Da’awa: Kafofin yada labarai da dama a watan yunin 2026 sun yi rahoton cewa dan bindigan TikTok mai kaurin suna Sule Yellow ya shiga hannun dakarun sojoji inda wasu ke da’awar cewa ba da dadewan nan ba ya faru.
Hukunci: Yaudara ce! Duk da cewa da gaske ne jami’an tsaro sun kama Suke Yellow, hujjojin da muke da su na nuna cewa tun watan Maris na shekarar 2026 aka kama shi, bisa bayanan kafofin yada labarai wadanda suka hada jar da jaridar The Cable da TVC News.
Cikakken bayani
Ranar 6 ga watan yunin 2026, kafofin yada labarai da dama wandanda suka hada har da Oyo News, PM News Nigeria, Daily Post Nigeria, da Nairaland, duk suka yi rahoton cewa sojojin Najeriya sun kama dan bindigan nan na TikTok mai kaurin suna, Sule Yellow.
Rahotannin sun yi labarin kamar kwanan ne abin ya faru, inda wasu ma suka yi bayanin kamen kamar wani babban cigaba ne aka samu a bangaren tsaro.
A labarin da aka wallafa a Oyo News (ana iya ganin shi a nan) an yi mi shi take kamar haka, “Notorious TikTok bandit, Sule Yellow, has been arrested by the Nigerian Army after reportedly collecting ransom from a victim’s family. Wato ‘Dan bindiga mai kaurin suna na TikTok ya shiga hannun dakarun sojojin Najeriya bayan da ya karba kudin fansa daga iyalan wadansu wadanda ya kama.
Da Oyo News suka wallafa wannan labarin a shafin su na Facebook, daga 24 ga wtaan Yunin 2026 ya sami alamar like sama da 18,000, an yi tsokaci sama da 4,000 sa’annan an sake rabawa sau 768.
Haka nan ita ma jaridar, PM News Nigeria (kamar yadda za ku iya gani a nan) ta wallafa rahoton da ta yi wa taken, “Sule Yellow: An kama dan bindigan da aka san shi da nuna kudi a TikTok.”
Jaridar Daily Post Nigeria mata wallafa labarin (wanda za ku iya gani a nan) da taken, “Dakarun Najeriya sun kama dan bindigan TikTok, ‘Sule Yellow’ (ga bidiyon).”
Da muka yi nazarin duka rahotannin mun lura cewa duk labaran iri daya ne, dukasun yi da’awar cewa dakarun sun kama Sule Yellow ne yayin da ya ke komawa maboyarsa a jeji bayan da ya karbi kudin fansa daga iyalan wasu wadanda ya yi garkuwa da su.
Ganin yadda labarin ya dauki hankali ne ya sa DUBAWA tantance batun.
Tantancewa
DUBAWAta fara da gudanar binciken mahimman kalmomi inda ta gano cewa tun da dadewa aka kama Sule Yellow kuma an yi labarin watanni da daman da suka wuce.
TheCable ta wallafa rahoton ranar 16 ga watan Maris ta taken “Jami’an tsaro sun kama dan bindiga bayan da ya gama nuna bidiyon kudin fansar da ya samu a kan wadanda ya yi garkuwa da su.”
Rahoton ya yi bayani dalla dalla kan yadda aka kama Sule Yellow bayan da ya kammala wani bidiyon TikTok din da ya yi kai tsaye inda ya rika alfahari da garkuwar da ya ke yi da jama’a ya na samun kudi. TheCable ta kuma kwatanta bidiyon ta na cewa Yellow na cikin ankwa kewaye da jami’an tsaro.
TVC News ma ya wallafa rahoton a daidai wannan lokacin.
Da muka yi bitar rahotannin watan Yunin 2026 da na Maris 2026 mun ga akwai kamanceceniya a tsakaninsu musamman a cikin irin bayanan da suka yi dangane da abubuwan da suka faru, da kwatancen da ma kamen abin da ya nuna cewa duk batu daya ne suke bayani a kai.
DUBAWA ta kuma duba ta gani ko akwai wata sanarwar da sojojin Najeriya suka yi kwanan nan danage da kamen Sule Yellow cikin watan Yunin 2026, sai dai ba mu sami wani labari haka ba har sadda muka wallafa wannan rahoton.
Hujjojin da muka samu sun tabbatar da kamen Sule Yellow, amma ba kwanan nan ba ne. Bisa dukkan alamu an sake dawo da wadannan rahotannin ne.
Da suka gabatar da rahotannin ba tareda sun fayyace taka mai mai sadda aka kama shi ba tunda lamarin ya faru ne watanni da dama da suka gabata, rahotannin sun sa mutane ganin kaman kwanan nan ne lamarin ya afku.
A Karshe
Da’awar wai jami’an tsaro sun kama Sule Yellow kwanan nan yaudara ce kawai. Kafofin yada labarai masu nagarta sun nuna cewa tun watan Maris 2026 aka kama shi.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.