A watan Fabrairu, 2026 an shiga yanayi na yaki tsakanin Iran da Amurka inda sojojin Amurka suka afkawa Iran bisa zargin cewa tana kokarin mallakar makaman nukiliya.
Iran dai ta rasa ran al’ummarta 3009 bayan wannan rikici ya barke kafin a tsagaita wuta a ranar 8 ga Afrilu,2026 inda aka tsagaita tsawon makonni biyu, cikin wadanda aka rasa har da jagoran addinin na Iran Ayatollah Ali Khamenei, da Aziz Nasirzadeh, ministan tsaro na kasar da
Abdolrahim Mousavi, shugaban sojojin kasar.
Da dama ”yan Najeriya sun ji a jika ta fuskar tattalin arziki, inda suka sheda rufe mashigar Hormuz abin da ya shafi harkar samar da makamashi a duniya.
Dagawar farashin mai da tsadar sufuri ya sanya aljihun kowa ya koka a Najeriya.
Wannan yaki babbar barazana ne ganin cewa batu ne na rikici kan abin da ya shafi duniya ma’ana magana kan makamin nukiliya.
Amurka da Isra’ila a bangare guda suna ikirarin cewa Iran na kokarin mallakar makamin nukiliya yayin da a bangare guda ita Iran na ganin afka mata a matsayin take hakkinta a matsayinta na kasa mai cin gashin kanta, harin kuma da ya sabawa dokar kasa da kasa.
Rikicin dai barazana ne ga duniya kan batun na makamin nukiliya yayin da ake fafutukar ganin an dabbaka yarjejeniyar ta zaman lafiya da hana yaduwar makamin nukiliya (NPT).
DUBAWA, a cikin wannan bayani ta duba wannan yarjejeniya da aka rattaba hannu a kanta gwamnan shekaru wacce ta zama abar dogaro kan batun rayuwa da mutuwa a hannun shugabanni na wannan zamani.
Waye ya halatta ya mallaki makaman nukiliya?
Yarjejeniyar hana bazuwar makamai ta (NPT), da aka aminta da ita a shekarar 1968 aka fara aiki da ita a 1970, an kafata bayan yakin cacar baka don hana bazuwar makamai masu hadarin gaske.
Karkashin wannan yarjejeniya duniya ta rabu gida biyu,: Kasashen masu makamin nukiliya (NWS) da kasashen da basu da makamin nukiliya (NNWS).
Kasashe irinsu Amurka da Rasha da China da Faransa da Burtaniya tuni dama sun yi gwajin makamin na nukiliya kafin shekarar ta 1967, wannan ya sanya suka zama kasashen da aka aminta cewa su ke da makamin na nukiliya a lokacin da sauran kasashen suka amince ba za su hada makamin ba sai dai kawai Isra’ila da Pakistan da Indiya.
Ganin cewa wadannan Kasashe sun aminta ba za su mallaki makamin na nukiliya ba sai aka amince masu su yi amfani da fasahar ta nukiliya don zaman lafiya wajen samar da makamashi da binciken lafiya inda su ma za su gudanar da ayyukansu karkashin kulawar kasa da kasa don tabbatar da ganin suna bin sharudan da aka gindaya masu.
Wannan yarjejeniya kamata yayi ta yi tafiya da fuska biyu, yayin da aka hana wasu kasashe su mallaki makamin nukiliya, kamata yayi kuma a ce kasashen da suke da makamin su wargaza shirinsa sannu a hankali.
Wannan yarjejeniya ta taimaka wajen dakile kasashe su mallaki makamin na nukiliya a fadin duniya sai dai kuma sannu a hankali an samu Baraka.
Koriya ta Arewa ya janye daga yarjejeniyar a shekarar 2003 ta yi gaban kanta wajen ganin ta mallaki makamin na nukiliya
Yayin da kasashe uku wadanda suka janye hannu a yarjejeniyar suka ci nasara wajen hada makamin na nukiliya mallakarsu.
Wannan ta sanya aka rika aza ayar tambaya cewa idan wasu kasashe aka bar su suka mallaki wannan makami wajen wannan yarjejeniya , to me yasa Amurka ta sa idanu sosai kan kasar ta Iran ita kadai?
Rikici da aka gina a gwamnan shekaru
Rikici tsakanin Iran da Amurka, tsohon abu ne wanda ke zama na tarihi mai cike da sarkakiya.
Alakar ta sake lalacewa bayan 1979 a lokacin juyin juya hali na Iran wanda ya kawo karshen gwamnatin Iran da ke samun goyon bayan Amurka, tun daga wancan lokaci ne fa kasashen biyu ke kallon juna cikin zargi.
Akwai dai fargaba kan batun mallakar makamin nukiliyar kasar ta Iran, fargabar da ta karu a shekarun 2000 inda aka samu rahotanni da suka nuna cewa kasar na shirin mallakar makamin nukiliya.
Amurka da kawayenta sun shiga fargaba cewa Iran cikin sirri na shirin mallakar makamin nukiliya, yayin da Iran ke ci gaba da kafewa kan bakanta cewa shirinta don amfanar al’umma ne.
A shekarar 2015 an samu babbar nasara ta faru ta rattaba hannu kan hadakar yarjejeniya gudanar da aiki ta (JCPOA). Karkashin wannan yarjejeniya Iran ta amince ta takaita shirinta na mallakar makamin nukiliya, sannan aka ba wa masu sa idanu na kasa da kasa su sanya idanu kan aikin, sannan aka janye takunkumai da aka saka mata.
