Da’awa: Ife Agoro, mai kamfannin DANG Lifestyle brand, ta wallafa wani bidiyo video a shafin X inda tayi da’awar cewa da zarar mace shekarunta sun kai 33 kwan haihuwarta zai fara rasa ingancinsa.

Hukunci: Yaudara ce. Shedun masana ilimin kimiya da jawaban kwararru sun nunar da cewa kwan haihuwa na ‘ya mace na fara rasa inganci ne ko karkonsa idan ta kai shekaru 35 ba 33 ba.
Cikakken Sako
A ranar 24 ga watan Mayu, 2025, Ife Agoro, mai kamfanin kayan kawa da yada bidiyo a shafin intanet na X ta fitar da wani sako a shafinta na (@diaryofa9jagirl), inda tayi jawabin cikin wannan bidiyo video (an killace shi nan here) take ba da labari yadda ake alkinta kwan haihuwa. Ta ba wa mata shawara su alkinta kwan haihuwarsu kafin su kai shekaru 30, tace mace na kaiwa 33 kwan haihuwarta zai fara samun rauni ko ingancinsa ya ragu.
“Mace na cika shekaru 33 ingancin kwan haihuwarta zai fara raguwa” a cewar Ife a bidiyonta mai tsayin dakika 59.
Wannan bidiyo ya yadu matuka inda mutane suka shiga mayar da martani da tsokaci a shafin na intanet.
Ya zuwa ranar 15 ga watan Yuni,2025 wannan wallafa ta samu mutane miliyan daya da suka gani (views) da mutane 869 da suka sake wallafawa (repost) da mutane sama da 1,800 da suka nuna sa’awarsu (likes)
Wata mai amfani da shafin na X (@Kumms) quoting ta kafa hujja da wannan bidiyo da tace ta ganshi a karo na biyu ana cewa “karko ko inganci na kwan haihuwa na raguwa a shekaru 33 Allah Ya kawo dauki.”
A mayarwa da @Kumms martani ko a nata tsokaci (FB @Ishuku) sai ta ce ‘’na yarda da wannan 100 bisa 100.”
@Kumms ta kara da cewa shekara guda ta rage mata idan har wannan da’awa gaskiya ce ta rubuta cewa “Abin tashin hankali shekara guda ta rage min.”
Preethi Kasireddy (@iam_preethi), Kwararriya a cibiyar harkokin da suka shafi samun haihuwa ta bayyana a wata wallafa cewa mata ba sa rasa inganci ko karko na kwan haihuwa a shekara 35 sai dai idan akwai wani dalili na rashin lafiya.
Tace idan mata na lura da lafiyarsu, kwan haihuwarsu zai kasance mai kyau ko inganci har karshen shekaru 30 ko 40.
Wata mai amfani da shafin na X, Taurus Groove (@jiggyjayy2), ta bayyana cewa muddin mace na yin jinin haila, za ta iya fitar da kwan haihuwa kuma za ta iya haihuwa.
Taurus ta ci gaba da cewa yawaitar haihuwa na karuwa idan mace ta wuce shekaru 35 saboda mace na fitar da kwai sama da daya a duk lokacin da hailarta ta zo ko jinin al’ada. Ta bayyana irin wannan wallafar da zama “abin haifar da fargaba”,
Juneteenth Ak (@Bronxspice3) wrote, ta rubuta ne cewa “ Suna nunawa kamar matan da suka haure 30 (wadanda ko kusa basu dena haila ba) kamar an kaisu bango, ba za su kara haihuwa ba. Fatan samun haihuwa na raguwa ne idan an haure 35 ba rana tsaka ba. Mata da dama a karshen shekaru 30 ko farkon 40 suna haifar ‘ya’yansu lafiyayyu.”
Ganin yadda wannan wallafa ka iya zama mai hadari, hakan yasa DUBAWA ta ga wajibcin gudanar da bincike kan abin da ya shafi samun haihuwa idan aka yi laakari da shekarun mace.
