Mai amfani da shafin Facebook ya wallafa wani hoton da aka gyara ya na da’awar wai wani mutun mai kai biyu ya iso Najeriya

Da’awa: Mai amfani da Facebook, na da’awar wai wani mutumi mai kawuna biyu ya iso Najeriya.

Mai amfani da shafin Facebook ya wallafa wani hoton da aka gyara ya na da’awar wai wani mutun mai kai biyu ya iso Najeriya

Hukunci: Yaudara. Hujjojin da muka samu sun nuna cewa wani hoton aka yi wa hikima ya fito kamar mutun na da kai biyu kuma aiki ne na wani mai suna Onilogbo Hakeem wanda ya yi wa wani fim da ake kira Anikulapo Series, Rise of the Spectre.

Ciakken bayani

Najeriya na da al’adu masu kayatarwa da kuma masu basira sosai a tsakanin ‘yan kasar. Ana iya ganin basira a yadda ‘yan adam ke iya bayyana abubuwan da suke ji, iliminsu da ra’ayoyi. Wata sa’a ana amfani da shi a fina-finai.

Ranar 6 ga watan Maris 2024, wani mai amfani da shafin Facebook mai suna Very Dark Man, ya wallafa wani hoton na wani mutumi mai kawuna biyu da bayanin cewa wai ya iso Najeriya.

Mai amfani da shafin Facebook ya wallafa wani hoton da aka gyara ya na da’awar wai wani mutun mai kai biyu ya iso Najeriya

Hoton da Very Dark Man ya wallafa a shafinsa

Da muka duba shaffin da hoton da ke kai, mun kula cewa ba shi da mabiya sosai.

“See Gobe! Wani mutumi mai kai biyu ya iso Naija. Abun mamaki bai taba kare wa, yanzu an gano mutun mai kawuna biyu a Najeriya. Wasu sun ce wani bangare ne na fim aka tsakuro, amma ba mu san gaskiya ba. Wannan labarin ya riga ya bazu. Za mu cigaba da fadakar da ku kan abubuwan da ke faruwa yayin da muke cigaba da samun karin bayani. Bidiyo a shafi na,” ya ce.

Wannan labarin ya sami alamar likes fiye da 998, an yi tsokaci 416 an kuma raba sau 118.

Yayin da wasu basu yarda da batun ba, wasu suna tunanin gaskiya ne. Mislai Patience Peter cewa ta yi: Abun da na ke gani a India ya iso Najeriya. God abeg oo.” abun da ke nuna cewa ta yarda da labarin.

Wata kuma Phina Ebi cewa ta yi: ” ‘yan biyun da ke hade?”

Ganin yadda da yawa daga cikin wadanda suka karanta labarin suka gaskata da shi, DUBAWA ta dauki nauyin tantance gaskiya dan a guji shiga wani yanayi na rudani.

Tantancewa

Binciken DUBAWA ya bayyana mana cewa wannan aiki ne na wani kwararre wanda ya iya shirya ‘yan wasa su fito a duk siffar da ake so, sunan mutumin Onilogbo Hakeem Effect. Shi da kansa ma ya wallafa hoton a shafin shi na Facebook ranar 5 ga watan Maris na shekarar 2024, da wani bidiyo kuma a shafinsa na Instagram. Inda ya dauki bidiyon ya yi kama da inda ake daukar fina-finai, kuma a wurin tsokaci Hakeem Effect ya yi bayanin cewa aiki ne ua uo wa darektan fina-finai Kunle Afolayan wa fim dinsa na Anikulapo.

“Fim din Anikulapo, idan za ku iya tunanin duk wani abun da ba zai iya faruwa ba @hakeemeffect zai san yadda ya yi ya ga ya tabbata, godiya ga Kunle Afo saboda irin basirar da ya nuna,” kadan daga cikin tsokacin da aka sanya a jikin bidiyon ya bayyana.

Hakeem Effects [Hakeem Onilogbo Ajibola] ya na daga cikinmasu yi wa taurarin Nollywood kwalliya da zane-zane irin wadanda ke amfani da dabaru na musamman. Shi ne kuma shugaban kamfanin  “Trick International,” kamfanin da ke kerawa da siffanta duk wani abun da ake bukata wajen yin fina-finai a masana’antar Nollywood. Ya yi aiki a kan fina-finai irin su Omo ghetto, King of Boys, da Sagaf. Daya daga cikin wadanda ya ke yi kwanan nan shi ne Anikulapo.

“Anikulapo: Rise of the Spectre” Fim ne wanda ke da kashi shida wanda aka kirkiro a matsayin cigaban ainihin fim din “Anikulapo” wanda aka yi a shekarar 2022 wanda ya sami karbuwa sosai a karkashin jagora kuma furodusa Kunle Afolayan. An fara ganin fim din ne a shafin Netflix ranar daya ga watan Maris a kasashe sama da 190 a duniya.

A Karshe

Hotunan da aka wallafa ba na wani mutumi mai kai biyu da ya iso Najeriya ba ne. Aiki ne kawai na zane-zane da kir-kire kir-kiren suffofi na wasanni wadanda aka yi amfani da su dan yin wani dan wasa wanda zai fito a shirin Anikulapo Series. Dan haka wannan zargin Yaudara ce kawai. 

Wanda ya yi wannan binciken ya yi shi ne a karkashin shirin horas da masu binciken gaskiya na DUBAWA 2024 a shirin Kwame KariKari, tare da hadin gwiwar Olufisoye Adenitan daga tashar FRCN positive FM da ke Akure jihar Ondon Najeriya dan wanzar da “gaskiya” a aikin jarida da habbaka fahimtar kafofin yada labarai a kasar.

Exit mobile version