Site icon Dubawa

Yaudara ce! Ba ƴan sanda 10 aka kashe ba a harin ’yan bindiga a Sokoto

Misleading! One police officer, not 10, killed in Sokoto bandit attack

Jami’an ’yan sanda. Mallakar Hoto: FB/Nigeria Police Force

Da’awa: Wani mai amfani da X ya yi ikirarin cewa ’yan ta’addan Fulani masu jihadi sun yi wa jami’an ’yan sandan Najeriya 10 kwanton bauna tare da kashe su.

Yaudara ce! Ba ƴan sanda 10 aka kashe ba a harin ’yan bindiga a Sokoto

Hukunci: Yaudara. Duk da cewa lamarin ya faru ne a ƙaramar hukumar Kebbe ta jihar Sokoto, bayanai sun nuna cewa ɗan sanda ɗaya ne aka kashe, yayin da aka ƙona motocin sintiri guda biyu.

Cikakken Bayani

Wani mai amfani da shafin X, Okanumee Uchechukwu (@okanumeee2), ya wallafa wani bidiyo yana ikirarin cewa ’yan ta’addan Fulani masu jihadi sun yi wa jami’an ’yan sanda 10 kwanton bauna tare da kashe su gaba ɗaya, yana cewa babu wani jami’i da ya tsira.

Rubutun, (wanda aka adana a nan), ya ambaci Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, Gwamnatin Najeriya, Shugaban Amurka da Human Rights Watch, tare da zargin gwamnatin Najeriya da kasancewa ƙungiyar ta’addanci.

Rubutun ya ce, “’Yan ta’addan Fulani masu jihadi sun yi wa jami’an ’yan sandan Najeriya 10 kwanton bauna jiya @PoliceNG kuma suka kashe su gaba ɗaya. Babu wanda ya tsira; har zuwa yanzu babu wani ɗan Najeriya, kafafen sada zumunta da gidajen watsa labarai da ke magana a kai. @NigeriaGov ita ce babbar ƙungiyar ta’addanci. @POTUS @hrw.”

Ya zuwa ranar 14 ga Agusta, 2026, bidiyon ya samu maasu kallo mutane 101,400, martani 99 da sake wallafawa 950.

Da yake mayar da martani kan da’awar, Sinachi (@OPromeese) ya zargi hukumomin tsaro da rashin mayar da martani yadda ya kamata ga matsalar ’yan bindiga, yana cewa a wasu lokuta jami’ai kan kama waɗanda ake zargi amma daga baya a sake su.

Wani mai amfani da X, Delores Barnum (@DonaldBarnum3), ya kuma yi shakku kan da’awar, yana cewa lamarin kamar an shirya shi ne. Delores ya ce, “Ba da daɗewa ba gwamnatin jihar za ta nemi Naira biliyan 230 a matsayin kasafin kuɗin tsaro.”

Mun kuma gano irin wannan bidiyon da aka wallafa a X da Facebook a nan da nan.

Saboda yiwuwar da’awar ta yaudari jama’a, DUBAWA ta gudanar da bincike domin gano abin da ya faru.

Tantancewa

Da farko, DUBAWA ta duba bidiyon da aka wallafa tare da da’awar. Bidiyon ya nuna wasu mutane ɗauke da makamai suna ikirarin nasara yayin da suka zagaye da motoci du suka cinnawa wuta. DUBAWA ta tabbatar da cewa harshen da ake magana da shi a bidiyon Hausa ne.

Ɗaya daga cikin mutanen ɗauke da makami a cikin bidiyon ya ambaci ƙaramar hukumar Kebbe, abin da ya ba da alamar wurin da lamarin ya faru. Kebbe gari ne kuma ƙaramar hukuma da ke jihar Sokoto, a Arewa maso Yammacin Najeriya.

DUBAWA ta kuma gudanar da bincike da ido kan motocin da aka nuna a bidiyon. Alamomi da tambarin ɗaya daga cikin motocin sun nuna cewa motar Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ce daga Hedikwatar ’Yan Sanda ta Yankin Kebbe.

Yaudara ce! Ba ƴan sanda 10 aka kashe ba a harin ’yan bindiga a Sokoto

Hoton motar ’yan sanda.

Daga nan, DUBAWA ta gudanar da binciken kalmomi ta amfani da bayanan da ke cikin bidiyon, inda ta gano rahotannin wata arangama mai tsanani tsakanin jami’an tsaro da ’yan bindiga a ƙaramar hukumar Kebbe ta jihar Sokoto.

Rahotannin jaridun Daily Trust, Leadership da Daily Post sun danganta lamarin da sabbin hare-haren da aka kai a ƙaramar hukumar Kebbe ta jihar Sokoto a ranar 3 ga Agusta, 2026.

Rahotannin sun nuna cewa ɗan sanda ɗaya ne kawai, wato Mataimakin Sufeto na ’Yan Sanda (ASP) Bala Wakili, aka kashe a yayin harin.

An kuma ruwaito cewa ’yan bindigar sun ƙona motocin sintiri guda biyu; ɗaya mallakar Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ce, ɗayan kuma mallakar Rundunar Tsaron Al’umma a Sokoto.

Mai magana da yawun Rundunar ’Yan Sandan Jihar Sokoto, DSP Ahmad Rufa’i, shi ma ya tabbatar da harin a cikin rahoton, yana cewa wani ɗan sanda “ya yi saudaukarwa mai girma” a bakin aikinsa.

A Ƙarshe

Da’awar cewa ’yan ta’adda sun yi wa jami’an ’yan sandan Najeriya 10 kwanton bauna tare da kashe su gaba ɗaya yaudara ce. Duk da cewa harin ’yan bindiga ya faru a ƙaramar hukumar Kebbe ta jihar Sokoto, bayanani sun nuna cewa ɗan sanda ɗaya ne kawai, ASP Bala Wakili, aka kashe, yayin da aka ƙona motocin sintiri guda biyu.

Exit mobile version