Site icon Dubawa

Shin Namijin Goro Da Tom Tom Na Karawa Namiji Kuzari A Yayin Mu’amalar Aure?

Hoton namijin goro da alawar Tom Tom

Hoton namijin goro da alawar Tom Tom

Da’awa: Hada Namijin Goro da Tom-Tom na karawa namiji karfin kuzari a lokacin saduwa.

Shin Namijin Goro Da Tom Tom Na Karawa Namiji Kuzari A Yayin Mu'amalar Aure?

Hukunci: Yaudara ce! Babu wata hujja dake nuna cewa hada namijin goro da tom-tom na kara karfin kuzari a lokacin saduwa, sai dai namijin goro kadai na karawa dan adam garkuwar jiki.

Cikakken Bayani

Namijin goro ‘ya’an itace ne kamar goro wanda aka fi sani, ba abinci ne wanda ake ci yau da kullum ba, ana cinsa ne saboda nishadi, a wurin biki ko suna da sauransu. Akwai wasu mutane da ke cin sa domin wasu dalilai na lafiya yayinda wasu ke cin sa shi kadai ko a hada shi da tom tom ko dabino da nufin ya taimaka musu da karin kuzari wajen gamsar da iyalansu a yayin mu’amalar aure.

Kamar yadda wani magidanci ya shaida mana cewa yayi amfani da wannan hadin na namijin goro da tom-tom kuma yayi masa aiki, “A da bana daukar lokaci wajen saduwa da iyalina kuma hakan yana damu na, sai na samu labarin wannan hadin daga wani aboki na”

Daman dai ana hada namijin goro da tom-tom ne ta hanyar daura ruwa akan wuta su yi zafi, sannan sai a saka tom-tom a ciki bayan ya narke sai a daddaka namijin goro har sai ya zama kamar gari sannan a zuba shi a cikin ruwan zafi wadanda ke tafasa, bayan sun jima suna tafasa sai a sauke a zuba ruwan a sha. Haka kuma wasu na amfani da namijin goro da dabino ta hanyar tauna su a tare.

Ganin yadda wannan ya zama dabi’a ga wasu mazaje magidanta a Najeriya, Dubawa ta yi bincike domin sanin abinda bincike ya bayyana da kuma ra’ayin kwararru game da hadin namijin goro da kuma tom-tom.

Tantancewa

A yayin tantancewa, mun gano wani bincike da shafin nan na WebMD dake wallafa batutuwan da suka shafi lafiya, sun bayyana cewa namijin goro yana da amfani ga lafiya kuma har yanzu masana na ci gaba da bincike game da wannan itace. 

Daga cikin abubuwan da binciken farko-farko ya nuna cewa yana magani cututtuka da suka hada da kumburin jiki, da cutar mura, ko hanta har da wani nau’in cutar suga. 

Masana da kwararru a fannin lafiya sun kara jaddada cewa namijin goro yana da alfanu sosai ga lafiyar mutum kuma har ma yafi ainahin goro wanda aka fi sani amfani ga lafiya.

Mun tuntubi Bala Gandanga na asibitin jami’ar Usmanu Danfodio wanda ya bayyana cewa “akwai lokutan da su kan su likitoci kan umurci maras lafiya da ya ci namijin goro domin yaji sauki kamar wadanda jikinsu ya kumbure” kasancewar bincike ya tabbatar da amfanin sa.

Ya kara da cewa namijin goro yana kara karfin garkuwar jiki, wannan zai iya zama dalilin da yasa idan wasu mazaje suka ci zasu ji sun samu kuzari a lokacin saduwa da iyali.

Sai dai Bala Gadanga ya yi gargadin cewa, masu hada goron da tom-tom ko wani abu domin cimma wata manufa suna yi ne bisa radin kan su, domin ba wani bincike da ya tabbatar da cewa hakan na da wani alfanu ga lafiyar su.

“Idan ma mutum na cin wannan namijin goro akai-akai zai iya jawo masa matsala, ko kuma ya zama jikin sa ya saba da namijin goron dole sai ya ci gaba da cin sa domin samun gamsuwa ga abinda yake nema,” inji Kwararre.

Hakama kafar yada labarai ta BBC Hausa ta tattauna da wani kwararren likitan abinci a Najeriya Dakta Auwal Musa Umar wanda ya ce bisa dukkan bincike da aka yi babu wata hujja da ke nuna cewa namijin goron na taimaka wa ƙarfin namiji, ko ƙarfin sha’awarsa.

Likitan ya ce duk da cewa idan aka yi amfani da shi ta hanyar da ta dace yana taimaka wa lafiyar jiki, bincike ya tabbatar da cewa daɗewa ana ta’ammali da namijin goro ba ta hanyar da ta dace ba, kan haifar da matsalar rage ƙarfin ƙwayoyin halitta na haihuwa ga maza, lamarin da ka iya janyo wa namiji matsalar rashin haihuwa.

A Karshe

Babu tabbacin cewa hada namijin goro da tom-tom na kara karfin kuzari a lokacin saduwa, sai dai namijin goro kadai na karawa dan adam garkuwar jiki, saboda haka Yaudara ce! 

An yi wannan binciken ne karkashin shirin Binciken Gaskiya na DUBAWA wato Indigenous Language Fact-Checking 2024, tare da hadin gwiwar Vision 92.5FM, Sokoto, domin dabbaka labarun “gaskiya” a cikin aikin jarida da karfafa ilimin yada labarai.

Exit mobile version