Sai dai yarjejeniyar ta samu rauni a 2018, lokacin da Donald Trump a mulkinsa na farko a matsayin shugaban kasa ya janye Amurka daga cikin yarjejeniyar.
Gwamnatin ta yi da’awa cewa Yarjejeniyar ta JCPOA ba ta zurfafa ba wajen hana kasar ta Iran mallakar makamin nukiliya, sai Amurka ta sake kakaba takunkumi ga kasar ta Iran sannu a hankali kuma ta janye daga yarjejeniyar da aka kulla.
Tun daga wancan lokaci ne aka shiga tsamin dangantakar diflomasiya da matsin tattalin arziki har da tsayayyar aikin soja ko da yake ba a kai ga yaki ba.
Hadarin mallakar makamin nukiliya
Rikicin da ke faruwa kawo yanzu, na da nasaba da muhawarar da ake kan hakkin amfani da nukiliyar a shiri na zaman lafiya don makamashi, kasancewar daya daga cikin kasashen da suka sanya hannu a yarjejeniyar ta shekarar 1970 wato Iran ta kafe cewa shirinta na nukiliya a wurare kamar Natanz da Fordow da Isfahan, ana yi ne don amfanar al’umma domin samar da hasken lantarki da batu na samar da magunguna.
Su kuwa kasashen Amurka da Isra’ila sun yi da’awa cewa yadda Iran ke zuba jari a harkar ta makamashi Uranium ya nuna a fili shirinta na kokarin mallakar makamin nukiliya ne.
Halin da ake ciki game da batun na Uranium a Iran , rahotanni daga Cibiyar Kula da makamashi ta kasa da kasa (IAEA) ya zuwa 2025, ya kara jaddada muhawara kan batun na Iran.
Gudanar da shirin na Uranium don mallakar makamashi lantarki sai an daga darajar uranium ya kai kaso 3.5% ko 5%.
Sai dai hukumar ta IAEA ta ba da rahoto da ta ce darajar na Iran ya kai kaso 60% abin da ke nuna cewa ta tunkari mataki na kaiwa ga mallakar makamin na nukiliya Wanda ake bukatar akai kaso 80% na bukatar uranium-235.
Makaman nukiliya sune mafiya hadari da aka taba sanarwa wanda su kan fitar da abubuwa masu hadari.
Hadarinsu bai tsaya iya lalata abubuwa da aka kai wa farmaki ba cikin dakika makamin nukiliya daya zai iya halaka birni guda ya kashe dubban daruruwan na mutane sai kuma sinadaran turiri da suke fitarwa da ke tasiri ya haifar da cutar kansa da lalata muhalli.
Duniya ta sheda illar makamin kare dangi a karon farko saboda babbar illar da yayi a watan Augusta shekarar 1945 lokacin ruwan bama-bamai na Hiroshima da Nagasaki inda Amurka ta halaka dubban daruruwan mutane a wadannan hare-hare da ta kai.
A Hiroshima ita kadai bisa kiyasi akwai mutane kimanin 70,000–80,000 ne suka halaka sannan aka kara samun kimanin mutane 140,000 da suka halaka dalilin ciwuka da suka samu dalilin turiri na makamin.
Haka kuma a Nagasaki, kimanin mutane 40,000 suka halaka take, sannan an samu kimanin mutane 70,000 da suka halaka sannan wadanda abin ya shafa sun samu illoli na tsawon lokaci da cutar kansa da wasu cutika masu illa.
Ta Yaya hakan zai shafi Najeriya?
Duk da cewa a siyasance za a ga Najeriya ta yi nisa da inda ake wannan rikici ta fuskar tattalin arziki ‘yan Najeriya abin ya shafe su musamman ta fuskar farashin man fetir.
Tashin hankali da Iran ta fada zai shafi duniya kasancewarta ta tara mafi girma wajen fitar da albarkatun Mai a duniya, wannan kan girgiza kasuwar hada-hadar mai a duniya.
Gabas ta Tsakiya ta kasance muhimmiya wajen samar da albarkatun mai kuma barazana ga hanyar da ake fitar da mai babban kalubale ne kamar a hanyar mashigar tekun ta Hormuz, wannan zai sanya adadin mai da ake fitarwa ya ragu, wanda ba makawa farashin mai zai tashi.

Abubuwan da ake jigilarsu ta mashigar tekun ta Hormuz. Inda aka samo: UNCTAD
A makonni na baya-bayan nan farashin mai ya daga
daga N1,051.47 a duk lita a watan Fabrairu 2026 inda ya kai N1,200 da N1,300 a watan Maris, ya danganta da a wane waje ne a Najeriya.
Masu sharhi suna alakanta tashin farashin na mai da tashinsa a kasuwar duniya saboda dalilin wannan rikici.
Duk da cewa Najeriya na samar da albarkatun Mai tana ji a jikinta saboda tashin farashin mai a duniya ga batun musayar kudade da shigo da mai da barin kasuwa ta yi alkinta.
Wannan na nufin idan akwai tashin hankali a duniya, Najeriya na kashe kudade masu yawa wajen jigila da kayan abinci da lantarki da sauransu.
Tashin farashin man jirgi na da alaka da yadda ake samar da shi a duniya, idan aka samu tasgaro wannan na tasiri a fannin jigilar jiragen saman wannan na sanyawa mahukunta a Najeriya su bukaci masu jiragen kada su dakatar da jigilar jiragensu ko su daga farashin jigilarsu.