Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya yada wani bidiyo bisa da’awar halin da aka shiga bayan kai farmaki a Najeriya.

Hukunci: Yaudara ce! Hoton bidiyo da aka nuna yanayin gari yayi fata-fata bayan harin ta’addanci, a Sudan lamarin ya faru ba a Najeriya ba.
Cikakken Labarin
A tsawon shekaru Najeriya na ci gaba da fuskantar hare-haren ta’addanci, lamarin daya zama silar rasa rayukan al’umma da dama a sassa daban-daban na kasar.
A baya-bayan nan wani mai amfani da shafin X @SadiqMaunde ya yada
bidiyo (kamar yadda aka alkinta a nan) wanda ya nuna irin barna da ‘yanta’adda suka yi a wani gari da ya zama kufayi a Najeriya.
“Wannan ba a Afganistan da Siriya ko wani wasan kwaikwayo ba ne. Wannan shine halin da muka samu kanmu a wannan kasa karkashin mulkin APC a Najeriya,” kamar yadda mai da’awar ya nunar.
An sake yada irin wannan wallafa a shafin na Facebook, kamar yadda ake iya gani a wadannan wurare nan da nan da nan.
Ya zuwa ranar Alhamis 30 ga watan Augusta 2026, wannan bidiyo an kalle shi sama da sau 215,000 da masu nuna sha’awa 4,200 da masu sake wallafawa 2,400 da masu nuna alamar za su sake dubawa 586 da masu kafa hujja 140.
Yayin da wasu cikin masu tsokaci ke ci gaba da caccakar gwamnatin Tarayyar Najeriya wasu na nuna shakku a dangane da sahihancin wannan wallafa.
“Abin takaici, a tsawon shekaru 12 na wannan gwamnati tun daga 2015 har yau lamarin tsaro na ci gaba da tabarbarewa!…, a cewar @Topmanlamb.
Shima a nasa tsokaci@Imnottgaius yace “ Abin takaici, bama ganin irin wannan a labarai.”
Shi kuwa @Bosas38 ya rubuta cewa” bishiya da aka dasa a tsakiyar kan titi, ba da hanya zancen gangan.”
Duba da yanayi na matsalar tsaro da fargabar da ake da ita ga kuma yawan mutane da suka ga wannan wallafa, hakan ya sanya ya zama wajibi ga DUBAWA ta tantance labarin.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da bincike na gano asalin hoto inda wannan ya kaimu ga bidiyo da aka wallafa a shafin Instagram a ranar 18 ga Agusta,2026.
Wallafar ta nunar da cewa wannan bidiyo an dauke shi a garin da ke zama kufayi na Al-Fashir da ke kasar Sudan, bayan shekaru da aka dauka ana gwabza fada tsakanin dakarun Rapid Support Forces (RSF) da na Sudanese Armed Forces (SAF), fada da ya sanya dubban mutane suka kauracewa muhallansu.
“A kalla mutane 59,000 aka kashe a fadan da aka yi a cewar mahukunta sai dai ana ganin adadin yafi haka, zai iya kaiwa dubban daruruwa, idan aka tattara wadanda suka rasu ta dalilin yunwa da cutuka bayan da harkokin kula da lafiya suka rushe, “ a cewar wani bangare na wallafar.
Da aka zurfafa a bincike sai aka samu wasu bidiyo suma da aka wallafa a shafin Facebook, kamar a wadannan wurare nan da nan, wadanda aka alakanta da rikicin da ke faruwa a Sudan.
Mun kuma samu rahoto da aka wallafa JINHA, kamfanin dillancin labaran Mata, a ranar 4 ga Agusta,2026, wanda ya ba da rahoto kan halin da ake ciki a rikicin Sudan, yakan ba da rahoto kan halin da ake ciki a sassa daban-daban na kasar, da kisan gillar da ake dangantawa da dakarun Rapid Support Forces (RSF), yayin da rikicin ke kara ta’azzara ba da kariya ga fararen hula na kara samun koma baya.
A baya-bayan nan Al Jazeera ta ba da rahoto cewa dubban mutane sun yi kaura zuwa Kordofan da ke Arewaci bayan harin da dakarun na RSF suka kai a kauyuka da ke yankin.
Majalisar Dinkin Duniya ita ma ta ba da rahoto cewa a baya-bayan nan rikicin da ya barke a Sudan yayi sanadi na raba kimanin mutane 200,000 da muhallansu tun daga karshen 2025.
A karshe
DUBAWA a bincike da ta gudanar ta gano cewa bidiyon da aka dauka a Sudan ne ba a Najeriya ba, don haka da’awar yaudara ce.