Site icon Dubawa

Yaudara ce! Bidiyon da ya shuhura na nuna dakarun Somaliya ne ba ‘yan bindiga a Najeriya ba

Misleading! Viral video shows Somali security forces, not Nigerian bandits

Da’awa:  Mai amfani da shafin TikTok  ya wallafa  bidiyon da ke nuna wasu mutanen da suka yi dammara cikin wani jirgi, ya na da’awar wai ‘yan bindigan Najeriya ne suke tafiya a jirgin sama.

Yaudara ce! Bidiyon da ya shuhura na nuna dakarun Somaliya ne ba ‘yan bindiga a Najeriya ba

Hukunci: Yaudara ce. Hujjojin da mu ka samu sun nuna cewa dakarun sojojin Somaliya ne a cikin jirgin.

Cikakken bayani

Ranar 4 ga watan Yunin 2026,  mai amfani da shafin TikTok “officialaa_nova” ya wallafa wani bidiyo (da aka sa a nan)  a shafin TikTok da da’awar cewa ‘yan bindiga ne a Najeriya ke tafiya a cikin jirgin sama.

A cikin bidiyon wanda ya wallafa da bayaninsa a matsayin sautin bidiyon, mawallafin ya yi da’awar cewa dan bindigan da ke gaban jirgin ya na bayanin yadda ‘yan bindigan suke hawa jirgin ya kuma tambayi filin jirgin da suke amfani da shi.

Har wa yau, bidiyon ya sake bayyana cikin wasu shafukan sada zumuntar wadanda suka haka da TikTok, Facebook, Instagram, da X.

Mun kuma sake gano wata da’awar a shafin Facebook a nan. 

A cikin bidiyon ana iya ganin wasu maza cikin kayan soja suna zaune a cikin jirgin, tare da da’awar cewa ‘yan bindiga ne ke amfani da jirgin Najeriya wajen gudanar da harkokin sufurinsu.

Daga ranar 9 ga watan Yunin 2026 an kalli bidiyon har sau 235,400 ya sami alamar like sama da 6,645, an yi tsokaci sama da 347 sa’anan masu rabawa sun raba shi sau 1,559. Bidiyon ya dauki hankali sosai a kafofin sada zumunta, inda yawanci suka bayyana damuwarsu dangane matsalar tsaron da ta addabi kasar yayin da wasu kuma suka nuna shakkunsu dangane da sahihancin bidiyon da ma da’awar kanta.

Daya daga cikin masu tsokacin Hajia cewa ta yi, “Na rantse shugaban kasa na sane da duk wadannan abubuwan.” Yayin wani shi ma wani mai suna Muyiwa goyon bayan Hajiar ya yi yana cewa “Ko ke ma ki tambayi kan ki mana.”

To sai dai Mohammed Abdullahi, bai amince baki daya ba tun da shi cewa ya yi,  “Ku tsaya! Wannan labarin bogi ne(Fake news).”

Tasirin da labari irin wannan zai iya yi kan tsaro ne ya sa DUBAWA yanke hukuncin tantance sahihancin labarin.

Tantancewa

DUBAWA ta fara da cire mahimman hotuna a cikin bidiyon dan tantance su cikin manhajar tantance bayanai. Sakamakon da aka samu ya danganta bidiyon da wani bayanin da aka taba wallafawa kan dakaru da jami’an tsaron Somaliya a maimakon kungiyoyin ‘yan bindigan da ke aiki a Najeriya.

Binciken da muka cigaba da gudanarwa duk sun nuna Somaliya ne da farko. Mun fara da rubutun da aka yi a bidiyon da muka tantance shi ne aka fara  dorawa ranar 24ga watan Yulin 2025, wanda muka ga cewa cikin harshen Somali aka rubuta. Shafin da ya wallafa bidiyon shafi ne na wani mai suna  “Abdifatah Mohamud,” wanda suna ne na ainihin dan Somaliya. 

Yaudara ce! Bidiyon da ya shuhura na nuna dakarun Somaliya ne ba ‘yan bindiga a Najeriya ba
Yaudara ce! Bidiyon da ya shuhura na nuna dakarun Somaliya ne ba ‘yan bindiga a Najeriya ba

Hotunan da muka dauka daga bidiyon  Abdifatah Mohamud da bayanin a rubuce cikin harshen Somaliya da fassara a cikin turanci.

Daya daga cikin mazan da za’a iya gani cikin jirgin yana sanye da kayan yaki da ke da wani tambari mai launin ruwan bula da farar tauraruwa kamar dai yadda ya ke a tutar kasar Somaliya.

Yaudara ce! Bidiyon da ya shuhura na nuna dakarun Somaliya ne ba ‘yan bindiga a Najeriya ba

Daya daga cikin dakarun yana sanye da rigar yaki da abaji mai ruwan bula da farar tauraruwa. Asalin hoton: daga shafin officialaa_nova video

Mun sake daukar hotuna daga cikin bidiyon wadanda suka nuna maza da dama a cikin kayan soja kuma kayan sun yi daidai da irin kayan da sojoji ke sanyawa a hukumance, ba su yi shiga irin wanda aka saba gani wajen kungiyoyin ‘yan ta’adda ko masu aikata miyagun laifuka ba.

Sakamakon binciken hotunan da muka yi da manhajar Reverse-image search su ma sun nuna mana cewa mutanen da ke cikin bidiyon dakarun sojin Somaliya ne kuma ma ya danganta bidiyon da wadanda muka fara gani a yanar gizon kamar yadda za ku iya gani a  nan da  nan.

Har wa yau DUBAWA ta sami hujjojin da suka ba ta tabbacin cewa wannan bidiyon ba shi da wata alaka da ‘yan bindiga a Najeriya da ma kowani irin abun da ke da nasaba da tsaron da ya afku a Najeriya.

A Karshe

Wannan bidiyon ba na ‘yan bindiga a Najeriya ba ne sojojin kasar Somaliya ne a cikin jirginsu suna bakin aiki.

“Cibiyar Habbakawa da Koyon Sabbin Dabarun Aikin Jarida (CJID) ke aiwatar da wannan horaswar ta musamman tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.”

Exit mobile version