Kare hakki, samar da daidaito mai dorewa da kuma tabbatar da hanyoyin dogaro da kai wa mata da ‘yan mata a duniya baki daya shi ne taken bukin ranar mata ta duniya a wannan shekarar ta 2025. Bukin na bana na zuwa ne daura da bukin cika shekaru 30 da rattaba hannu kan yarjejeniyar Beijing da dandalin daukar mahimman matakai wadda ita ce yarjejeniyar da ta fara samun karbuwa wajen bangarori da dama har ma ta samar da sauye-sauye masu ma’ana a batun hakkin mata da ‘yan mata.
A shekarar 1995 sadda Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar da taron Mata a karo na hudu kasashe 183 suka rattabawa wannan yarjejenjiyar hannu. Daga cikin abubuwan da wannan yarjejeniyar ta tanadar dai har da fadada irin kariyar da mata ke samu daga dokokin kasa, da ababen more rayuwa irin wadanda mata suka fi bukata, da bai wa matasa damar shiga a dama da su, da ma dai sauya wasu daga cikin batutuwan da suka shafi yanayin zamantakewa musamman wadanda ke da dangantaka da al’adun kaka da kakanni wadanda watakila ba su je daidai da zamani ba.
Najeriya na daga cikin kasashen da suka sanya hannu kan wannan yarjejeniya kuma idan har ana so a ga irin tasiri ko rashin shi a yadda kasar ke gudanar da hidimominta dole ne a duba wasu daga cikin mahimman fannonin da ke alaka da rayuwar mata.
Kan gaba shi ne yanayin zamantakewa da yadda ake kallon mata musamman idan aka yi la’akari da nauyin da al’umma ta rataya a wuyarsu. Blessing Mato wadda babbar ‘yar kasuwa ce mai saida riguna irin na alatu da fafutuka wajen kare hakkin mata da samar musu da rayuwa mai inganci ta ce wasu al’adu da ma kafafen yada labarai ba su yi wa mata adalci saboda yadda ake nuna su.
“Sau da yawa sai a ce dole mace ta zauna a gida ta kula da iyali, a maimakon fita ta yi aiki, me zai hana mace kula da gidanta ta kuma yi sana’a ko aikin da ta ke so? bai kamata a ce wannan ya cigaba da kasancewa mata kalubale ba a wannan zamanin.”
Bacin haka a cewar Mato, akwai alamun cewa a yanayin zamantakewar zamanin yanzu, ana mutunta hakkokin mata ana kuma daraja su fiye da yadda aka sani a baya. Sa’annan kuma abun farin ciki ma shi ne yanzu maza suna taimakawa sosai a gida wanda ke taimakawa mata wajen samun lokacin hutu da kuma yin abubuwan da suke sha’awa. Ba kamar ‘yan shekarun da suka gabata yanzu mata da dama na iya cika bururrukansu na zuwa makaranta, na yin sana’a na shiga siyasa da samun irin ayyukan da ba safai ne ake samun mata suna yi ba a baya. Sai dai kamar ko da yaushe a kan dan sami wasu matsalolin da ke da nasaba da abin da Majelisar Dinkin Duniya ke so ta ga an kawar, kamar rashin daidaito a albashi domin har yanzu albashin maza ya fi na mata yawa, kuma tsoro ko fargabar bakin mutane na “abun da za’a ce” na yawan hana mata yin abubuwan da suke so su yi.

Ilimin ‘ya’ya mata a Najeriya
Fannin ilimi na da mahimmancin gaske, alkaluma na nuna cewa an sami karuwa a yawan ‘ya’ya matan da ke shiga makaranta. To sai dai wannan adadin na nuna yawan mutanen da aka dauka ne yayin shiga ba wai wadanda suka kammala ba ko kuma wadanda ke cigaba da karbar karatun ba, domin adadin kan sauya sosai bayan sun fara karatun saboda kalubalen da mata kan fuskanta.
Hyeladzira Mshelia, shugabar sashen kula da shirye-shirye a kungiyar CODE ta ce suna aiki tare da al’ummomi daban-daban musamman a yankin arewacin Najeriya wajen kula da ‘ya’ya mata wadanda ke da shekaru 12 zuwa sama dan ganin sun sami ilimin boko, sun zauna a makaranta har karshe sa’annan sun kuma sami damar zuwa matakin da ke biye da wanda suke har su kammala jami’a.
To sai dai duk da haka, kungiyarta ta CODE na fuskantar matsaloli ko a wannan gefen duk da cewa akwai kungiyoyi da yawa da ke hada hannu da su wajen aiwatar da wannan aikin.
“Rashin tsaro na kan gaba cikin matsalolin domin akwai matan da zuwa makarantar ke musu wahala saboda tazarar da ya ke da shi daga inda suke zama, sa’annan akwai rashin kudi,” a cewar Mshelia.
