Site icon Dubawa

Yaudara ce! Wani bidiyon mutane dauke da bindigogi tare da sojoji a yanayi na komai kalau, abin da ake fada a kansa ba haka ba ne

Misleading! Viral video of armed men with troops taken out of context

Da’awa:Wani mai amfani da shafin X ya yada wani bidiyo dauke da hoton sojoji da ‘yan sanda suna tare da ‘yan bindiga a yanayi na kamar akwai fahimtar juna.

Yaudara ce! Wani bidiyon mutane dauke da bindigogi tare da sojoji a yanayi na komai kalau, abin da ake fada a kansa ba haka ba ne

Hukunci: Yaudara ce! Da aka bincika an gano cewa wannan bidiyo tsoho ne an yi shi tun a 2025,kafafan yada labarai sahihai sun nunar da cewa abin da ake fada game da bidiyon ba haka ba ne

Cikakken Labarin 

Matsalar tsaro na ci gaba da zama babban kalubale a Najeriya ganin yadda ake ganin jami’an tsaro da ‘yanbindiga wani abu ne da ke ci gaba da jawo muhawara a tsakanin al’umma.

A ranar 18 ga watan Yuni,2026 wani mai suna Obiasogu David (@afrisagacity) ya yada bidiyo na wasu jami’an tsaro sanye da kaki tare da ‘yanbindiga.

An ga yadda jami’an tsaron ke shiga motarsu yayin da ‘yanbindigar ke hawa babura wasu na tafiya a kasa kamar wasu abokan juna da sojojin da ‘yansanda.

”Wannan bidiyo mai tsawon minti guda an ba shi taken,”An gano jami’an tsaro a kayan damara tare da ‘yanbindiga da bindigunsu suna tare kamar wasu abokai. Me ke faruwa ne?”

Wannan wallafa kamar (a nan) ta ja hankalin wadanda suka kalla sama da  6355 (views) da masu tsokaci 15 (comments) da wadanda suka sake yadawa 80 (shares) ya zuwa ranar 22 ga watan Yuni, 2026.

Wannan da’awa ta fuskanci martani mai zafi a shafukan sada zumunta.

Ahmedu Nwoko (@AhmeduNwoko) ya rubuta cewa, “ ‘yan Najeriya su kare kansu su dena jiran jami’an tsaron da tuni sun ba da kansu, abu ne sananne tuni gwamnatin Najeriya ke tallafar ‘yanta’adda su kashe al’umma a Najeriya.”

Shima Fanocean (@Emmanue50088843) ya rubuta cewa, “Gwamnatin APC ta ‘yanta’adda ce, na dade ina fadin haka dama ace ‘yan Najeriya sun sani cewa ‘yanta’adda suke mulkarsu.”

Ganin cewa wannan batu ne da ya kamata a yiwa taka tsantsan, ga irin tasirinsa ga ‘yanNajeriya, hakan ya sanya DUBAWA ganin cewa ya zama dole a tantance labarin.

Tantancewa

Domin gano gaskiyar da’awar mun bibiyi asalin bidiyon tare da yi masa filla-filla inda DUBAWA ta kalli kowace gaba tasa ta hanyar amfani da InVid wata manhaja da ake amfani da ita don gano asalin bidiyo. 

Sakamakon ya nunar da cewa wannan bidiyo na nan tun a watan Yuni,2025 , mun ga shafukan Facebook da dama sun yada wannan bidiyo kamar nan zaa a iya latsa wannan (link)  ga shi ma a nan zaa iya latsa (link).

Daga nan an bincika ta hanyar amfani da wasu muhimman kalmomi don duba batun a 2025. Wannan ya kaimu ga rahoton da jaridar The Guardian inda ta yi wa labarin taken “ Bidiyon ‘yanta’adda da dakarun tsaro a Katsina da aka yi wa mummunar fahimta.”

Jaridar ta The Guardian ta ankarar cewa Bidiyon da ya nuna dakarun tsaro da ‘yanta’adda a Katsina kamar suna dasawa an masa mummunar fahimta.

Zagazola Makama, kwararre kan harkokin da suka shafi yaki da ta’addanci ya nunar da cewa lamarin a zahirin gaskiya batu ne na sasanci da ake yi da ‘yanta’addar ba tare da amfani da karfin bindiga ba a Yankin Arewa maso Yammacin Najeriya.

Mutanen da aka gani a Bidiyon ba wasu ba ne illa ‘yanbindigar da suka kudiri aniyar ajiye makamansu bisa radin kansu a kokarinsu na komawa cikin al’ummarsu.

A Karshe

Bidiyon na gaske ne amma da’awar da ake raba shi da ita ba gaskiya ba ce. Hoton bidiyon da ake gani an dauke shi ne a 2025, lokacin da wasu da suka dena ta’addanci suka mika wuya tare da ba da makamansu a yayin da ake kulla yarjejeniyar zaman lafiya.

Exit mobile version