|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Mai amfani da shafin TikTok ya wallafa bidiyon da ke nuna wasu mutanen da suka yi dammara cikin wani jirgi, ya na da’awar wai ‘yan bindigan Najeriya ne suke tafiya a jirgin sama.

Hukunci: Yaudara ce. Hujjojin da mu ka samu sun nuna cewa dakarun sojojin Somaliya ne a cikin jirgin.
Cikakken bayani
Ranar 4 ga watan Yunin 2026, mai amfani da shafin TikTok “officialaa_nova” ya wallafa wani bidiyo (da aka sa a nan) a shafin TikTok da da’awar cewa ‘yan bindiga ne a Najeriya ke tafiya a cikin jirgin sama.
A cikin bidiyon wanda ya wallafa da bayaninsa a matsayin sautin bidiyon, mawallafin ya yi da’awar cewa dan bindigan da ke gaban jirgin ya na bayanin yadda ‘yan bindigan suke hawa jirgin ya kuma tambayi filin jirgin da suke amfani da shi.
Har wa yau, bidiyon ya sake bayyana cikin wasu shafukan sada zumuntar wadanda suka haka da TikTok, Facebook, Instagram, da X.
Mun kuma sake gano wata da’awar a shafin Facebook a nan.
A cikin bidiyon ana iya ganin wasu maza cikin kayan soja suna zaune a cikin jirgin, tare da da’awar cewa ‘yan bindiga ne ke amfani da jirgin Najeriya wajen gudanar da harkokin sufurinsu.
Daga ranar 9 ga watan Yunin 2026 an kalli bidiyon har sau 235,400 ya sami alamar like sama da 6,645, an yi tsokaci sama da 347 sa’anan masu rabawa sun raba shi sau 1,559. Bidiyon ya dauki hankali sosai a kafofin sada zumunta, inda yawanci suka bayyana damuwarsu dangane matsalar tsaron da ta addabi kasar yayin da wasu kuma suka nuna shakkunsu dangane da sahihancin bidiyon da ma da’awar kanta.
Daya daga cikin masu tsokacin Hajia cewa ta yi, “Na rantse shugaban kasa na sane da duk wadannan abubuwan.” Yayin wani shi ma wani mai suna Muyiwa goyon bayan Hajiar ya yi yana cewa “Ko ke ma ki tambayi kan ki mana.”
To sai dai Mohammed Abdullahi, bai amince baki daya ba tun da shi cewa ya yi, “Ku tsaya! Wannan labarin bogi ne(Fake news).”
Tasirin da labari irin wannan zai iya yi kan tsaro ne ya sa DUBAWA yanke hukuncin tantance sahihancin labarin.
Tantancewa
DUBAWA ta fara da cire mahimman hotuna a cikin bidiyon dan tantance su cikin manhajar tantance bayanai. Sakamakon da aka samu ya danganta bidiyon da wani bayanin da aka taba wallafawa kan dakaru da jami’an tsaron Somaliya a maimakon kungiyoyin ‘yan bindigan da ke aiki a Najeriya.
Binciken da muka cigaba da gudanarwa duk sun nuna Somaliya ne da farko. Mun fara da rubutun da aka yi a bidiyon da muka tantance shi ne aka fara dorawa ranar 24ga watan Yulin 2025, wanda muka ga cewa cikin harshen Somali aka rubuta. Shafin da ya wallafa bidiyon shafi ne na wani mai suna “Abdifatah Mohamud,” wanda suna ne na ainihin dan Somaliya.


Hotunan da muka dauka daga bidiyon Abdifatah Mohamud da bayanin a rubuce cikin harshen Somaliya da fassara a cikin turanci.
Daya daga cikin mazan da za’a iya gani cikin jirgin yana sanye da kayan yaki da ke da wani tambari mai launin ruwan bula da farar tauraruwa kamar dai yadda ya ke a tutar kasar Somaliya.

