Da’awa: Wani shafin Facebook mai suna 9News Nigeria, ya wallafa bidiyon da ke da’awar wai an kama “wani Fulani dan bindiga cikin kayan sosjoji na bogi” Osogbo, jihar Osun.

Hukunci: Yaudara ce! Duk da cewa da gaske ne an kama wani a Osogbo kamar yadda aka nuna a bidiyon, ’yan sandan jihar Osun sun fda wa DUBAWA cewa mutumin na fama da tabin hankali kuma ba dan bindiga ba ne kamar yadda ake da’awa.
Cikakken bayani
Yayin da ake cigaba da damuwa a kan tsaro a yankuna daban-daban na kasar, da ma rudanin da ake samu sosai wasu masu haddasa husumi suna amfani da damar wajen yada labaran da ba daidai ba. Wani bidiyo mai tsawon dakiku 54 wanda ya yadu sosai a shafukan sada zumunta na da’awar wai wani dan fulani ne sayen da kayan sojoji aka kama a garin Osogbo na jihar Osun.
Wani shafin Facebook mai suna, 9News Nigeria, ya wallafa bidiyon tare da yi masa take kamar haka: “Bidiyo: An kama wani wanda ake zargi fulani dan bindiga ne sanye da kayan sojojin bogi a Osogbo.”
Wasu su ma wadanda suke da taskokin blog sun wallafa da’awar, irin su Lagos Reporters a shafin Instagram, Glow 99.1 FM Akure a Facebook, da wasu karin shafukan a kan dandalin na Facebook.
A wajen yin kwament ko tsokaci a karkashin wadannan labaran ya nuna cewa yawanci sun yarda da labarin, suna jinjinawa jami’an tsaron da ake da’awar sun kama mutumin tare da kira da a tuhume shi a gudanar da bincike. Sai dai akwai wasu a cikinsu su kuma wadanda suke shakkun sahihancin batun inda suka bukaci da a ba su hujjojin da za su tabbatar musu da cewa lallai matashin babban mai laifi ne.
Alal misali, Sorinmade Kayode ya yi kira da a kashe mutumin nan take; “A kashe shi kai tsar,” ya rubuta.
Wani shi ma mai amfani da shafin, Bello Shehu, ya ce, “ Ku fadi gaskiya, da’awar da ba za’a iya tantancewa ba…” yayin da shi kuma Amusayin Joseph ce wa ya yi, “Shin yaya gaskiyar wannan batun?”
Ganin yadda ake cigaba da fama da kalubalen rashin tsaro a kasar da ma irin tasirin da labaran karya kan tsaro ke da shi a kan al’umma ya sa DUBAWA tantance gaskiyar lamarin.
Tantancewa
DUBAWA ta yi bitar bidiyon inda ta gano cewa ya na nuna mutane ne da dama a bakin hanya suna jan wani matashi a kasa. Mun kuma ga cewa lallai akwai jami’an tsaro a cikin mutanen.
Daga sautin bidiyon, ana iya jin muryar wata mata tana ihu, “Dan bindiga a Osogbo sanye da kanyan sojoji na bogi.” To sai dai ba ya ga muryar wannan matar bidiyon kansa bai bayar da wasu hujjojin da suka tabbatar da cewa matashin dan bindiga ne ba.
Domin tantance sahihancin bidiyon, DUBAWA ta cire mahimman hotuna daga bidiyon ta sa cikin manhajojin da ke tantance mafari da sahihancin bidiyoyi wato reverse-image search engines a turance.
Daga sakamakon binciken, babu majiyar ta bayyana da hujjoji ko bayanan da su ka dace da labarin ko ma wadanda za su iya tabbatar da ko shi matashin wane ne bare ma su iya tabbatar da abin da aka ji a cikin bidiyon..
A waje guda kuma, DUBAWA ta gano rahotanni da dama dangane da wannan lamarin. Kafofin yada labarai irin su People’s Gazette, Daily Post, da Punch sun yi rahoton cewa rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta kama wani mutumin bisa zarginsa da kasancewa dan bindiga.
Yayin da jaridar Daily Sun, ta rawaito cewa “ana gudanar da bincike kan “mutumin da ake zargi dan bindiga ne” bayan da aka kama shi a Osogbo.”
Dan fayyacewa, DUBAWA ta tuntubi rundunar ‘yan sandan jihar Osun kuma ‘yan sandan sun tura mana bayanin da suka bai wa manema labarai. Bayanin wanda suka fitar ranar 8 ga watan Yunin 2026 jami’in hulda da jama’an ‘yan sandan, DSP Abiodun Ojelabi ya ce ‘yan sandan sun ma kammala bincikensu.
Sun ce a binciken sun gano wuka, wandon sojoji, layu, da wasu rigunan sa wa daga wurin matashin.
Sai dai ‘yan sandan sun ce da suka cigaba da binciken sun gano cewa matashin na da shekaru 38 na haihuwa kuma sunan yankan sa Adebayo Sunday. Rundunar ta ce matashin ya nuna alamun tabin hankali sadda suka yi masa tambayoyin, kuma ma da ma ya na da tarihin tabin hankalin. Masu bincike daga baya sun tuntubi wani mai maganin gargajiya wanda ta tabbatar mu su cewa ya taba ba shi magungunan tabin hankali fiye da shekaru goman da suka gabata.
Haka nan kuma ‘yan sandan sun kai shi asibitinsu kafin aka kai shi asibitin kula da masu tabin hankali dan samun magungunan da suka dace.
Abu mai mahimmanci shi ne ‘yan sandan ba su ce mutumin dan Fulani ba ne ba su kuma bayar da wasu hujjojin da ke danganta Adebayo da harkokin ‘yan bindiga ba. Sun dai ce ya na fama da tabin hankali.
A Karshe
Da’awar cewa wani bidiyo na nuna dan bindiga Fulanin da aka kama a Osogbo ya na sanye da kayan sojoji na bogi yaudara ce. Yayin da bidiyon ya nuna a zahiri cewa an yi kamen ne a Osogbo, hujjoji da bayanan da samu ba su goyi bayan wai mutumin Fulani ne ba ko ma dan bindiga.