Yadda wani bidiyo da aka dauka a Kankara, ya zama abin yada labarin Karya a Kaduna

How viral video, shot in Kankara, became misinformation tool in Kaduna
Getting your Trinity Audio player ready...

Wani bidiyo da aka yi ikirari ya nuna karara yadda ‘yanfashin daji ke siyan abinci da lemo, a wani shago a Kaduna, wannan bidiyo ya yadu a shafin Facebook da sauran shafukan sada zumunta.

Bidiyon ya nunar da cewa masu dauke da makamai na gudanar da ayyukansu kai tsaye ba tare da tsangwama ba, duk da cewa akwai wasu ayyuka da jami’an tsaro ke gudanarwa.

Wannan bidiyo dai ya haddasa cece-kuce, da martani inda da dama masu amfani da shafin suke nuna damuwarsu a dangane da halin da ake ciki ga matsalar ta tsaro, wasu ma na tambaya ko jami’an tsaro za su iya magance wannan matsalar ta ayyukan ta’addanci.

Sai dai binciken DUBAWA ya gano cewa wannan bidiyo ba a Kaduna aka dauke shi ba kamar yadda mai da’awar ke fadi.

Amma matsalar ba ta tsaya ga wajen da aka ce an dau bidiyon ba; batu ne na yaudarar al’umma a sauya masu tunani da sanya masu fargaba, musamman a yankunan da ake cikin halin na tashin hankali.

Yadda bidiyon ya bayyana a shafin intanet da wani taken labarin na daban.

A ranar 18 ga watan Mayu, 2026 wani shafin Facebook mai suna Hausawa ya yada wani bidiyo (da aka alkinta shi a nan) da ya nuna wasu mutane dauke da muggan makamai suna siyan kayan abinci da abin sha a wajen wani mai shago.

An kara wani bayani a dangane da wannan da’awa inda aka ce, lamarin ya faru ne a jihar Kaduna, aka ce masu fashin dajin sun bayyana suna siyen kayayyaki ba tare da wata fargaba ba ta ko za a kama su.

Ya zuwa ranar 27 ga watan Yuni,2026, wannan bidiyo ya ja hankali sosai inda aka samu mutane 47,000 da suka kalla da masu tsokaci 219 da masu nuna sha’awa 524 da masu yadawa 201. 

Bayan nazartar tsokaci da ake yi an sami mabanbantan martani, wasu daga cikin masu amfani da shafin sun nuna amincewarsu da abin da ake fadi game da bidiyon yayin da wasu kuma ke nuna alamar tambaya kan wuri da aka ce lamarin ya faru inda wasu ke cewa an dauki bidiyon ne a jihar Katsina.

Martins Otareh yayi tsokaci da cewa, “ Wadannan na cikin taurari a arewacin Najeriya.”

Yusuf Madami Isa ya nuna ayar tambaya akan wajen da abin ya faru, yana mai tsokaci da cewa ‘’Wannan lokacin shedaniyar yarjejeniyar zaman lafiya da aka yi ne a Katsina ba a Kaduna ba.’’

Mun kuma samu wannan bidiyo a shafin Facebook kamar a wadannan wurare nan da nan da nan, haka nan a shafukan YouTube da Instagram.

DUBAWA da fari ta lura da cewa ana fadin cewa wannan bidiyo ba a Kaduna aka dauke shi ba. Sai dai muryar da ake yawan ji na bayyana ana jin fadin Kankara.

Haka kuma an ga wasu mutanen a bidiyon suna daukar hotuna tare da ‘yanbindar suna fadin cewa, kuna cikin mutanen da muka kulla yarjejeniyar zaman lafiya da su…?”

Daya daga cikin ‘yanbindigar ya ba da amsa da cewa “karamar hukumar Kankara,”a harshen Hausa.

An karkasa bidiyon don gano asalin inda ya fito, sai muka ga an wallafa wannan bidiyo a shafin  Rana24, wata kafar yada labarai da ke gudanar da ayyukanta a garin Kankara.

Yadda wani bidiyo da aka dauka a Kankara, ya zama abin yada labarin Karya a Kaduna

Hoto da aka dauko daga bidiyon. Tushe: Rana24

Wani mai amfani da shafin Facebook Abdulkadir Yusuf, shima ya yada wannan bidiyo kamar yadda ake gani a nan, inda yayi rubutu a kan bidiyon da ya nuna cewa an dauki bidiyon ne a Kankara, kuma wannan ya dauki tsawon watanni kafin bayyanar da’awar da aka danganta da Kaduna.

