen ko kashinsu, ana ba wa al’umma shawara cewa su guji yin shara ko amfani da na’urar zuke kura, kasancewar ana iya yada kwayoyin cutar a cikin iska, don haka ake ba da shawarar cewa a jika wajen da ruwa kafin fara tsafacewa kasancewar hakan zai hana tashin kwayoyin da za a iya shaka da ke zama masu hadari.
Ana kuma ba wa al’umma shawara cewa su rika yawan wanke hannu a matsayin hanyar kariya mai muhimmanci.
Duk lokacin da aka saamu labarin bullar hantavirus mahukunta a fannin lafiya na ba da shawarar cewa wanda aka ga alamun cutar a tattare da shi a gaggauta kebe shi. Sanya idanu kan mutanen da suka yi mu’amala da mai dauke da cutar zai taimaka wa jami’an lafiya su gaggauta kai dauki idan aka samu sabon kamuwa da cutar.
A tsarin zamantakewa da ke tafe da kula da lafiya, daukar matakai na kariya na taimakawa wajen dakile bazuwar cuta a kare al’umma daga kamuwa da cutar.
Kare kai daga kamuwa da daukar mataki
Shedu sun nunar da cewa barazanar bazuwar cutar ta hantavirus da hadarin da ke tattare da yada cutar ta hantavirus ciki kuwa har da nau’in cutar na Andes bashi da yawa, idan har an dauki matakan da suka dace.
A muhallin kula da lafiya ana daukar hanyoyin kariyar kwararru ga duk marasa lafiyar, ciki kuwa har da wanke hannu da tsafatar muhalli da yin taka tsan-tsan idan za a dauki jini da sauran wani abu da ya shafi ruwa-ruwa daga cikin masu dauke da cutar.
Idan ana tsammanin ko an tabbatar da cewa an harbu da kwayar cutar ta hantavirus a dauki matakan kariya cikakku da kula da marasa lafiya yayin da ake kula da lafiyarsu, idan ana aikin da zai tada kura a kula sosai kada a tada kurar, idan an gano mutum na dauke da cutar a gagauta kebe shi a bi ka’idoji na jami’an lafiya suke bayarwa a irin wannan yanayi.
Bambanci da ke tsakanin Hantavirus da Zazzabin Lassa
Duk da cewa Hantavirus Pulmonary Syndrome da zazzabin Lassa dukkaninsu beraye ne ke baza su wadanda kan haifar da cuta mai tsanani ga mutane, akwai alamunsu da yadda suke yaduwa ga bangarorin jiki da suke shafa.
Hantavirus na shafar hunhu ta jawo wahalar yin numfashi da cutar pneumonia ko sanyi ita ko cutar Zazzabin Lassa na shafar bangarorin jiki da dama ne a lokuta da dama su rika fitar da jini idan lamarin yayi tsamari.
Hantavirus da wahala aga tana yaduwa daga mutum zuwa mutum, ita kuwa Lassa ana yada ta nan da nan ta hanyar haduwar ruwa-ruwa na jiki musamman a asibiti da wajen kula da lafiya.
Wani banbanci kuma shine Lassa an fi saninta a Afurka ta Yamma a kasashe kamar Najeriya inda take bulla daga lokaci zuwa lokaci, ita kuwa Hantavirus ba a cika samunta ba sai dai ana samunta a yankuna da dama na duniya ya danganta da beran da aka samu.
Dukkanin cutukan guda biyu ana samunsu ta hanyar alaka da fitsarin beraye da yawunsu da kashinsu, kula da tsafta da daukar matakan kare kai daga beraye sune ginshikai.
A Karshe
Duk da cewa bazuwar cuta a mataki na duniya za a iya cewa kadan ne yanzu, amma samun labarin bullar cutar za ta sanya a dauki matakan kariya da rigakafi a kuma wayar da kan al’umma kan wannan cuta da ke yaduwa ta hanyar beraye.