Sai dai babbar matsalar ita ce yawacin tallafin da ake kawo wa ba su cika dorewa ba tilas ne kungiyoyin da ke aiki da mata dan tabbatar da ilimi su yi aiki tare wajen ganin cewa matakansu masu dorewa ne ma’ana tun farko a dauki matakan da za su cimma bukatun maza da na mata domin sun banbanta. Sa’annan ya kamata gwamnati ita ma ta jajirce.
“Misali matan da ke zama a wuraren da ke fama da rikici ba wuya sun bar makaranta, dole a zuba jari wajen sanya ababen more rayuwar da za su yi la’akari da matakan kariyar da mata ke bukata. Wata sa’a a irin makarantun da muke zuwa babu ruwa kuma yawanci bayi daya ne, dan haka babu yadda za’a yi mace ta saki jiki ta je bayi musamman sadda ta ke haila. Bacin haka mu kanmu al’ummomi ya kamata mu sanya ido mu tabbatar cewa gwamnati na kashe kudi a wuraren da muke bukata, idan kuma ba ta yi mu nemi yadda za mu bayyana mata,” Mshelia ta ce.
Kungiyoyin kasa da kasar da ke bayar da tallafi ba komai ne za zu iya yi ba, tilas ne gwamnati ta dauki nauyin da ya rataya a wuyarta domin ilimi hakki ne na yara maza da mata ya kamata su sami ilimi cikin sauki kuma idan ba wai gwamnati ta aiwatar da manufofin ilimi yadda ya kamata da ma yawan kudin da ya ke bukata ba, babu sauyin da za’a gani.
Ba adadin matan da suka shiga makaranta ne kadai ake la’akari da shi a fannin ilimin kadai ba, har ma da irin darussan da mata ke dauka shin akwai mata da yawa a darussan kimiya da fasaha saboda su ma su shiga a dama da su a fagen? Chioma Agwuegbo Agwuegbo wadda kungiyarta ta TechHerng ke taimakawa mata wajen samun abun dogaro da kai ta hanyar amfani da sabbin dabaru da fasahohin zamani ta ce kafin a fara maganar irin wadannan darussan dole a duba a ga makarantun.
Ta fadi haka ne domin yawancin makarantun, musamman wadanda ke karkara babu kujerun zama, babu wutar lantarki da ma dai sauran ababen da ake bukata dan karatu da koyarwa cikin walwala. Haka nan kuma malaman ma ba su cika samun albashinsu a kan kari ba, idan ma sun samu ba lallai ne ma a bas u cikakken kudin ba.
Bacin haka su kansu malaman ba su da irin horaswar da ake bukata. Dan haka tun kafin ma a je ga batun banbancin da ke tsakanin ilimin maza da mata a fannin kimiyya da fasaha dole a yi la’akari da cewa babu mafi karancin abin da ake bukata dan samar da irin wannan ilimin a yawancin makarantun da ke kasar.

To ko yaya batun cin zarafin mata wanda ba da dadewar nan ba ya kasancewa mata karfen kafa?
Agwuegbo na daga cikin matan da suka yi tsayin daka wajen sa muryoyinsu a harkokin da suka shafi inganta rayuwar mata musamman yadda ya shafi kare musu hakkokinsu. Dan haka ne ma kungiyarta ta TechHerng ta samar da wata gidauniya ta musamman dan taimakawa wadanda suka raunata sakamakon cin zarafi.
Mai rajin kare hakkin matan ta ce hakan na da mahimmancin gaske domin a ‘yan shekarun baya-bayan nan an ga karuwa a kalaman da ke nuna adawa da kare hakkin mata hasali ma a cikin watanni biyun da suka gabata, akwai kungiyoyin da suka gudanar da bincike kan yawan matan da aka kashe ko kuma suka raunata sosai a hannun mazajensu, kuma adadinsu ya kai 30, wannan kuma adadin na wadanda aka sani ke nan saboda an sa a yanar gizo mai yiwuwa ya fi haka.
To sai dai ba za’a ce babu cigaban baki day aba domin ra’ayinta duk da cewa cin zarafin mata na cigaba da karuwa ana iya cewa an sami cigaba wajen fadakarwa da kuma wayar da kan al’umma a kan cin zarafin mata domin yanzu a kan tattauna batun ana kuma daukar matakai sai dai abun da ya rage shi ne a samu gwamnati ta dauke shi da mahimmanci ta mayar da shi babban laifi ba wai wani abun da ya kamata a rika dauka a matsayin yanayin zamantakewa kawai ba.
Mata a wuraren shugabanci
Ba yarjejeniya Beijing ce kadai Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranci sanya hannu a kai ba dan tabbatar da cigaban mata da ‘yan mata. Ko a shekarar 1979 an sa hannu kan yarjejeniyar CEDAW wadda ta haramta nuna wa mata wariya. Wannan kuma tun a shekarar 1981 kasashen da suka sanya mata hannu suka fara amfani da ita a hukumance.
