|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: An yada wani bidiyo da ya nuna an kama wasu mata hudu a matsayin sheda da ke nuna cewa an yi wata sabuwar garkuwa da mutane a garin Kauran Namoda a jihar Zamfara Arewa maso Yammacin Najeriya.

Hukunci: Karya ce. An yada irin bidiyon a baya wanda ya nunawa DUBAWA cewa wannan bidiyo ba sabo ba ne, an yada shi tun a watan Janairu, 2023, shekaru uku kenan gabanin wannan yadawa da aka yi baya-bayan nan.
Cikakken Sako
Wani bidiyo ya sake bayyana a shafukan sada zumanta inda yake nuna mata guda hudu suna zaune suna kira da a kawo masu dauki, wannan bidiyo an yada shi a shafukan X da Instagram da Facebook inda ake da’awar cewa an yi garkuwa da su a baya-bayan a garin Kauran Namoda da ke jihar Zamfara.
Daya daga cikin wallafar an fitar da ita a shafin X na Zuntu Abdulfatah a ranar 20 ga watan Yuni, 2026. An kalli wannan bidiyo sau 16,500 an sake yada shi sau 163.
“Wasu ‘yanta’adda dauke da bindigu an samu rahoto da ya nuna cewa an yi garkuwa da wasu mata a garin Kauran Namoda, na jihar Zamfara lamarin da ke nuna cewa wannan lamarin na kara ta’azzara a wannan yanki,” a cewar wannan shafi.
“Wannan lamarin da ya faru a baya-bayan nan ya sake fito da fargaba da ake ciki a wannan yanki na tabarbarewar tsaro, wannan ya sanya al’umma ke kara kiraye-kiraye cewa jami’an tsaro da gwamnatoci su kara kaimi wajen tunkarar wannan matsalar, inda suke kira a ba da kariya ga fararen hula a dakile ayyukan wadannan ‘yanta’adda.
Iyalan wadanda aka kama sun shiga dimuwa da fatan ganin an sako wadanda aka kama, ganin yadda lamarin tsaron ke kara tabarbarewa.”
A kwai wasu bidiyon irin wannan da aka yada a shafukan na Instagram da Facebook kamar a nan da nan inda dubban mutane suka yi tsokaci.
Wannan bidiyo da aka yada a baya-bayan nan ya ja hankali ganin yadda ake samun ci gaban tabarbarewar tsaro da garkuwa da mutane da ake samu a jihar ta Zamfara.
Tantancewa
DUBAWA ta duba wasu irin wadannan bidiyo da aka yi a baya, dama rahotanni da aka yi, bayan tsakuro wani bangare na wannan bidiyo.
Bincikenmu ya kaimu ga tarin bidiyo da aka wallafa a shafukan YouTube da Facebook da aka yi a 2023.
Daya daga cikin wallafar da aka yi a shafin na YouTube an mata taken “A KALLA: Daliban Zamfara da aka yi garkuwa da su na kira da a kawo masu dauki.”
Wannan bidiyo an wallafa shi bisa alakanta shi da yin garkuwa da mata hudu a jihar Zamfara.
Karin bincike ya gano wasu rahotanni a wasu manyan kafafan yada labarai na kasa wadanda suka wallafa rahoton a watan Yuli da Agusta,2023, wadanda suka yi labari irin wannan a wancan lokaci da bidiyo iri daya.
A rahoto da jaridar Guardian ta wallafa a ranar 4 ga watan Augusta,2023, ta ba da rahoto da ke cewa mata hudu da aka kama watanni bakwai da suka gabata sun bayyana a wani bidiyo mai tsawon mintuna biyu da dakika 19, da masu garkuwa da su suka saki.
Wadannan matan sune Jamila Yahaya Isa da Aisha Yahaya Isa da Ummulkhairi Musa da Ummulkhairi Sani Umar, an kuma yi garkuwa da sune a lokacin da suke kan hanyarsu ta tafiya daga Kaura Namoda zuwa Birnin Magaji Road.
Daga bisani gwamnatin jihar Zamfara ta tabbatar da cewa wadannan mata guda hudu an kubutar da su.
A cewar babban darakta a sashen tsaron ciki na jihar ta Zamfara Nuhu Umar mata guda hudu da aka kama su a ranar 15 ga watan Janairu, 2023 an sako su.
Babban jami’in ya bayyana haka ne a lokaci da yake mika wadannan mata hudu da aka kubutar ga Gwamna Dauda Lawal na jihar ta Zamfara a watan Agusta,2023.
A karshe
Da’awar karya ce, wannan bidiyo da ya yadu a baya-bayan nan cewa an yi garkuwa da mata hudu a kan hanyar Kaura Namoda a jihar Zamfara, tsohon bidiyo ne da aka saki tun a 2023. Matan da aka kama su hudu an kama sune a ranar 15 ga Janairu,2023 kuma tuni aka kubutar da su.
Duk da cewa akwai wasu hare-hare da yin garkuwa da mutane da aka samu a jihar Zamfara babu wata sheda da ta hada wannan labarin bidiyo da ya sake bayyana da halin da ake ciki a baya-bayan nan a jihar.
