Site icon Dubawa

Yaudara ce! Hoton mutanen da suka yi hadarin jirigin ruwa a jihar Sokoto ne ake da’awar wai harin da aka kai wani masallaci a jihar Neja ne

Misleading! Image of Sokoto boat mishap victims attributed to Niger mosque attack

Da’awa: Chukwudi Collins a shafinsa na Facebook ya wallafa wani hoto inda ya nuna wasu mutanen da ya ke da’awar wai sakamakon harin aka kai wani masallaci ne ranar 21 ga Agusta 2026 a karamar hukumar Borgu da ke jihar Neja.

Yaudara ce! Hoton mutanen da suka yi hadarin jirigin ruwa a jihar Sokoto ne ake da'awar wai harin da aka kai wani masallaci a jihar Neja ne

Hukunci: Yaudara ce! Sakamakon binciken da DUBAWA ta gudanar ya nuna cewa hotan ba a dauke shi a lokacin da aka kai hari kan masallacin jihar Naje ba. Hoton ya nuna gawanwankin mutanen da suka mutu a karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto ne a dalilin hadarin jirgin ruwa.

Cikakken Labari 

Chukwudi Collins a shafinsa na Facbook ya saka wani hoto (A nan) kuma a wani dandalin hira na abokansa inda yake cewa gawanwakin mutanen da suka mutu a dalilin harin da aka kai a wani masallaci yayin da ake sallan Juma’a a wasu kauyuka hudu dake karamar hukumar Borgu a jihar Neja ranar 21 ga Agusta 2026.

Da’awar da aka yi a hoton ya ce “Labari da duminsa: An kashe mutum 30, an yi garkuwa da wasu da dama a harin da aka yi a masallaci. Mutum 30 sun gamu da ajalinsu bayan mahara sun kai hari a kauyuka hudu a karamar hukumar Borgu dake Neja yayin da ake sallan Juma’a ranar 21 ga Agusta. An rawaito cewa mahara sun yi garkuwa da mutane da dama a dalilin harin amma wani bidiyo da ya kareda kafafen sada zumunta na yanar gizo ya nuna cewa mutum 600 ne aka yi garkuwa da su.

Zuwa ranar 30 ga Agusta 2026 mutum 13 sun nuna suna son hoyton, 2 sun mai da martani da 7 sun sake wallafa hoton. Mutane ba su fadi ra’ayinsu ba saboda wanda ya saka hoton ya saka ne a shafin da sai an amince da martanin da mutum ya yi kafin ake iya gani a fannin mai da martani na shafin.

Seyi Adedokun ya ce “Adinin salama kenan”.

Prince Adeogo ya gargadi mazaunan kudu da tsakiyar Najeriya da su rika zama a fadake kan abin da ya kwatanta shi da masu so fadada yankin Fulani.

Hakan ya faru yayin da Arewa maso Yammacin Najeriya ke fama da hare-haren mahara inda hakan ya sa DUBAWA ta gudanar da bincike.

Tantancewa 

Dubawa ta gudanar da bincike domin gani asalin inda aka samu hoto sannan da alakan hoton da harin masallacin da aka yi a jihar Neja.

Sakamkon binciken ya nuna cewa hoton na da alaka da mutuwar mutane a dalilin wani hadarin jirgin ruwa da aka yi a jihar Sokoto.

Wani sakamakon binciken ya nuna hoton yana da alaka da wani rahoto da gidan jaridar Al Jazeera ta wallafa a ranar 20 ga Agusta 2026. Da’awar da aka rubuta a hoton ya ce wannan gawanwakin mutanen da suka yi hadarin jirgin ruwa ne a jihar Sokoto.

THE STRAITSTIMES ya wallafa hoton a rahotan da ya fitar game da hadarin jirgin ruwan. Hadarin ya faru a kusa da kauyen Gorau dake karamar hukumar Goronyo dake jihar Sokoto ranar 20 ga Agusta.

DUBAWA ta kuma gano wani rahoto da Reuters ta yi game da hadarin inda rahotan ya gabatar da cikakkun bayanai game da hadarin da mutanen da hadarin ya shafa.

Gidan jaridar ta kuma gano wani bidiyo da Channels Television da ya nuna jana’izan mutanen da suka mutu a dalilin hadarin jirgin ruwan. Wasu wuraren da bidiyon ya nuna na kama da hotan da aka saka wanda hakan ya kara tabbatar da alakar hoton da hadarin jirgin runan jihar  Sokoto a maimakon harin masallacin da aka yi a jihar Neja.

Harin masallacin da aka yi a jihar Neja ya faru. A wani rahoto da gidan jaridar PREMIUMTIMES ta yi shugaban karamar hukunmar Borgu ya tabbatar cewa mutum 30 sun mutu a harin da aka yi a masallaci yayin da ake sallar Juma’a ranar 21 ga Agusta.

Duk da cewa harin ya faru amma hoton da Chukwudi Collins ya yada a yanar gizo na da alaka ne da hadarin jirgin ruwan da aka yi a jihar Sokoto ba harin masallacin jihar Neja ba.

A Karshe

Hoton da aka saka bashi da alaka da harin masallacin da aka yi a jihar Neja yaudara ce kawai. Amma hoton na da alala da hadarin jirgin ruwan da aka yi a karamar hukumar Goronyo a jihar Sokoto. Rashin fahimta ne ya sa ake ganin hoton na nuna harin da aka yi a masallaci a jihar Neja.

Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).

Exit mobile version