Site icon Dubawa

Yaudare ce! Tsohon bidiyon wani hari a Burkina Faso ake yadawa a matsayin harin ‘yan bindiga kan sansanin soji a Najeriya

Misleading! Old Burkina Faso attack video shared as bandits attack at Nigerian military base

Da’awa: A Shafin Arise Again dake Facebook ne aka saka wani bidiyo dake nuna harin da mahara suka yi a sansanin sojoji a Najeriya.

Yaudare ce! Tsohon bidiyon wani hari a Burkina Faso ake yadawa a matsayin harin 'yan bindiga kan sansanin soji a Najeriya

Hukunci : Karya ce! DUBAWA ta gano cewa bidiyon ba daga Najeriya ba ne. Bidiyon na nuna harin da ‘yan ta’adda ‘Jama’at Nusrat al-Islam wal-Muslimin (JNIM) suka kai wa jami’an tsaro a kasar Burkina Faso.

Cikakken bayani

A ranar 20 ga Yuli 2026 ‘Arise Again’ a Shafin ta na Facebook ta saka wani bidiyo a (nan) wanda ke da’awar wai wasu mahara sun kai wa sansanin sojoji hari a Najeriya.

Bidiyon ya nuna yadda maharan suka rika barin wuta a sansanin tare da wata da’awar dake nuna cewa mahara sun kai wa sojoji hari.

Zuwa ranar 20 ga Yuli 2026 bidiyon mutum 32,000 suka kalla, 229 da suka so bidiyon, 36 sun mai da martani da 200 sun kara wallafawa. Da dama daga cikin wadannan mutane sun nuna amincewar su da bidiyan da da’awar dake tattare da shi dake nuna cewa maharani sun kai wa sansanin sojoji hari ne a Najeriya.

Nicholas Bonoh ya ce ‘Wai shin me ya sa mahara ke sanin inda sansanin sojoji suke amma sojoji basa sanin inda mabuyar mahara suke?

Joseph Gabriel ya ce “mafi yawan su sun samu horo ne a sansanin sojoji.”

DUBAWA ta gudanar da bincike ganin yadda ake ta yada bidiyon da yadda ake fama da rashin tsaro a kasar nan.

Tantancewa

DUBAWA ta dauki wasu bangarorin bidiyon domin gudanar da binciken a kansu ta hanyar amfani da ‘Google Reverse Image Search’ inda sakamakon ya nuna cewa bidiyon  ya dade a yanar gizo kafin wannan Shafin ya kara wallafa shi sannan bidiyon na da alaka da rahotanin da ake ta badawa kan hare-haren Jama’at Nusrat Al-Islam wal-Muslimin (JNIM) a kasar Burkina Faso ba a Najeriya ba.

JNIM kungiyar Salafi ce na ‘yan ta’adda dake alakanta kanta da Al-Qa’ida. Kungiyar na hana zaman lafiya a yankin Afrika ta Yamma.

JNIM na zaman ta a kasashen Burkina Faso da Mali sannan suna da rassa a wasu bangarorin Najeriya da Jamhuriyar Kasar Niger.

Sakamakon binciken da gidan jaridar ta gano sun nuna cewa bidiyon ya dade a yanar gizo da da’awar karyan cewa mahara sun kai wa sojojin Najeriya hari. DUBAWA ta gano cewa mutane da dama sun wallafa bidiyon a nan, nan da nan tun a watan Nuwanba 2025.

DUBAWA ta gano rubutun da wani masanin aiyukkan mahara Zagazola Makama ya yi inda ya karyata bidiyon a nan a shafinsa na X bayan an gabatar da shi a matsayin bidiyon dake nuna harin da mahara suka yi a sansanin sojoji a Najeriya. Rahotanin sun tabbatar cewa bidiyon na aiyukkan kungiyar JNIM ne da suka kai wa jami’an tsaro hari a kasar Burkina Maso wanda hakan ya zo dai-dai da sakamakon da DUBAWA ta samu.

Gidajen jaridu da suka hada da Daily Post da TVC News sun rawaito da farko cewa a ranar 27 ga Maris 2025 Rundunar Sojin Najeriya ta musanta bidiyon dake nuna cewa mahara sun kai wa sansamin sojoji hari a Arewa. Bisa ga rahotan kungiyar JNIM ne suka kai wa jami’an tsaron Burkina Faso hari a Pama daga ranar 29 zuwa 30 ga Janairu 2025.

Hujojjin da aka samu sun nuna cewa tsohon bidiyo ne da aka dauko aka sake wallafawa da da’awar cewa mahara sun kai wa sansanin sojoji hari a Najeriya a kwanannan.

A Karshe

Bidiyon bai nuna cewa mahara sun kai wa sansanin sojoji hari a Najeriya ba. Bidiyon na harin da kungiyar JNIM ne suka yi a Burkina Faso wanda ya dade a zaune a yanar gizo amma aka sake wallafawa da da ‘awar karyan dake alakanta shi da rashin tsaron da ake fama da shi a Najeriya. A dalilin haka wannan bidiyo karya ce.

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.

Exit mobile version