|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: A 2026 ne a shafin @Shine Borno na Facebook aka wallafa wani hoto dake nuna yadda mahara suka kashe ‘yan sanda ranar 10 ga Agusta 2026 a Rafi Makuku dake jihar Kebbi.

Hukunci: Yaudara ce! Rahotani da dama da rundunar ‘yan sandan Najeriya sun tabbatar cewa mahara sun kashe ‘yan sanda 10 amma hotan da ake nunawa AI ce.
Cikakken Labari.
A shafin Facebook na Shine Borno, aka wallafa wani hoto (da aka saka a nan) da da’awar cewa mahara sun kashe ‘yan sanda a Rafin Makuku dake karamar hukumar Sakaka a jihar Kebbi ranar 12 ga watan Agustan 2026.
“Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da kisan ‘yan sanda 10 a dalilin batakashin da suka yi da mahara a jihar Kebbi inda jami’an tsaron suka kashe mahara 17.
A ranar 15 ga Agusta 2026 da’awar ya samu mutum 1,300 duba hoton, 285 sun mai da martani da 39 sun sake wallafa hoton.
Apaer Aaron a shafinsa na Facebook ya ce “Kasar dake kula da mutanen ta ba za ta bar mutane da ma’aikatanta na mutuwa ba kulun ba tare da daukan mataki ba.
“Idan har Gwamnatin Tarayya ta shirya yin daga da ta’addanci amma su wanene ‘yan ta’addan? Boko Haram da makiyaya? Ina yi wa matasa maza da mata dake shi’awar zama jam’an tsaro kuka. Da dai zai fi idan sun nemi wani aikin da ya fi wannan sun yi. Inji Jeffrey Agber.
Simeon Otilo ya yi tambaya cewa “menene ya sa matsaloli irin haka ke yawan faruwa rundunar tsaron Najeriya?
Wannan hoto ya kareda yanar gizo musamman yadda aka gani shi a nan, nan, nan, nan, nan, nan da nan, da nan a Facebook.
Tantancewa.
Mun gudanar da bincike ta hanyar amfani da ‘Google Reverse Image’ amma ba mu ga wani abu dake da alaka da hotan.
DUBAWA ta yi amfani da ‘Keyward search’ inda ta gano DUBAWA The Punch, The Cable, Daily Trust, da sauran gidajen jaridu masu inganci sun fitar da rahoto kan kai wa jami’an tsaro hari. Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta tabbatar da harin da kisan ‘yan sanda 10 da wasu mutane ‘yan farin hula da mahara suka yi a kauye da aka wallafa ranar 13 ga Agusta 2026.
DUBAWA ta yi amfani da ‘Artificial Intelligence (AI)’ domin tabbatar da ingancin hoton IsThisAI inda ta gano cewa kashi 91% na hotan AI ne sannan da Hive Detect tool wanda ya nuna cewa kashi 58.1% na hotan AI ne.

Hoton da ke nuna cewa nazarin da aka yi kan ko an kirkiro da AI ne ya nuna cewa akwai yiwuwar an yi haka na kashi 91 cikin 100

Hoton nazarin da aka yi a manhajar Hive ya nuna cewa akwai yiwuwar an kirkiro da AI na kashi 58.1 cikin 100
DUBAWA ta ci gaba da gudanar da bincike inda ta gano hulan rundunar sojin Najeriya a kusa da kawunan jami’an tsaron da aka kashe. Sannan gidajen jaridu da rundunonin tsaro ba su tabbatar ko an kashe sojoji ba a harin.
A Karshe
Hotan da ya nuna mahara sun kashe jami’an tsaro yaudara ce. Binciken da aka gudanar sun nuna cewa lamarin ya faru a jihar Kebbi amma hoto da aka yi amfani da shi AI ne.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.
