Babu gaskiya a bidiyo da ya nuna ‘yan Fulani na kai wa mutane hari a jihar Katsina

No evidence viral video shows Fulani Bandits live-streaming attacks in Katsina
Fulani masu garkuwa mutane. Asalin hoton: Shafin muryar Amurka/ Voice of America
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: A shafin Facebook na mujallan Hausaland ne wani bidiyon da aka saka a TikTok ya nuna yadda wasu ‘yan Fulani mahara ke kona kauyuka tare da kashe wasu da ake zargi daga al’ummar Hausawan wurin ne wadanda ba su ji basu gani ba a can a jihar Katsina.

Babu gaskiya a bidiyo da ya nuna ‘yan Fulani na kai wa mutane hari a jihar Katsina

Hukunci: Babu isashen hujja. Babu tabbataciyyar hujjan dake nuna Fulani a lokacin da suke kai wa mutane hari a jihar Katsina. Bidiyon bai nuna wurin da wannan lamari ya faru ba, babu alamun gaskiya a bidiyon sannan babu hukumar da ta fito ta tabbatar da bidiyon.

Cikakken Labari.

A ranar 29 ga watan Yulin 2026 mujallan Hausaland a shafinta na facebook ya wallafa bidiyon (A nan) a TikTok ya nuna yadda Fulani ‘yan ta’adda ke kona kauyuka da kashe wasu Hausawa ‘yan farin hula da basu ji ba su gani ba a jihar Katsina.

Da’awar ta nuna cewa Fulani ‘yan ta’adda sun dauki bidiyon kuma sun saka a TikTok yadda suke kona kauyuka tare da kashe Hausawa ‘yan farin hulan da basu ji basu gani ba a Arewa maso Yammacin Najeriya (Katsina). Wannan tamkar ta’addanci ne da kisan kabillanci. Wannan laifi ne ga bil Adama. Muna kira ga hukumomin kasa da kasa, Hausawa matasa, dattawa Hausawa da shugabancin Najeriya da su gaggauta daukan mataki. Shurun da ake yi na sa mutane rasa rayukansu.

Bidiyon ya nuna wasu matasa masa akan babura sannan wasu na tafiya a kasa kuma a bayan su hayaki mai kauri na tashi.

A ranar 5 ga Agusta 2026, mutum 3,400 sun kali bidiyon, 105 sun kara wallafawa, 84 na son bidiyon da mutum 36 sun mayar da martani.

Moussa TK ya rubuta a shafinsa na Facebook cewa “Hausawa ku shirya makaman ku domin kare rayukan ku daga harin wadannan la’ananun ‘yan Fulani”. 

 Raphael Nwokobia ya ce “Menene ya sa Fulani ‘yan ta’adda ke yin haka? Hausawa sun saudakar da komai domin ganin sun basu wurin zama amma abin kirkin da suka yi shine zai sa a saka musu da kisa”.

DUBAWA ta gano irin wadannan bayanai a Xda Facebook inda hakan ya sa ta gudanar da bincike.

Tantancewa.

DUBAWA ta yi amfani da manhajar tantance asalin hotuna ‘InVID verification Tool’ domin gudanar da bincike kan bidiyon.

Sakamakon binciken ya nuna cewa Ohamadike TV ya wallafa wannan bidiyo a shafinsu na Facebook a ranar 28 ga watan Yuli 2026 da da’awar cewa “Wannan shahararren dan bindiga kuma dan TikTok Suka ya saka bidiyon yadda mutanen sa suka kona wani kauye”.

 A ranar 28 ga Yuli 2026 @secmxx ya saka wannan bidiyo a shafinsa na X da da’awar “Dan bindiga kuma dan TikTok Suka ya saka bidiyon aiyukkan da kungiyarsa ke yi na kona kauyukan mutane a  jiya. Akwai alamun cewa bidiyon ya dade domin ciyawan dake cikin bidiyon ba su yi kama da wadanda ke tsitowa da damina ba. Mai badda bayanai kan aiyukkan mahara ya yi kokari wajen sa ido a wuraren da maharan suka fi karfi.

DUBAWA ta gano rashin gaskiya a tattare da wasu rubutun da wasu suka yi wajen maida martani. Wani rubutun da gidan jaridar ta gani ya nuna cewa wannan lamari ya faru a jihar Katinsa, sai dai babu tabbacin inda harin ya faru. Amma da’awar da aka saka a X da Facebook bai fadi cewa lamarin ya faru a jihar Katsina ko wani wurin da ya faru. 

Rahotanin da Daily Times ranar 31 ga Yuli 2026 da PM News ranar 3 ga Agusta 2026 sun nuna a lokuta daban-daban yadda mahara suka kai hari a karamar hukumar Bakori a jihar Katsina inda a dalilin harin mutum sama da 5,000 sun rasa gidajen su da kai wa mazaunan kauyen Shuwaki hari. Wadannan rahotanin sun bayyan wuraren da harin ya faru ba kaman na wannan bidiyo ba da ba fadi inda lamarin ya faru ba.

DUBAWA ta gudanar da bincike domin gano ko da wata hukuma ok rundunar ‘yan sandan jihar ta yi magana game da bidiyon amma bata ga komai ba. Gidan jaridar ta duba shafin gwamnatin jihar Katsina na yanar gizo da shafin ‘yan sandan jihar amma duk basu bada bayanai game da bidiyon ba.

Gidan jaridar ta tattuna da wasu mazaunan jihar Katsina game da bidiyon.

Amina Musa dake zama a garin Katsina ta ce a kwanakin da suka gabata jihar ta yi fama da hare-haren mahara musamman a yankin karkara amma babu inda aka rika kona kauyuka kamar yadda bidiyon ya nuna.

DUBAWA ta gudanar da bincike domin gano ko gidajen jaridu sun fitar da rahoto ko kuma hukumomi sun bada bayanai game da bidiyon musamman daga wajen rundunar ‘yan sandan jihar amma babu komai.

A TikTok sakamakon binciken da gidan jaridar ta samu shine yadda mahara ke nuna kudade da kayan da suka karba na fansan mutanen da suka yi garkuwa da su.

A Karshe.

DUBAWA ta kasa tabbatar da cewa lamarin da bidiyon ke nunwa ya faru a jihar Katsina. A kwanakin da suka gabata jihar ta yi fama da aiyukkan mahara amma babu bayanin da alakanta abin da ya faru a bidiyon da harin da jihar ta yi fama da su a kwanakin da suka gabata.

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.