Daya daga cikin dakarun yana sanye da rigar yaki da abaji mai ruwan bula da farar tauraruwa. Asalin hoton: daga shafin officialaa_nova video
Mun sake daukar hotuna daga cikin bidiyon wadanda suka nuna maza da dama a cikin kayan soja kuma kayan sun yi daidai da irin kayan da sojoji ke sanyawa a hukumance, ba su yi shiga irin wanda aka saba gani wajen kungiyoyin ‘yan ta’adda ko masu aikata miyagun laifuka ba.
Sakamakon binciken hotunan da muka yi da manhajar Reverse-image search su ma sun nuna mana cewa mutanen da ke cikin bidiyon dakarun sojin Somaliya ne kuma ma ya danganta bidiyon da wadanda muka fara gani a yanar gizon kamar yadda za ku iya gani a nan da nan.
Har wa yau DUBAWA ta sami hujjojin da suka ba ta tabbacin cewa wannan bidiyon ba shi da wata alaka da ‘yan bindiga a Najeriya da ma kowani irin abun da ke da nasaba da tsaron da ya afku a Najeriya.
A Karshe
Wannan bidiyon ba na ‘yan bindiga a Najeriya ba ne sojojin kasar Somaliya ne a cikin jirginsu suna bakin aiki.
“Cibiyar Habbakawa da Koyon Sabbin Dabarun Aikin Jarida (CJID) ke aiwatar da wannan horaswar ta musamman tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.”

NIGERIA CUSTOMS HAS BEGINS ONLINE AUCTIONING OF SEIZED VEHICLES
Toyota Land Cruiser-N1.3m
•Toyota Prado N1.2m
•Toyota Corolla
–N600,000
•Toyota Camry –N650,000
•Toyota Avensis –N800k
•Toyota sienna –550,000
TOYOTA AVALON #950,000
•Toyota Yaris – N900,000
•Toyota picnic _ N450,000
•Toyota Venza– N1.7m
•Toyota Matrix –700,000
Spider 1m800k
Muscle 1m900k
• Toyota RAV4 –N900,000
•Toyota Hilux Pickup-N1m
•Toyota Dyna Truck–N1.3million
•Toyota 4 Runner–N1m
tundra 2.670,000
tacoma 2.5Million
•Toyota Hiace Bus –N1.5m
•Toyota Highlander-N1.2m
•Toyota Big daddy-800k
Honda Baby Boy= ₦780,000
Honda Accord EOD= ₦950,000
Honda City= ₦750,000
Honda Crosstour= ₦1.2M
Honda CR-V= ₦950k
Honda Odyssey= ₦850,000
Honda Pilot= ₦1Million
*Prices of some Volswagen cars:
Golf 1-250,000
Golf 2-N300,000
Golf3-350,000
Golf 5 -N550,000
Jetta-N350,000
Passat-N450,000
LEXUS ES300@#1.3 MILLION
LEXUS ES330@#1.6 MILLION
LEXUS ES350@#2 MILLION
LEXUS RX300@#1.7 MILLION
LEXUS RX330@#3 MILLION
LEXUS RX350@#4 MILLION
LEXUS RX400@#3.5 MILLION
LEXUS GX460@#4 MILLION
LEXUS GX470@#5 MILLIONLexus GX460=₦6.6M
Lexus GX470=₦8.4M
Lexus GX570=₦13.8M
Lexus IS-250=₦2.1M
Lexus ES-330=₦1.5M
Lexus ES-350=₦2.6M
Lexus RX300= ₦1.5M
Lexus RX330= ₦2.8M
Lexus RX350= ₦3.2M. BENZ C-CLASS ₦3,000,000
MERCEDES-BENZ E-Class ₦3,500,000
MERCEDES-BENZ G-Class ₦4,000,000
MERCEDES-BENZ GLK ₦4,500,000
MERCEDES BENZ ML₦5,000,000Mercedes-Benz C-Class 2minterested=”” buyer=”” should=”” kindly=”” contact=”” officer=”” Gabriel =”” .=”” for=”” more=”” information=”” {+2348o=”” 6739=”” 9090=”” }=””>