Mene ne abin da ya faru na hakika?

A wata rana a yanayi na hazo-hazo a yankin Kankara na jihar Katsina, wasu ‘yanbindiga sun shiga gari jim kadan bayan kammala wata yarjejeniyar zaman lafiya, inda wasu daga cikinsu suka shiga wani shago. Wannan wajen bayan wasu watanni aka sake nuna shi da wani labari na daban, aka kuma kai shi wata nahiya.

Wannan hoton bidiyo dai da aka gani an yi shine a lokacin da ake nazartar tattaunawa da gungun ‘yanbindigar a kokari na kulla yarjejeniyar zaman lafiya a shirin dakile yawaitar tashe-tashen hankula da suka dauki tsawon shekaru, suka kuma lalata yanayin rayuwa a yankunan al’umma a yankin na Arewa maso Yammacin Najeriya.

A wancan lokacin wannan bidiyo ya dauki hankali, inda mutane da dama suke ta kokari na ganin sun fahimci wani dalili ya kawo wannan haduwar da ba kasafai ake ganin irinta ba.

Idan za a iya tunawa karamar hukumar ta Kankara ta dauki hankali na al’ummar kasa da kasa a watan Disambar, 2020 a lokacin da aka yi garkuwa da dalibai sama da 300 daga makarantar sakandaren Kankara, Wannan yanayi ya samu tofin Allah Ya tsine daga al’umma ta kasa da kasa, lamarin kuma da ya sake fito da halin tabarbarewar tsaro a yankin na Arewa maso Yammacin Najeriya.

Tun daga wancan lokaci ne al’umma suka ci gaba da fama da matsalar kai hare-hare a kauyuka da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da satar shanu da raba mutane da muhallansu.

Kamar sauran jihohi da ke fama da matsalolin na tsaro, ita ma jihar ta Katsina na duba amfani da karfin soja dama tattaunawar sulhu da ‘yanbindigar a kokari na dakile matsalar ta tsaro da ta addabi al’umma.

Mannir Idris, wani danjarida a jihar ta Katsina wanda ke zaune a karamar hukumar ta Kankara ya bibiyi wannan yarjejeniya ta zaman lafiya inda yace an cimma yarjejeniya 

a ranar 1 ga Satumba, 2025.

Wannan tattaunawa anyi ta ne tsakanin shugabanni na kananan hukumomi da al’ummar gari ba ma da gwamnati a matakin jiha ba ta Katsina, wacce ita ke jaddada cewa bata goyon bayan tattaunawa, sai dai ta bari al’umma su dauki matakan da suka ga sun dace wajen kawo karshen matsalar a yankunansu.

DUBAWA ta gano cewa shagon yana garin Kankara ne (Rufaida Yoghurt & Fura Shop) sannan ta yi magana da ma’aikata da ke a wajen, wani ma’aikaci a wajen da bai so a bayyana sunansa ba saboda gudun abin da ka iya zuwa ya dawo, ya tabbatar da cewa a wajen ne aka yi wannan lamari, kuma ma wasu kayayyakin an dauka ba tare da biyan kudi ba.

“Lamarin ya faru ne a shagonmu da ke Kankara, mun karbi lamarin a matsayin kaddara, ”kamar yadda daya daga cikin masu aiki a kantin ya fadawa DUBAWA.

How viral video, shot in Kankara, became misinformation tool in KadunaHoton shagon na  Rufaida Yoghurt & Fura a Kankara. Tushe: DUBAWA.

Danjarida Mannir ya jaddada cewa bayanan shi da kansa ya tattara bayani a tattaunawa da daga yaron shagon. Mannir ya kara da fadawa DUBAWA cewa an kulla yarjejeniyar zaman lafiya a ranar 1 ga Satumba,2026, bayan wannan rana ce wasu daga cikin ‘yanbindigar suka shiga garin na Kankara don nuna wa al’umma cewa yarjejeniyar zaman lafiyar ta fara aiki.

“Da dama cikin al’umma da suka san wasunsu, sun fito sun gansu haka nan suka yi gaisuwa da wadanda suka sani,” a cewarsa.

Mannir ya bayyana cewa daga baya ya gano cewa ‘yanbindigar sun bar shagon ba tare da biyan kudi ba, inda suka fadawa masu shagon cewa za su dawo washegari su biya kudin tun da dai an kulla yarjejeniyar zaman lafiya.

