|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wani a shafinsa na Facebook ya ce rundunar sojin sama ta Najeriya sun kashe mahara sama da 200 da suka taso daga jihar Zamfara za su Kebbi.

Hukunci: Yaudara ce! Tabas sojoji sun yi batakashi da maharan da suka taso daga jihar Zamfara za su Kebbi sannan rahotani su nuna cewa sojojin sun kashe mahara 17 amma ba sama da 200 ba. Rundunar ‘yan sanda ta ce har yanzu ba ta da tabbacin yawan mutanen da suka ji rauni a dalilin batakashin.
Cikakken Labari.
A shafinsu na Facebook United Middle Belt Region ta ce rundunar sojin sama ta Najeriya sun kashe mahara sama da 200 bayan sun taso daga jihar Zamfara za su Kebbi.
Da’awar da aka saka ya nuna cewa rundunar sojin sama dake aiki a karkashin rundunar Ofreshan FANSAN YAMMA sun yi wa mahara ruwan bamabamai bayan sun tattaro bayanan siri game da aiyukkan su da ya nuna cewa maharan a iyakan kasan jihar Zamfara da Kebbi.
Da’awar ya nuna cewa maharan sun taso daga kauyen Sangeko Gap daje jihar Zamfara za su kauyen Makuku a jihar Kebbi akan babura.
“JUST IN: Rundunar sojin sama sun kashe mahara 200 bayan sun taso daga jihar Zamfara za su Kebbi” da’awar ya ce.
Zuwa ranar 15 ga Agusta mutum 679 na son da’awar, 429 sun mai da martani da 50 sun sake wallafa da’awar.
A Facebook mutane da dama basu amince da shi ba wasu kuwa sun amince.
Alonge Fahad Armstrong a shafinsa na Facebook ya yi tambayar cewa “Rundunar sojin sama ta Najeriya na da masaniyar wannan labarin karyan”?
Amos Babatunde Adebisi ya ce “Wanda ya dauki bidiyon ya yi aiki mai kyau. Ya kamata ya yi karin haske kan yadda aka kashe mahara 200 sannan shi mai daukan bidiyon ya tsira da ransa”.
Maidawa Samba Jr., da ya amince da hakan ya ce “Irin wannan labarin ne nake so ji daga rundunar sojin sama”
Lookman Bolaji ya rubuta a shafinsa “Hakan ya yi kyau. Allah ya albarkaci jami’an tsaron Najeriya ya ci gaba da kare su duka”.
Tantancewa.
DUBAWA ta gudanar da bincike domin gano ko wani ingantacen gidan jarida sun buga labarin inda ta gano cewa a ranar Litini 10 ga Agusta 2026 jami’an tsaro sun kai wa mahara hari bayan sun kamo hanya daga jihar Zamfara za su Kebbi.
Ana hasashen cewa maharan da suka taso daga kauyen Sangeko Gap a jihar Zamafara za su Makuku dake karamar hukumar Sakaba jihar Kebbi sun kai 240. Maharan na tafiya a kan babura sannan sun kasa kansu zuwa gudaje uku yayin da suka yi kusa da jihar Kebbi wanda hakan ya firgita mutane masauna kauyukan dake iyakan kasan dake Zamfara da Kebbi.
Rundunar sojan kasa dake aiki a karkashin rundunar ‘8 Division’, ‘yan sandan moba da sojan sama dake aiki a karkashin rundunar Ofreshan FANSAN YAMMA sun tare wasu mahara yayin da suke kokarin shiga jihar Kebbi.
Mataimakin shugaban rundunar, jamian hula da jama’a na rundunar sojin Najeria, rundunar ‘8 Division’, sojojin dake aiki a karkashin rundunar ‘Sector 2, Ofreshan FANSAN YAMMA lutanan konel Olaniyi Osoba ya tabbatar da lamarin wa jaridar Daily Trust inda a lokacin yake cewa jami’an tsaron na aiki sannan rundunar sojin Najeriya na boye wasu bayanai domin guje wa matsalolin yaudara. Gidajen jaridun PUNCH da Vanguard sun bada rahoto kan lamarin.
DUBAWA ta gano rahotanin da gudajen jaridu da suka hada da Premium Times, AL JAZEERA da pmnewsnigeria suka fitar game da lamarin.
Bisa ga rahotanin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi Bashi Usman ya tabbatar cewa jami’an tsaron sun kashe mahara 17 sannan suna kokarin tattance yawan maharan da aka kashe. Rahotan ya kuma nuna cewa ‘yan sanda 10 sun mutu, mutane biyu ‘yan farin hula sun mutu sannan ‘yan sanda biyu sun ji rauni.
DUBAWA domin kara tabbatar da rahotan ta duba shafin ‘yan sandan Najeriya dake yanar gizo musamnman na rundunar ‘yan sandan jihar Kebbi inda ta ga babu bayanan da ya tabbatar cewa rundunar sojin sama sun kashe mahara 200.
DUBAWA ta duba shafin gwamnatin jihar Kebbi dake yanar gizo amma babu bayanin kashe mahara 200 din da gwamnati ta fitar amma gwamnatin a shafin ta ta ce gwamnan jihar Nasir Idris ya yi alkawarin tallafawa iyalan ‘yan sanda 10 din da suka mutu a filin dagan da aka yi a Rafin Makuku dake karamar hukumar Sakaba.
A Karshe
Sakamakon binciken da DUBAWA ta gudanar ya nuna cewa rundunar sojin sama dake aiki a karkashin Ofreshan FANSAN YAMMA sun kashe mahara 17 amma ba 200 din da ake fada ba.
Rundunar ‘yan sanda ta ce har yanzu tana kokarin tattance yawan mutanen da suka ji rauni a dalilin farmakin. Kashe mahara sama da 200 da ake fada karya ce.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.
