|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: wani mai amfani da shafin X, Usman (@secmxx), na da’awar wai jami’an tsaro sun daui wasu mayakan da ba’a san ko su wane ne ba cikin jirgi mai saukar ungulu dagaa makarantar firamaren da ke karamar hukumar Mashegu

Hukunci: Yaudara ce! Duk da cewa ba mu iya tantance duka abubuwan da suka faru ba, jirgi mai saukar ungulun ya sauka a wata makabarta ne ba makarantar firamaren Kaboji kamar yadda ake da’awa ba.
Cikakken bayani
Wani mai amfani da shafin X wanda aka tantance shafin shi a humance, @secmxx, ya wallafa wani bidiyo ranar biyu ga watan Yulin 2026, wanda ke nuna wasu maharan dajin da ake zargin wai maharban Dogo Gide ne wadanda suka yi rauni ake sanya su cikin wani jirgi mai saukar ungulu yayin da wani dandazon mutane ke hangensu daga nesa.
Taken da aka yi wa bidiyon na cewa, “Wasu daga cikin mayakan da suka yi rauni ke nan ake kwashe su daga makarantar firamaern Kaboji a karamar hukumar Mashegu na jihar Neja…”
Mawallafin ya kuma kara da cewa wadannan ‘yan bindigan sun iso Tashan Bare na karamar hukumar Mashegun jihar Neja ne daga Zamfara kuma sun bukaci galan 30 na man fetir da abincin da aka riga aka dafa.
Daga 4 ga watan Yulin 2026, mutane sama da dubu 31 sun kalli bidiyon, wasu 32 sun yi tsokaci, 97 sun yi ma’amala da labarin wasu 65 su kuma sun adana shi a bookmark.
Da ya ke mayar da martani dangane da labarin wani mai amfani da shafin DavidEdu (@Dave92025002) ya yi rubutu kamar haka, “Idan kun yarda ku tantance wannan labarin. Yanzu kuna nufin cewa ‘yan bindiga sun fara amfani da jirage masu saukar ungulu?
Wani shi ma mai amfani da shafin, Brigs (@Brigs247286) ya yi tsokaci kamar haka, “Ba gaskiya ba ne, Dogo Gide ya isa wurin cikin motarsa kafin ya tafi da jirgi mai saukar ungulu ya na daga hannu kamar wani shugaban kasa.”
Shi kuma Larry King (@mrlarryking2), tambaya ya yi kamar haka, “mayakan da suka yi raunin har ake kwashe su, dakarun Najeriya ne?
Wannan da’awar ta shi ga kusan ko’ina kamar yadda za ku iya gani a nan, here, nan, nan, nan da nan a shafin Facebook.
Ganin yadda matsalar tsaro ta ke a yakin arewacin Najeriya da ma yiwuwar labari irin wannan ta kai ga farfgaba ko kuma ma ta yaudari jama’a ya sa DUBAWA tantance labarin.
Tantancewa
Sadda DUBAWA ta zakulu mahimman hotuna a cikin bidiyon ta sa cikin manhajar InVid wadda ke tantance aasalin hotuna ba mu ga wani labarin da ke da alaka da hotunan ba.
Sai dai DUBAWA ta tattuna da wasu shaidun gani da ido daga kauyen Kaboji da ke karamar hukumar Mashegun na jihar Neja inda aka ce jirgin ya sauka.
Lallai mazauna wurin sun tabbatar da labarin mawallafin na cewa akwai jirgi mai saukar ungulun da aka gani ya kwashi ‘yan bindigan da suka yi rauni sai dai ba a wata makabarta ya sauka ba a makarantar firamaren kauyen ya sauka ba kamar yadda ake da’awa.
“Wata tsohuwar makabarta ce. Ko daya bata kusa da makarantar firamaren. Sun yi amfani da jirgi mai saukar ungulun ‘yan sanda ne wajen fitar da mayakan Dogo Gide,” ya fadawa DUBAWA.
