
Da’awa: An yada wani bidiyo a kafafen sada zumunta da ke nuna wani mutum yana dukan mabarata tsofaffi mata da yara, inda ake ikirarin cewa mutanen Arewa ne da ke zaune a Kudancin Najeriya.

Hukunci: Ƙarya ce. Rahotanni daga kafafen yada labarai na Ghana sun tabbatar da cewa lamarin ya faru ne a Kwame Nkrumah Circle Interchange da ke Accra, kuma binciken DUBAWA ta hanyar Google Maps ya tabbatar da wurin ne.
Cikakken bayani
An yada wani bidiyo mai ban tausayi a kafafen sada zumunta wanda yake nuna wani mutum yana dukan tsofaffi mata da yara ƙanana da bulala wadanda ake ganin mabarata ne.
Bidiyon, wanda aka dauka a ƙarƙashin gada, ya nuna yadda mutumin ke bibiya yana dukan mata sanye hijabi yayin da suke gudu don tsira.
A cikin bidiyon, wani muryar namiji da ke magana da Hausa yana nuna takaici da ɓacin rai, yana cewa ana tozarta ‘yan Arewa da ke neman taimako a Kudancin Najeriya.
“Yanzu an fara yi wa mutanen Arewa bulala a Kudu kenan?” Wannan shine rubutun da Sharif Almuhajir, wani malamin jami’a, ya saka lokacin da ya yada bidiyon.
Zuwa ranar 3 ga Nuwamba, 2025, an kalli bidiyon fiye da sau 98,000, an yi sharhi 1,200, da yadawa sau 799, abin da ya janyo da cece-kuce a tsakanin ‘yan Najeriya da dama, musamman masu zaton cewa lamarin ya faru ne a Kudancin ƙasar.
Wasu sun nuna fushi da takaici, yayin da wasu suka nemi a tabbatar da gaskiyar lamarin kafin daukar wani mataki.
Wata mai suna Rahma Abdulmajid ta rubuta cewa, “wannan ba sai a Kudu ba, har a Arewa da ma kasashe makwabta haka muke fuskanta.”
Shi kuwa Adam Bin Daud Abdullah ya ce, “wannan ba a Najeriya aka dauka ba malam, amma sakonka ya fito fili. Ina fatan shugabanninmu za su dauki mataki don kare jama’a.”
DUBAWA ta gudanar da bincike saboda irin wannan labari na iya haifar da rikici da rarrabuwar kawuna tsakanin Arewa da Kudu idan ba a fayyace gaskiya ba.
Tantancewa
DUBAWA ta yi amfani da manhara binciken bidiyo ta InVid don nazarin muhimman sassan bidiyon. Mun gano motocin haya masu launin rawaya da fari kamar irin wadanda ake amfani da su a birnin Accra, Ghana.
Haka kuma an lura da launin fentin gadar wanda yake kama da tutar kasar Ghana.

Hoton motocin haya masu launin rawaya da fari da aka gani a bidiyon, irin wadanda ake amfani da su a Accra, Ghana.

Hoton fentin gadar da ya yi kama da tutar Ghana.
DUBAWA ta gudanar da bincike ta kalmomin labarin, inda ta gano rahotanni daga GhanaWeb da GHpage wadanda suka wallafa labarin.
A cewar rahoton GhanaWeb, bidiyon yana nuna wani mutumin Ghana a wurin Kwame Nkrumah Circle Interchange da ke Accra yana amfani da bel don dukan masu bara, akasari tsofaffi mata da yara.
Rahoton ya bayyana cewa lamarin ya faru ne bayan mutane sun koka kan yawaitar masu bara a yankin, wanda hukumomin kasar suka bayyana a matsayin barazana ga tsafta da tsaro.
Shafin GHpage ma ya ruwaito cewa ‘yan Ghana da dama sun bukaci a kama mutumin saboda irin “cin mutunci da zalunci” da ya aikata a bidiyon.
Ba wani rahoton da ya danganta lamarin da Najeriya ko da ‘yan Najeriya.
Domin tabbatar da ainihin wurin, DUBAWA ta duba Kwame Nkrumah Circle Interchange da ke Accra a Google Maps ta kuma kwatanta shi da hotunan bidiyon.

Hoton kwatancen tsakanin bidiyon da hoton Google Maps.
A Karshe
Bidiyon da ake yadawa da ke nuna wani mutum yana duka masu bara ba a Najeriya aka dauka ba.
Yaya sabuwar dokar haraji ta shafe al’uma? Ga abubuwa biyar da ya kamata ku sani
#Anambra2025: Yadda masu jefa kuri’a za su iya kaucewa bayanan karya a rumfunan zabe
Sahara Reporters ta yi da’awar cewa Wike ya kauracewa taron majalisar koli wanda karya ce
Babu sheda cewa Zamafara ta tura Askarawa 500 don yakar ‘yanfashin daji su kadai