|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Mc Izzy a shafinsa na Facebook ya nuna wani bidiyon yadda wani sojan najeriya ke samar da harsasai wa ‘yan bindiga.

Hukunci: Yaudara ce! Duk da cewa bidiyon ya nuna zahirin abin da ke faruwa amma bidiyon daga shekarar 2022 ne ba a cikin kwanakin nan aka dauke shi ba.
Cikakken Labari.
Mc Izzy a shafinsa na Facebook ya wallafa wani bidiyo (a nan) inda ya nuna wani mutum sanye da rigar sojoji da abokan aikinsa ke chaje shi bayan an tsinci harsashi da ya boye a kugunsa. Izzy ya yi zargin cewa sojan shine ke samar da harsasai wa mahara da masu garkuwa da mutane.
Ya rubuta cewa “kun ga yadda sojan ke samar da harsasai wa mahara”.
Izzy ya ce “Wadannan mutane sune ya kamata a hukunta su duk duniya su gani domin ko kun amince ko ba ku amincewa ba akwai saura irin haka da suke irin wannan muggun aiyukka. Da dama daga cikin su na runduar ‘yan sanda, sojoji da ma ko’ina.
Rubutun da ya yi da aka fasara shi da turanci ya ce “Mutum irin haka kamata ya yi a hukunta shi duniya ta gani domin ko a amince ko ba a amince ba akwai mutane irin haka da suke aikata wadannan aiyukka. Da dama daga cikinsu na rundunar ‘yan sanda, sojoji da ko’ina.
Zuwa ranar 7 ga Agusta 2026 mutum 483,000 sun kalli bidiyon, 769 sun kara wallafa shi, 769 na son bidiyon da 104 sun mai da martani.
Bidiyon ya jawo ce-ce- ku-ce a fannin tattaunawa inda wasu suka ce bidiyon tsoho ne amma wasu sun amince cewa bidiyon sabo ne.
Jay Jay a shafinsa na Facebook ya ce bidiyon tsoho ne inda ya rubuta cewa “wannan tsohon bidiyo ne ai”
“Wannan tsohon bidiyo ne da aka dauka shekaru 3 zuwa 4 da suka gabata yanzu” Oluwakemi Oyibo ya ce.
Aliu Ahmed ya ce “Ba shine kadai ke aikata irin haka ba. A gani na ya kamata a gudanar da bincike ….”
“Allah ya ci gaba da tona asirin su Amin” Abdullahi Faruk ya rubuta.
Tantancewa.
An yi amfani da ‘InVID tool’ wajen tantance bidiyon sannan aka kara amfani da ‘Reverse image search’ inda sakamakon ya sa aka gano wani bidiyo da @ NationNews ya wallafa ranar 12 ga watan Oktoba 2022 da rubutun da aka yi ya ce “An kama soja da harsasan da ake zargin zai kai wa Boko Haram”.
A Instagram @ogunupdate ya wallafa wannan bidiyo a ranar 11 ga Oktoba 2022. Rubutun da aka yi ya nuna “Allah ya fi ku; kullun na barawa rana daya na mai kaya, za ka je ka bai wa Boko Haram wadannan makamai domin su kawo mana hari”
An kuma gano wani bidiyo mai tsawon minti 1 da sakan 56 da aka saka a 2022 inda rubutun da aka yi daban yake da wanda aka fara sakawa mai tsawon mintu 4da sakan 31.
Binciken da aka gudanar ya taimaka wajen gano wani bidiyo da gidan jaidar ‘The Cable’ ta saka ranar 11 ga Oktoba 2022 da taken “An kama sojan da ya sato harsasan da zai je bai wa Boko Haram a Borno”
Rahotan da gidan jaridar ta fitar ya nuna cewa sojoji sun kama sojan mai suna Emmanuel Iorliam dake aiki a karkashin rundunar ‘156 Task Force Batalion’ da aka fi sani da sunan Ofreshan Hadin Kai a kauyen Mainok dake jihar Borno.
A wani rahoto da Punch ta fitar ranatr 13 ga Oktoba 2022 ya nuna irin wannan bidiyo.
Hujjan da aka gano ya nuna cewa bidiyon tsoho ne da aka dauka tun a shekarar 2022. Wanda hakan ke nuna cewa an sake saka bidiyon ne.
A Karshe.
Bidiyon tsoho ne da aka dauka tun a shekarar 2022 da aka saka domin yaudaran mutane.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.