Washegari a ranar Talata 2 ga Satumba,2026 wacce ta zama ranar kasuwar Kankara, Mannir yace ‘yanbindigar sun sake shiga gari a wannan karo karara ba tare da daukar makamai ba, sai dai wannan yarjejeniyar zaman lafiya ba ta je ko’ina ba kasancewar bayan kwanaki biyu ne kadai sai ta wargaje.

DUBAWA ta kuma yi magana da wasu al’ummar garin na Kankara kamar Muhammad Mannir ya tabbatar da cewa wadannan ‘yanbindigar sun shiga garin bayan kulla yarjejeniyar.

Muhammad ya fada wa DUBAWA cewa duk da cewa baya gurin da aka cimma yarjejeniyar amma mai gidansa yana wajen.Yace daga baya ne ya rika ganin masu dauke da bindigu suna shiga garin na Kankara.

“ A wannan lokaci ne wani ya tambayi hanyar zuwa Shagon Rufaida, daya daga cikin abokaina ya kaisu wajen,” a cewar Muhammad.

A cewar Muhammad, mazauna garin basu yi kaura ba lokacin da suka shiga garin. Wasu sun gaisa da wadannan mutane, da dama mutane sun san su kafin rikicin masu fashin dajin yayi yawa.

Muhammad ya gane daya daga cikin ‘yanbindigar da suka bayyana a bidiyon, wasu bayanan da aka tattara sun kuma fahimci, cewa an tabbatar da cewa an dauke shine a Kankara ba Kaduna ba.

Yace irin wannan bayyana ta ‘yanta’ada da ba a saba gani ba na zuwa bayan zaman lafiya da aka kulla, domin in ba haka ba ba za a ga irin wannan ba. 

Bayanan da aka gano ya nuna cewa bidiyon a karamar hukumar Kankara aka dauke shi ba a jihar Katsina ba, sabanin da’awar cewa ‘yanta’adda sun bayyana a wan i shago a jihar Kaduna. 

Sannan binciken DUBAWA ya gano cewa an dauki wannan bidiyo a Kankara ba a Kaduna ba, tasirin illar wannan bidiyo bai tsaya ga kawo rudani a game da inda aka dauke shi ba. 

Fiye da karya kan inda aka dauki hoton

Nura Kasim, mazaunin Kaduna ya fadawa DUBAWA cewa da fari wannan bidiyo ya haifar da rudani a tsakanin iyalai, yace matarsa ta fara ganin wannan bidiyo inda ta fada masa cewa ga ‘yanbindiga sun shigo garin suna yawo yadda suka ga dama a Kaduna.

“Ina nesa da gida lokacin da matata ta kira ni da ta ga wannan bidiyo, Tun da shi wannan ba a ce ga a inda aka dauki bidiyon ba, sai muka shiga rudani tare da tuntuba wace hanya za mu bi zuwa gida, sai da na yi tunanin ko dai na kwana ne a ofis domin na yi tunanin akwai fargaba kan hanyar da zan bi, a cewar Nura.

Yace daga bisani na turawa abokina bidiyon wanda ya gane cewa ai wannan tsohon bidiyo ne aka sake fito da shi kuma ma ai wannan ba a Kaduna ba ne, a wannan lokaci ne na gane cewa da’awar karya ce, sai muka samu kwanciyar hankali,” a cewarsa.

Sardauna Bello, wani mazaunin garin na Kaduna wanda ke amfani da shafin Facebook, ya fadawa DUBAWA cewa yana tantama ko wannan bidiyo an dauke shi a jihar ta Kaduna, kuma illar da aka yi na danganata bidiyon da malamin addini Ahmad Gumi shi yasa yayi magana a bainar jama’a.

“Matsala ta ita ce an taba malami nane an bata masa suna,” a cewar Sardauna, kamar yadda ya fadawa DUBAWA.

Yadda Sardauna ya nuna illar labaran karya da gangan abin da ke jawo muhawara, wannan ya sanya dole kara zurfafa bincike kan abin da ke zama na karya. Duk da ya nuna tantamarsa kan cewa inda aka yi lamarin ba a Kaduna ba ne, 

Danganta Gumi da batun shima abin takaici ne kasancewar lamari ne da ya shafi tsaro da ke bukatar yin taka tsantsan.

Martanin da yayi ya sake fito da illar labaran karya da yaudara a matsayin lamari babba.

A cewar rahoton 2025 Reuters Institute Digital News kaso 58% na masu tsokaci a Najeriya da masu fada aji a shafukan intanet, su ke zama tushe na labaran karya da yaudara. Wannan ya kasance ja gaba cikin wadanda aka nazarta a tsakanin kasashe.