Da wannan yarjejeniyar dai burin shi ne a cimma daidaito mata ma su shiga a rika damawa da su, sai dai bisa dukkan alamu dai wannan lamarin ya zama tamkar rawar ‘yan mata, wato a yi gaba a yi baya.
“A gani na ba mu kai ko’ina ba idan aka yi la’akari da batun cigaban mata a siyasa da shugabanci saboda akwai matsaloli da dama kamar siyasa a matakin jam’iyyu, akwai rashin kudi, da kuma al’adar fifita maza a kan mata da dai sauransu. Bacin haka akwai fin karfin da aka nunawa mata da ma cin zarafinsu da ake yi,” in ji Mshelia.
Yawan mata a siyasa na cigaba da raguwa, a cewar Agwuegbo wadda ita ma ta amince da nazarin Mshelia, ta na cewa abin takaicinma shi ne akwai kididdigar ma da ke nuna cewa inda Najeriya ta ke yanzu a yawan matan da ke rike da mukaman shugabanci daidai ne da yadda ya kasance a shekarar 1999.
“Muhallin da matan ke aiki ne ma ya fi bayar da takaici, domin ko daya ma kamar ba’a son mata su sami gindin zama, a gani na wannan tambaya ce da ya kamata a yi wa hukumar zabe mai zaman kanta na INEC da ma ‘yan majalisa, domin idan muna da majalisar da ke cike da maza kadai, wadanne irin dokoki ne za’a yi? Babu yadda za’a sami cigaba mai ma’ana.” in ji
Agwuegbo ta kara da cewa kafin mace ma ta ce za ta shiga siyasa, yaya ta gama ta kananan matsalolin da ta kan fuskanta nay au da kullun. Alal misali abu zai faru kuma mace na bukatar lauya, da wuya za ta samu, idan ma ta samu ba za ta iya biyan kudin ba kuma ban da haka abin da ya fi takaici ma shi ne yawancin lauyoyin ba lallai ne su bi musu hakkin su ba sa’annan ba lallai ne su bi tanadin doka ba tunda suna musu Kallon mata masu rauni shi ya sa ma kungiyarta (TechHerng) ke kokarin samar da wata hadakar lauyoyi na sa kai a duka jihohin kasar, wadanda za su iya taimakawa matan da aka ci zarafinsu musamman a yanar gizo.
A cewar Mshelia dai kafin a ce an sami cigaba mai ma’ana sai an ga karuwar mata a wuraren shugabanci inda za su sami dandalin bayyana ra’ayoyinsu tare da bayar da gudunmawa cikin walwala ba tare da tsangwama ko kalubale ba. Domin duk da cewa suna iya kokarinsu, cigaba mai ma’ana shi ne a ga yawan matan da ake zabe ya karu, a kuma ba su dama su fito yi takara a rage yawan maza.
Har yanzu akwai sauran aiki a gaba. Mata uku ne kawai a majalisar dattawan Najeriyar da ke da kujeru 109 wanna ne mafi karanci a nahiyar Afirka. Rigimar da ke faruwa tsakanin shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio da sanatar jihar Kogi Natasha Akpotu-Uduaghan ya nuna cewa duk macen da ta yi yunkurin samun wani mukami na siyasa sai ta yi da gaske idan ba haka ba, tamkar kabari ta haka wa kanta.
Ganin yadda Blessing Mato ke da bajinta sosai a fannin kasuwanci saboda yadda ta ke huldodi a matakin kasa da kasa, ta ce lallai mata sun sami cigaba a wannan fannin to amma babban kalubalen shi ne samun tallafi dan tabbatar da dorewar sana’o’in da suke yi.
Misali a cewarta, “akwai mata da yawa da ke kasuwanci amma samun kudaden gudanarwa na da wahala sosai yawanci na fuskantar matsalar rashin tallafi, sa’annan kuma akwai bukatu masu tsauri wajen karbar rance a banki yayin da wasu kuma ba su da abun jinginarwa dan samun bashi. Yawancin lokuta sai a ga kamar mata da yawa ne suka samu amma kuma idan aka duba da kyau sai ka ga ba mata da yawa suka samu ba.”
Akwai kuma matsalar rashin ilimi na yadda za su yi amfani da kudin su sami riba wanda abu ne da ke da mahimmanci wa duk wanda ke so ya shiga kasuwanci. Ko da shi ke dai duk da haka, akwai hadin kai tsakanin yawancin matan da ke shiga kasuwanci wadanda ke taimakawa juna da shawarwari da kuma hada su da wadanda za su iya taimaka mu su domin hakan ne ya fi dacewa tunda dai kamar yadda Barmani Choge ta ce ne, macen da ba ta da sana’a ….