Site icon Dubawa

Yaudara ce! Sarkin Musulmi bai goyi bayan wa’adin mulki na biyu na Tinubu ba

Misleading! Sultan of Sokoto did not endorse Tinubu's second-term bid

Shugaba Bola Tinubu tare da Sarkin Musulmi a Fadar Shugaban Ƙasa. Mallakar Hoto: FB/Bayo Onanuga.

Da’awa: Wani mai amfani da shafin X ya yi iƙirarin cewa Sarkin Musulmi na Sakkwato ya bayyana cewa Bola Ahmed Tinubu ne kaɗai zaɓin da ya dace, tare da kira a sake zaɓensa karo na biyu.

Yaudara ce! Sarkin Musulmi bai goyi bayan wa'adin mulki na biyu na Tinubu ba

Hukunci: Yaudara ce. DUBAWA ta gano cewa an cire kalaman Sarkin Musulmi daga ainihin mahallinsu. Ya yabawa Shugaba Tinubu ne kan kafa Ma’aikatar Raya Kiwo ta Tarayya tare da nuna goyon baya ga gyaran da gwamnati ke yi a ɓangaren kiwon dabbobi, ba wai ya goyi bayan wa’adin mulki na biyu ba.

Cikakken Bayani

Yayin da ake ci gaba da tattaunawa kan babban zaɓen Najeriya na shekarar 2027, wasu masu amfani da kafafen sada zumunta na ci gaba da yaɗa ikirarin cewa fitattun sarakuna da shugabannin addini na bayyana goyon bayansu ga ‘yan siyasa.

A ranar 1 ga Agustan 2026, wani mai amfani da shafin X, HABIBU YUSUF SODANGI (@HabibuYSodangi), ya yi ikirarin cewa Sarkin Musulmi na Sakkwato ya bayyana a bainar jama’a cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ne kaɗai zabinsu, tare da neman a kafa hukumar kula da fulani ko kuma ma’aikata ta musamman gare su.

Rubutun da ya wallafa (an adana a nan) na cewa, “Sarkin Musulmi na Fulanin Sakkwato ya fito a talabijin kai tsaye yana cewa, ‘Ko kuna so ko ba ku so, Tinubu ne kaɗai zaɓinmu, kuma muna so ya kafa mana Hukumar Fulani ko kuma wata ma’aikata domin wannan ta’addanci ya tsaya.’ Shin kun fahimci abin da nake nufi, ko kuwa sai na ƙara yi muku bayani?”

Zuwa ranar 2 ga Agustan 2026, rubutun ya samu masu kallo 3,691, martani 47, da sake wallafawa 52.

Da’awar ta jawo muhawara mai zafi tsakanin masu amfani da shafin.

Wani mai amfani da X, Aku Obinna (@AkuObinna18701), ya yi sharhi cewa, “Me Fulani suke samarwa a Najeriya? Wannan ƙasa ya kamata a raba ta, kowa ya kama gabansa.”

Shi kuwa OUT OF EXPERIENCE (@outexperienc) ya rubuta, “Wannan wata sabuwar manufa ce da ke ƙara bayyana. Gwamnatin ‘yan jihadi ce ke karɓar Najeriya.”

Sai dai wani mai amfani da shafin, Hamza (@aminuhs), ya yi shakku kan sahihancin da’awar, inda ya tambaya ko a wace tashar talabijin aka yi wannan hira da kuma ranar da aka watsa ta.

DUBAWA ta kuma gano irin wannan da’awa ana yaɗawa a wasu shafukan Facebook a nan, nan, nan da kuma nan.

Saboda tasirin da da’awar za ta iya yi ga fahimtar jama’a kan batutuwan siyasa, DUBAWA ta gudanar da bincike.

Tantancewa

DUBAWA ta fara ne da yin bincike ta amfani da muhimman kalmomin da ke cikin da’awar, amma ba ta samu wani sahihin rahoto daga kafafen yaɗa labarai da ke tabbatar da iƙirarin ba.

Daga nan ne DUBAWA ta gano wani bidiyon da ake yaɗawa dangane da ikirarin, sai dai an ɗauke shi ne yayin bikin buɗe babban taron ƙungiyar makiyayar ta Miyetti Allah (MACBAN) na 2026 da aka gudanar a Abuja ranar 30 ga Yulin 2026.

Binciken cikakken jawabin Sarkin Musulmi ya nuna cewa bai yi magana kan zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2027 ba, kuma bai bayyana goyon bayansa ga wa’adin mulki na biyu na Shugaba Bola Ahmed Tinubu ba.

Maimakon haka, ya yabawa Shugaba Tinubu ne saboda kafa Ma’aikatar Bunƙasa Kiwon Dabbobi ta Tarayya, yana mai bayyana hakan a matsayin wani ci gaba da ba a taɓa samu ba a fannin kiwon dabbobi.

A wani ɓangare na jawabin da yayi da Hausa, Sarkin Musulmi ya ce, “Ko kuna so ko ba ku so, gaskiya wannan abu ne da ba a taɓa yi ba. Dole ne mu gode masa, mu ƙara ba shi goyon baya domin ya ci gaba da ayyukan alherin da yake yi a wannan ƙasa.”

Har ila yau, ya yabawa Shugaban Ƙasa saboda kafa Kwamitin Sauye-sauyen Kiwon Dabbobi na Shugaban Ƙasa ƙarƙashin jagorancin Farfesa Attahiru Jega, yana mai bayyana cewa sauye-sauyen za su amfani makiyaya da manoma baki ɗaya.

Babu inda Sarkin Musulmi ya ce “Tinubu ne kaɗai zaɓinmu”, ko kuma ya buƙaci ‘yan Najeriya su sake zaɓen Shugaba Tinubu a shekarar 2027.

DUBAWA ta kuma duba rahotannin Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) da jaridar Tribune kan taron. Dukkan rahotannin sun ruwaito yabon da Sarkin Musulmi ya yi, amma babu inda suka ambaci cewa ya goyi bayan sake zaɓen Shugaba Tinubu.

A Ƙarshe

Da’awar cewa Sarkin Musulmi na Sakkwato ya bayyana cewa “Tinubu ne kaɗai zabinmu” tare da kira ga ‘yan Najeriya su zaɓe shi a wa’adin mulki na biyu yaudara ce.

Exit mobile version