Majiyar dai ya ce jirgin ya sauka ne tsakanin karfe 11 na dafe da 12 na rana kuma sun motocin sojoji hudu a Kaboji. Haka nan kuma ya ce sun je sun tsaye a kusa da wani karamin asibitin da ke kauyen inda wani bafilatanin da ake kyautata zaton Dogo Gide ne ya fito.
“Ya na da tsawo kuma ya na sanya abin rufe fuska. Ya bai wa daya daga cikin mazauna wurin wayarsa su yi masa caji a cikin asibitin saboda suna da wutar sola,” ya bayyana.
“Yayin da wayar ke caji, sai ta fara kadawa, sai mutumin da ke cikin asibitin ya ga sunan wanda ke kira ‘Kachalla Kebbi’. Daga nan sai ya karbi wayar ya fata cewa “yara na na zuwa daga daji, dan haka jirgin ya fara zuwa,” ya bayyana.
Mahadi ya ce jirgi mai saukar ungulun ya kewaya kauyen sau uku kafin ya sauka a tsohuwar makabartar.
Jama’a sun sheka wurin a guje suka taru dan ganin abin da zai faru. Sojoji sun koma makabartar. Akwai wata motar asibiti da wasu motocin sojoji uku. Sadda suka kai makabartar, mutane hudu kadai muka gani a ciki. “
“Mutumin farko an harbe shi a kai, wani kuma a kafa yayin da sauran biyun kuma a hannu ne aka harbe su,” Mahadi ua bayyana.
A cewarsa, Dogo Gide ya shiga jirgin tare da daya daga cikin wadanda suka yi raunin, inda ya kara da cewa wadanda suka yi raunin ba ‘yan sanda ko sojoji ba ne, illa matasa maza masu dogon gashin da aka kitsa.
Wani mazaunin, Sani Mohammed shi ma ya fadawa DUBAWA cewa “Jirgi mai saukar ungulun bai sauka a makarantar firamaren ba, ya tabbatar a makabartar ya sauka. Akwai tazara sosai tsakanin makarantar firamaren da makabartar.”
“Mayakan Dogo Giden da suka yi rauni ne aka fitar a cikin jirgi mai saukar ungulun. Mutane hudun da suka yi rauni ne aka fitar daga daji aka sa a jirgin aka tafi da su,” a cewar Sani.
Cikin wani labarin da aka wallafa ranar 12 ga watan Janairun 2026 kakakin rundunar ‘yan sanda Nahum Kenneth ya wallafa (kamar yadda za ku iya gani a nan) hotunan wani jirgi mai saukar ungulun ‘yan sanda ya na tashi.
DUBAWA ta kwatanta lambar rajistan wannan jirgin wato, 5N-MNS, wanda ake iya gani a jikin jirgin wanda ake zargin ya dauki mayakan Dogo Gide.
Mun ganio cewa lambobin iri daya ne da wanda ke jikin jirgin ‘yan sandan.

Hoton jirgin da ‘yan sandan suka wallafa.
Mun tuntubi Wasiu Abiodun, mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, sai dai bai amince ya yi bayani dangane da abin da ya faru ba. Iyakaci dai ya ce ana kyautata zaton sojoji ne suka gudanar da wannan aikin.
“Ana hasashen cewa sojoji ne suka gudanar da wannan aikin. Zan baku shawara ku tuntubi sojojin dan samun karin bayani kan wannan lamarin,” ya ce.
A Karshe
Bidiyon da ake da’awar wai jirgi mai saukar ungulu ya kwashi mayakan Dogo Gide daga makarantar firamaren Kaboji a karamar hukumar Mashegi na jihar Neja yaudara ce. Bincikenmu ya nuna mana cewa jirgin ya sauka ne a tsohuwar makabartar Kaboji ba makarantar firamare ba kamar yadda labarin ke bayani. Wannan lamarin ya afku ne ranar biyu ga watan Yulin 2026.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.