Tantancewa
Rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya World Health Organisation, ya nunar da cewa a duk cikin mutane 6 daya na iya fuskantar matsalar rashin haihuwa a rayuwarsa, abin da zai iya zama sila ta rashin fara samar da iyali. Wannan ya nunar da muhimmancin zuwa wajen kwararru don su dora mutum kan hanya, idan ya samu wannan matsala, musamman taimako da za su iya samu na tattalin kwan haihuwarsu da dorasu kan tsarin dashen kwan haihuwa na IVF.
Mujallar BBC science focus magazine ta yi karin haske da cewa wannan tsarin tattalin kwan haihuwa da ake kira (oocyte cryopreservation) hanya ce da masana harkar lafiya ke bi a sa wa mace wasu sinadarai da za ta kara samun kwayoyin haihuwa, ya ma hadar da kwashe kwan haihuwar mace a ajiye har sai lokacin bukata ya tashi a tsarin dashen haihuwa na IVF. Wannan shine tsarin fasaha da ake yayi (fastest-growing) ga miji da mata da suke bukatar haihuwa.
Shekaru na da muhimmanci kamar yadda Hukumar da ke kula da Kyankyasar kwai da samar da dantayi (HFEA) (stated) ta bayyana ne a takardar manema labarai cewa tattalin kwan halitta na samuwa cikin nasara la’akari da shekarun mace.
Wace hikima ke cikin kimiyar samun rauni a kwan halittar mace?
Mun tattauna da Akindele Akinwunmi, kwararren likitan mata a asibitin Victory Specialist Hospital a jihar Ogun,wanda yayi bayani kan kimiyar da ke cikin raguwar kyau ko karkon kwan halittar ‘ya mace. Yace duba da shedu na kimiya an tabbatar da cewa ita ‘ya mace ana haifarta da wani adadi na kwan haihuwa daga lokacin da ta balaga sai kwayayen su ragu zuwa 200,000 inda za su ci gaba da raguwa a duk lokacin da take jinin haila.
Ya kara bayani da cewa idan aka kalli kimiyar da ke cikin yin jinin haila, da zarar lokacin sakin kwan yayi yana tafiya ne cikin wani batutu da ake kira (fallopian tube) inda yake zuwa inda za su hadu da kwayar maniyyi na namiji sai su had, idan kuma babu maniyin sai wannan kwan da ake kira “VIP”
ya wargaje ya shige cikin jiki, yabi mahaifa sai a samu jinin haila. Yace kwan ana zabinsa a duk lokacin jinin haila na mace sai a zabi mafi kyau a cikinsu.
A duk lokacin da mace za ta yi haila kafin lokacin tana sakin kwan haihuwa don ya hadu da maniyin namiji, wannan yanayi shi ke zagayawa a duk wata har sai lokacin da mace ta kudiri aniyar daukar ciki bayan saduwa da namiji.
Idan har an haifi mace tana da kwayayen haihuwa kimanin 400,000 sai kuma aka dauki lokaci ba ta dauki ciki ba har sai da ta kai shekaru 30, wannan na nufin yawan adadi da karkon kwayayen haihuwarta sun ragu. Wannan baya nufin matan da shekarunsu suka ja ba za su iya daukar ciki ba, sai dai wadanda suke a farkon shekarunsu na 20 zuwa talatin sun fi lafiyar iya daukar ciki kafin shekaru 35.
”Wannan bayanin haka yake duba da wannan nazari 2020 study by the Assisted Reproduction Technologies, wanda ya nuna yiwuwar cimma buri da kaso 50%, 60%, ko 70% bisa kiyasi na abin da ake burin ganin an samu idan aka tsara yin ajiyar kwan halittar macen a tsarin na ajiyar wato (oocyte cryopreservation).”
