|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Mujallar Hausaland a shafin ta na Facebook a ranar 14 ga watan Agusta ta saka bidiyon da ke nuna yadda ‘yan ta’adda ‘yan Fulani ke barazanar cewa babu mai hana su.

Hukunci: Yaudara ce! Bidiyon ba sabo bane sakamakon bincike sun tabbatar cewa bidiyon tsoho ne domin an saka shi a yanar gizo tun a watan Disemba 2024 sannan a lokacin an gano alakar bidiyon da shahararren dan bindiga Bello Turji da mutanen sa.
Cikakken Labari.
A ranar juma’a 14 ga watan Agusta 2026 mujallan Hausaland ta wallafa wani bidiyo da ya nuna mahara dauke da muggan makamai suna magana.
Da’awar da aka (saka a nan) ya ce “Abin tashin hankali. Bidiyo ya bullo na yadda wasu ‘yan Fulani ‘yan ta’adda ke barazana da gadarar cewa ‘Babu wanda ya isa ya hana su. Za mu kashe duk wanda muka ga dama’.
Da’awar ya nuna cewa wannan lamari ba ta’addanci ba ne kadai amma ya hada har da matsalolin kwace wa kabilu filayen su, kisa a bangarorin Najeriya.
A cikin ‘yan sa’o’i kadan mutum 117 sun nuna suna son bidiyon, 67 sun mai da martani, 172 sun wallafa bidiyon da 17 sun saka alama.
Wasu sun alakanta bidiyon da rikicin kabilanci da siyasa.
Ogechukwu Marcus ta rubuta cewa “Wadannan mutane ba za su iya yin haka a kasar Inyamurai ba domin bama tsoro.
Ernest Okoro ya ce “Hausawa sun yi shuru saboda adinin musulunci, su ci gaba”.
Ude Emenike ya ce “Mazi Nnamdi Kanu ya gani kuma ya fada cewa mikewa tsaye da wuri domin kawar da wannan matsala shine zai fi mana”.
DUBAWA ta gudanar da bincike domin gano asalin bidiyon.
Tantancewa
DUBAWA ta gudanar da bincike domin gano ko akwai ingantattun gidajen jaridar da suka saki bidiyon musamman domin tabbatar da lamarin da bidiyon ke nunawa a cikin kwanakin da ake hasashen lamarin ya faru amma ba ta ga komai ba.
Gidan jaridar ta ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da asalin bidiyon inda ta gano bidiyon da Abdullahi Haruna Gobir ya saka a shafinsa na Facebook a ranar 27 ga watan Disemban 2024.
A bidiyon da Abdullahi ya saka ya ce “Jana Christofa idan har ba a yi hankali ba Bello Turji zai bata maka suna a rundunar sojin Najeriya. Ya kamata ga gaggauta daukan mataki kafin ya bata sunan ka da rundunar sojin Najeriya. Wannan shine shawarar da zan baka cikin ladabi.
Ya yi gargadi kan Bello Turji sannan ya yi kira ga rundunare sojin Najeriya da su gaggauta daukan mataki domin kare kimar rundunar sojin Najeriya.
Daga nan binciken ya gano bidiyon da Nishadi TV ta saka da rubutun da ta yi da Hausa cewa “Dan ta’adda Bello Turji ya sake Sakin sabon bidiyon da ke bai wa gwamnati umurni. Anya akwai gwamnati Mai Cikakken iko a Najeriya?”
DUBAWA ta kuma gano cewa gidan jaridar ‘Ripples Nigeria’ ta wallafi wani rahoto ranar 27 ga Disemba 2024 dake nuna wasu bangarori na bidiyon.
Taken rahotan shine “Idan har ka isa namiji fito mu yi daga”. Inji Bello Turji ga Jana Buba.
Rahotan ya nuna cewa Turji yi kira ga rundunar sojin Najeriya da su fito su yi daga tare da shi. Turji ya kuma yi wa mazaunan Shinkafi, Isa, Zurmi da kewaye barazana saboda hada hannun da suka yi da jami’an tsaro.
Rahotan da’ Ripples Nigeria’ ta fitar a ranar 27 ga Disemba 2024 da wanda aka saka a Facebook ya nuna cewa bidiyon ya dade yana kareda yanar gizo tun a Disemba 2024 kafin mujallan Hausaland da sake wallafawa a ranar 14 ga Agusta 2026.
Wannan ya karyata rubutun da aka yi a Facebook bidiyon da aka saka an dauke sa ne a cikin kwanakin nan.
A Karshe
Bidiyon wanda mujallan Hausaland ta wallafa tsohob bidiyo ne sannan hujojji sun nuna cewa tun a Disemba 2024 ne aka saka bidiyon a yanar gizo sannan yana da alaka da shahararren dan bindiga Bello Turji.
Wannan aiki an aiwatar da shi karkashin Cibiyar koyon Aikin Jarida da Kirkire-kirkire da Ci gaba (CJID) tare da tallafin Kungiyar Tarayyar Turai.