Yawan masu amfani da kafafan da labaran yaudarar abun lura ne, Bayanai da aka tattara  DataReportal yayi kiyasin cewa kimanin ‘yan Najeriya miliyan 107 ke amfani da intanet, kuma miliyan 38.7 na amfani da shafukan sada zumunta ya zuwa farkon shekarar 2025. 

Duba da wannan ne,  kwararru ke cewa labaran da ba haka suke ba a dangane da tsaro ana masu fassara kala-kala, musamman idan aka samu bidiyo na gaske aka yi masu taken labaru da ke zama mai barazana.

Kwarraru sun yi gargadi kan yada labarai da suka shafi tsaro ba tare da yin bincike ba

Kwararren masanin tsaro Yahuza Getso yace bidiyo da suka shafi tsaro mutane sun fi zakuwa su yada su cikin gaggawa ba tare da bincike ba kan sahihancinsu.

“Mutane da dama da zarar sun samu bayanai nan da nan suke yada su, saboda suna tunanin cewa suna taimaka wa al’umma ne, sai dai cikin rashin sa’a wasu bayanan jita-jita ne, ana yinsu da gangan a yada su don haifar da rudani da fargaba da rashin fahimta,” kamar yadda ya fadawa DUBAWA.

A cewar Yahuza a wasu lokutan ana yada bidiyo da ya shafi tsaro sai ayi masu taken labari na karya, a cewar Yahuza idan aka yada labari da taken na karya kuma irin wannan na rikirkita harkokin tsaro da ma fahimtar matsalar tsaro a tsakanin al’umma.

Matsalar ba kawai yaudarar jama’a ba amma suna kuma kawo rudani kan abin da ya shafi tsaro, don haka kowane bayani musamman kan abin da ya shafi tsaro, yana da kyau a tantance su kafin yada su,” a cewarsa.

“Ba da ma bayanan da ba haka suke ba, na haifar da rudani ga masu iko da jami’an tsaro da kafafan yada labarai da sauran al’umma. Wannan ya sanya kowane bayani musamman kan abin da ya shafi tsaro, ya kamata ayi bincike akansa kafin a yada shi,” a cewar masanin tsaron.

Sai yayi kira ga masu amfani da shafukan sada zumunta su tabbatar da ganin sun tantance labari da tushensa kafin yada shi, sai yayi gargadi da cewa labarin yaudara guda daya zai iya isa ga miliyoyin al’umma cikin mintuna ya kara haifar da rudani da dama ake cikinsa.

Mohammed Babangida, babban mai dauko rahoto a HumAngle Media wanda ke da kwarewa kan rahotanni na rikice-rikice shima yace irin labaran da ake sake yada su na karya suna kawo rudani wajen fahimtar lamuran tsaro.

“Idan aka sake yada bidiyo kai wani farmaki, mutane za su dauka yanzu ne lamarin ya faru, yana iya kawo farmakin ramuwar gayya a cikin al’umma, ya kawo rashin aminta a cikin al’umma da rudani a cikin fahimtar al’umma kan halin da ake ciki da ya shafi tsaro,” kamar yadda Muhammad ya fadawa DUBAWA.  

Muhammad yayi gargadi cewa yada labaran da ba a tantance ba na kawo nakasu ga kokarin jami’an tsaro.

“Yada labarai da suke da alaka da tashin hankali ba tare da tantance su ba tun daga tushe, wannan na kawar da hankali kan halin da ake ciki na gaskiya da kawo rudani da fargaba, su kuma kambama farfaganda ta ‘yanta’adda da masu aikata miyagun laifuka sau tari ba tare da al’umma sun fahimta ba,” a cewarsa.

A karshe

DUBAWA ta gano cewa wannan bidiyo da ya yadu an dauke shine a karamar hukumar Kankara a jihar Katsina ba a jihar Kaduna ba kamar yadda mai da’awar ya nunar.

Yadda aka yi taken labarin a yanayi na yaudara, ya sanya mutane sun rika bawa labarin fassara daban-daban, abin da ke nuna yadda ake dauka bidiyo na gaskiya a sauya masa take don yada labarin karya da sake sanya al’umma cikin fargaba da rudani kan abin da ya shafi matsalar tsaro.

“Wannan aiki an aiwatar da shi  karkashin Cibiyar Koyon Aikin Jarida da Kirkire-Kirkire da Ci-gaba (CJID) da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai ta EU.”