Wannan nazari ya nunar da cewa mata da ke da shekaru kasa da 35 ana ganin kwan haihuwarsu na da inganci da kaso 21 idan aka kwatanta da kaso 17 da matan da ke da shekaru sama da 35. Idan kwan yana da kyau yafi sauki a samu nasarar alkinta kwan haihuwar idan aka kwatanta da kwayayen da basu da karko sosai, wanda sai an ta kokarin yin hakan wanda hakan kuma ke nufin kashe karin kudade. Kwai na matan da ke kasa da shekaru 35 yafi inganci idan aka kwatanta da matan da ke da shekaru sama da 35.
Da aka duba batun a mizani na kimiya ko son rai, Akindele yace tabbas a kimiyance mata suna da adadi na kwan haihuwarsu , idan suka haihu babu ci gaba da fitar kwan, kuma da zarar matan sun kai shekaru 35 su kan samu rauni. Ya kara da cewa akwai bukatar mata su samu ilimi na sanin wane lokaci ne suke da damar saurin daukar ciki.
Samuel Omopariola, kwarren likitan mata ne kuma masani kan abubuwan da ke jawo rashin haihuwa a asibitin koyarwa na Obafemi Awolowo University Teaching Hospital, ya bayyana cewa dantayi da ke cikin uwarsa a watanninsa na 7 na da kwayoyin haihuwa miliyan 7, idan ya fara girma tun bayan haihuwa har zuwa balaga a lokacin da aka fara jinin haihuwa wannan adadi na raguwa zuwa 400,000.
Daga shekaru 35 kwayayen za su ci gaba da raguwa saboda yawan jinin haila da ake duk wata, wanda zai sa yawan kwayayen da kyansu zai ci gaba da raguwa kuma yawan shekarun 35 ne ba 33 ba. Yace daga shekaru 45 sau tari daukewar jinin haila kan fara.
Kwararren masanin lafiyar yace a shekarun farko da mace ta fara jinin haila, a lokacin da take sakin kwan haihuwar da lokacin da take jinin, kwayaye da ke da hazaka wadanda ke zama lafiyayyu su ke kan gaba da ake zaba, sauran kuma sai a kyale su sai wani lokacin idan lokaci yayi nisa shekaru suka tura kwayaye mafiya kyau su ake dauka.
Duba da yadda abun da ya shafi haihuwa ake taka tsantsan da shi sai kwararren ya ba da shawarar cewa a asibitoci na haihuwa akwai bukatar a samar da kwararrun masu ba da shawara ga masu neman haihuwa ta yadda za su ba su shawarwari kan abin da ya kamata su yi ba tare da wata mtsala ba.Yace likitocin su zama masu gaskiya su fada wa marasa lafiya abin da ya dace bayan samun ingantattun bayanai a tattare bayanan a matsayin shedu don amfani a gaba.
Samuel ya kammala da cewa raguwar da ake samu na kwayoyin haihuwa da zarar mace ta kai shekaru 35 ko 40 ko 45 ko 50 zuwa sama ba za ta iya daukar ciki ba ko a yi mata dashe ta haihu, amma a kimiyance kyawun kwan haihuwarta na raguwa bayan ta kai shekaru 35.
Kwalejin da ke nazari kan sha’anin haihuwa a Amerika ta ba da haske notes cewa yayin da ake ganin dabara ce ga mata su alkinta kwan haihuwarsu musamman ga wadanda ke son haihuwa nan gaba a rayuwarsu, an fi ba da shawara ga matan da ke da cutar kansa su yi hakan don kada abin ya shafi damar da suke da ita ta samun haihuwa.
Haka kuma cibiyar kare bazuwar cutuka (Centre for Disease Control and Prevention) ta ba da haske cewa alkinta kwan haihuwa a lokacin da mace ke shekaru 20 yafi ba da damar samun haihuwa ko da kuwa a wace shekara mace ta so ta fara tara iyali.
A Karshe
Da’awar yaudara ce, shedu a kimiyance da binciken masana sun nunar da cewa
Kyau na kwayoyin haihuwar mace da yawansu yana raguwa ne daga shekaru 35 ba shekaru 33. Domin samun shawarwari da samun sakamako yafi kyau a tuntubi likitan mata.