|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: A shafin Facebook na mujallan Hausaland ne nuna cewa Fulani ‘yan ta’adda sun kashe shugaban karamar hukumar Bungudu jihar Zamfara.

Hukunci: Babu isashen hujja! Babu tabbataciyyar hujjar da ya nuna cewa an kashe shugaban karamar hukumar Bungudu dake jihar Zamfara Nura Abdullahi. Rahotanni sun tabbatar cewa Abdullahi na tsare a hannun mahara bayan sun yi garkuwa da shi ranar 25 ga Yuli 2026.
Cikakken Labari.
A ranar Talata 4 ga watan Agustan 2026 shafin Facebook na mujallan Hausaland ya nuna cewa an kashe shugaban karamar hukumar Bungudu dake jihar Zamfara. Da’awar ta nuna cewa: “Fulani ‘yan ta’adda sun kashe suhaban karamar hukumar Bungudu Zamfara. Mun gode, Tinubu”
Wannan da’awa ya bayyana kwanaki bayan mahara sun kai hari gidan shugaban karamar hukumar Bungudu Nura Abdullahi inda suka kashe jami’an tsaro hudu sannan suka yi garkuwa da shugaban karamar hukumar tare da wasu mutane biyu.
Da’awar (da aka saka a nan)ya samu 195 likes, 104 sun mayar da martani da 47 sun sake wallafawa da mutane da dama a Facebook da suka amince da hakan.
Misalli Modibbo Mohammed Mustapha ya ce “dai-dai hakan ya yi kyau”
Wani Ekezie Chidi ya ce “lallai ne ma shugaban karamar hukuma gaba daya hakan na nufin cewa mu sauran mutane namu ya kare”.
Shima Ibuyo Terkaa ya ce “Mutumin ya taba fadan cewa an samu nasarar dakile rashin tsaro amma sai gashi mutanen sun mai da shi abin koyi”.
Ganin yadda mutane da dama sun amince da da’awar duk da rashin ingantattun hujojji musamman yadda da’awar ya shafi matsalar rashin tsaro DUBAWA ta gudanar da bincike domin tabbatar da lamarin.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da bincike domin gano ko akwai rahotanin da ingantattun gidajen jaridu suka wallafa game da kisan shugaban karamar hukumar Bungudu Nura Abdullahi amma bata samu komai ba.
Amma ta gano wani rahotan da gidan jaridar PREMIUM TIMES ta wallafa ranar 4 ga Agusta 2026 cewa Bello Abdullahi wan shugaban karamar hukumar ya mutu a dalilin raunin harsashin da ya samu a lokacin da mahara suka kai wa gudan shugaban karamar hukumar hari.
Bisa ga rahotan maharan sun kai wa gidan shugaban karamar hukumar daje Bungudu hari ranar 25 ga Yuli 2026 in da a gidan suka kashe jami’an tsaro hudu sannan suka yi garkuwa da shugaban karamar hukumar tare da wasu mutane hudu.
Gidan jaridar ‘Blueprint’ a ranar 5 ga Agusta 2026 a wani rahotan da ta gabatar mai taken “Dan uwan shugaban karamar hukumar Bungudu da aka yi garkuwa da shi ya mutu a dalilin raunin harsashi da ya samu a Zamfara” Hakan ya tabbatar cewa ba shugaban karamar hukumar bane ya mutu amma dan uwansa ne wanda ya samu rauni bayan mahara sun kawo hari gidan shugaban karamar hukumar.
Rahotanin sun kuma shaida cewa shugaban karamar hukumar Bungudu na nan tsare hannun mahara wanda hakan ya karyata da’awar da aka saka a Facebook cewa an kashe shugaban karamar hukumar.
DUBAWA domin kara tabbatar da wandannan rahotani ta nemi rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara inda ta yi kokarin kiran jami’in hulda da da jama’a na rundunar DSP yazid Abubakar a wayar hannun sa amma ta kasa samun sa.
DUBAWA ta duba shafin Facebook na rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara domin ganin ko sun yi magana game da kisan shugaban karamar hukumar amma ba ta ga komai ba.
A Karshe.
Da’awar dake nuna cewa an kashe shugaban karamar hukumar Bungudu Nura Abdullahi karya ce. Amma hujojji sun nuna cewa mahara sun yi garkuwa da shi ranar 25 ga Yuli 2026 amma babu rahotanin da suka tabbatar da mutuwarsa.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.
