Bidiyon dake nuna ‘yan ta’adda na habbaka dokar shari’a, an gyara shi ne ya nuna hakan

Viral video of terrorists promoting Shari’a law, manipulated
Asalin hoton: shafin Futd Transport Daura.
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani a shafinsa na Facebook  ya wallafa wani bidiyo  da ya nuna yadda  ‘yan ta’adda ke yi wa ‘yan Najeriya barazanar cewa gwamnati ba za ta iya ceton su ba sai dai dokar shari’a.

Bidiyon dake nuna ‘yan ta’adda na habbaka dokar shari’a, an gyara shi ne ya nuna hakan

Hukunci: Yaudara ce! Sakakamon binciken da DUBAWA ta gudanar ya nuna cewa bidiyon an hada shi ta hanyar amfani da fasahar AI ne. Anihin bidiyon na Boko Haram ne tun wanda aka saka a yanar gizo tun a watan nuwan ba 2015.

 Cikakken Labari

A shafin sa na Facebook datboy comedy ya saka wani bidiyo a ranar 29 ga watan Yuli 2026 da ya wasu ‘yan ta’adda na yi wa ‘yan Najeriya barazanar cewa dokar shari’a ce kadai maganin matsalolin da ake fama da su a kasar nan.

A bidiyon (da aka saka a nan) maharan sun ce “Idan har kuna ganin gwamnati za ta iya ceton ku wannan karo, kuna ba’a ne. Abin da zai iya ceton ku shi ne dokar shari’a kawai. Allah ya ba mu wannan kasa kyauta kuma mai alkawari”.

Zuwa ranar 11 ga Agusta 2026 mutum 256,000 sun kali bidiyon, 2,600 sun duba, 1,200 sun mai da martani yayin da 1,700 kuma sun kara wallafa bidiyon.

Da’awar ya nuna cewa ya jawo ce-ce-ku-ce tsakanin mutane minda mutane da dama a Facebook sun amince da bidiyon.

Alabi Kayode Collins a shafinsa na Facebook ya ce “Mai ceton da muka sani shine Yesu amma ba dokar shari’a ba. Muna yi wa mai ceton mu kadai Yesu Almasihu yabo”.

Alabi Bamidele Grace ta yi tambaya “Shin menene amfanin dokar shari’a, menene dokar shari’a, saboda Allah? Ba ku yi maganar jin tsoron Allah ba zai dokar shari’a. Wadanda suke amfani da dokar akwai wani abin ko yi a rayuwar su ne da muke gani? Tsoron Allah shine hikima. A yi hankali”

Sai dai kuma wasu da suka kalli bidiyon sun nemi karin haske kan asalin bidiyon.

Simon Amadu ya ce bidiyon an yi amfani da AI ne wajen hada shi. “Wannan yaudarar AI ne “.

Ganin yadda bidiyo zai iya yadda labaran karya musamman a wannan lokaci da ake fama da rashin tsaro a Najeriya, DUBAWA ta binciki bidiyon.

Tantancewa

DUBAWA ta fara gane cewa bidiyon baya ci gabawa yadda ya kama inda a wasu wuraren bidiyon na tsinkewa.

A dalilin haka muka gudanar da bincike kan bidiyon ta hanyar amfani da Hive AI inda skamakon ya nuna cewa kashi 88.1% na bidiyon an yi amfani da AI.

Sautin da aka saka a bidiyon an yi amfani da AI domin an ga kashi 98.9% na AI a ciki.

Bidiyon dake nuna ‘yan ta’adda na habbaka dokar shari’a, an gyara shi ne ya nuna hakan

Hoton sakamakon nazarin da aka yi a manhajar HIVE

Wani AI din da aka yi amfani da shi wajen tattance bidiyon ISFAKEAI ya nuna akwai kashi 87% na cikin bidiyon.

Bidiyon dake nuna ‘yan ta’adda na habbaka dokar shari’a, an gyara shi ne ya nuna hakan

Sakamakon da aka samu a shafin ISFAKEAI.

DUBAWA ta kuma gano cewa an saka bidiyon tun a watan Nuwanba 2025 a yanar gizo ba a watannin da suka gabata ba kamar yadda ake nunawa. Shafin ‘Politics Religion and Crime” ne suka saka bidiyon a shafinsu na Facebook.

A wani binciken da aka gudanar ya nuna cewa gidajen jaridu da dama sun yi amfani da bidiyon a da. Gidajen jaridun sun hada da Zagazola, NHTV, da Affinity TV inda a bidiyon da suka yi amfani da shi ya nuna yadda Boko Haram ke kashe mata dake dauke da laya da guru bayan sun zarge su da bauta wa gumakai a karamar hukumar Gwoza jihar Borno.

 A Karshe

Bidiyon dake nuna yadda ‘yan ta’adda ke yi wa ‘yan najeriya barazanar habbaka dokar shari’a AI ne kuma yaudara ce kawai.

Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.