|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Mrmess TV a shafin su na Facebook sun wallafa bidiyon dake nuna cewa an gudanar da zanga-zangar nuna adawa da ayyukan ‘yan sanda a jihar Katsina
Hukunci: Karya ce. DUBAWA ta gano cewa bidiyon an dauke shi ne a karamar hukumar Zurmi dake jihar Zamfara sannan ya yi tsawon makonni yana kareda yanar gizo.
Cikakken Labari
A ranar 7 ga Yuli 2026 MrmessTV a shafin su na Facebook sun wallafa bidiyo dake nuna zanga-zangan da mutane a wani kauye a jihar Katsina suka gudanar.
A bidiyo muryar wani ya bayyana cewa “Hakan na faruwa ne a wani kauye dake jihar Katsina. Mutane sun bayyana rashin bukatan ‘yan sanda a kauyen su. Mutanen sun ce ‘yan sanda na sa ido mahara ‘yan bindiga na kawo musu hari.
Amma tambayan shine me ake so ‘yan sandan su yi…?”
A ranar 9 ga Yuli 2026 wannan da’awa ya samu masu dubawa 2,400 da masu kara wallafawa uku. An ga bidiyon a nan,nan,nan da Instagram dake nuni da da’awa irin haka.
A dalilin haka DUBAWA ta gudanar da bincike domin tattance bidiyon musamman yadda Labaran tsaro a Arewacin Najeriya ke yaduwa.
Tantancewa
DUBAWA a binciken da ta gudanar ta dauki wasu fannin bidiyon inda ta yi amfani da matakin gudanar da bincike ‘Reverse Image Search’ domin tabbatar da inda aka fara saka bidiyon.
Sakamakon binciken ya tabbatar cewa bidiyon ya yi tsawon makonni hudu yana kareda yanar gizo kafin MrmessTV ta kara wallafa shi.
An kuma gano bidiyon a Instagram nan, nan da nan a ranar 10 ga Yuni 2026 da da’awar dake nuni da cewa zanga-zangan ya gudana a Zurmi jihar Zamfara.
Tanttance bidiyon ya nuna shedar wurin da zanga-zangan ya gudana a matsayin “Ofishin ‘yan sanda Zurmi”.
DUBAWA ta tabbatar cewa Zurmi karamar hukumar ce a jihar Zamfara ba a jihar Katsina ba. Karamar Hukumar ta yi shekaru da dama tana fama da hare-haren mahara da suka hada da garkuwa da mutane da biyan diyya.
An kuma gano cewa mutanen da suka gudanar da zanga-zangan na Hausa irin ta Zamfarawa.
Sakamakon ya kara nuna cewa mazauna karamar hukumar Zurmi sun gudanar da zanga-zangan ranar 8 ga Yuni 2026 saboda rashin tsaron da suke fama da shi.
Zagazola ya bada rahotan zanga-zangan inda ya nuna cewa rundunar sojin Najeriya dake aiki a karkashin rundunar ‘1Brigade’ ne aika aika wurin domin kwantar da hankin mutane bayan zanga-zangan ya gudana.
Wani shafi a Instagram “politics _hunter” ya tabbatar cewa zanga-zangan ya gudana a Zurmi.
DUBAWA ba ta samu tabbataciyyar bayanai daga rundunar tsaron jihar Katsina ba musamman daga wajen jami’in hulda da jama’a na rundunar DSP AA. Sadik ba wanda zai iya tabbatar cewa bidiyon zanga-zangan ya faru a jihar Katsina ba.
A Karshe
Hujojjin da aka samu sun nuna cewa bidiyon an dauke shi ne a Zurmi jihar Zamfara sa’annan ya dade a yanar gizo kafin MrmessTV ya wallafa a matsayin zanga-zangar da akayi a jihar Katsina. A dalilin haka wannan da’awa karya ne.
