
Da’awa: Wasu hotuna sun karade shafukan sada zumunta da ke nuna cewa matan shugabannin kananan hukumomin jihar Adamawa sun je Turkiyya domin samun horo kan jagoranci da ci gaban al’umma.

Hukunci: Gaskiya ne. Binciken DUBAWA ya gano cewa matan shugabannin ƙananan hukumomin Adamawa sun tafi horo a Istanbul, Turkiyya, kamar yadda rahotanni masu inganci suka tabbatar.
Cikakken Bayani
A ranar 22 ga Satumba, 2025, hotuna da labarai sun karade shafukan Facebook da WhatsApp inda aka bayyana cewa matan shugabannin kananan hukumomin jihar Adamawa sun isa birnin Istanbul na ƙasar Turkiyya domin halartar taron horaswa na mako guda kan jagoranci da ci gaban al’umma.
Rahoton (kamar yadda muka zakulo a nan, nan da nan) ya ce tawagar ta ƙunshi matan shugabannin guda 21, kuma gwamnatin jihar Adamawa ce ta ɗauki nauyin tafiyar, tare da haɗin gwiwa da kungiyar shugabannin ƙananan hukumomi ta kasa, wato ALGON.
Wannan batu ya haddasa cece-kuce tsakanin jama’a musamman a arewacin Najeriya. Wasu na ganin an kashe kuɗin jama’a ba tare da buƙata ba, yayin da wasu ke tambayar ko labarin gaskiya ne ko kuma sharri ne kawai.
Wani mai amfani da Facebook, Abubakar Al Ameen, ya yi rubutu cewa: “Dan Allah, tayaya za ayi wa talakan Arewa adalci idan kuɗinsa ake kashewa wajen yawon bude ido?”
Wadannan martani sun nuna yadda jama’a ke kallon irin wannan tafiya a matsayin almubazzaranci, musamman a yanayi da talauci da hauhawar farashin kaya ke addabar jama’a.
Sai dai a gefe guda, wasu na shakku kan gaskiyar labarin, kamar wani Usman Ibrahim Tanko, ya yi tambaya cewa: “Yawon bude ido da kuɗin talakawa? Wannan abin ba gaskiya ne ba.”.
Saboda yadda labarin da ra’ayoyi mabanbanta suka karade kafafen sada zumunta, DUBAWA ta gudanar da bincike domin tabbatar da sahihancin ikirarin.
Tantancewa
DUBAWA ta bincika a shafin nema na Google inda muka gano cewa labarin gaskiya ne.
Suleiman Toungo, shugaban karamar hukumar Toungo kuma shugaban ƙungiyar shugabannin kananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen Adamawa, ya tabbatar da tafiyar a tattaunawa da jaridar Punch.
Ya ce: “Mun yi irin wannan horo a watanni biyu da suka gabata, don haka ba na ganin wani abu da ba daidai ba a cikin tafiyar matanmu zuwa wajen horo. Su matanmu ne kuma muna bukatar shawararsu. Muna kallon muhimmancin horar da su kan jagoranci, ba kudin da za a kashe a tafiyar ba.”
Jaridar Daily Trust ma ta ruwaito wannan batu, inda ta nuna yadda martani daban-daban suka biyo bayan tafiyar.
Wannan ya tabbatar da cewa hotunan da ake yadawa na tafiyar sun yi daidai da gaskiya, ba kirkirarrun hotuna ba ne ko labaran ƙarya da aka shirya don bata suna.
A Karshe
Ikirarin cewa matan shugabannin ƙananan hukumomi na jihar Adamawa sun tafi Turkiyya domin shirin horo kan jagoranci gaskiya ne.