Yadda shafin Facebook, bayanan da ba daidai ba, da gazawar dokoki ke jefa matan Najeriya cikin sarkakiya in sun je daukar ciki wa wadanda ba su iya dauka da kansu dan samun kudi

Bayan da Temitope Afolabi ta fahimci cewa maigidanta na iya zuwa kurkuku saboda bashin nera milliyan 48 din da ke kansa sakamakon wani cinikin kasuwancin da ya lalace ne ta yanke shawarar daukar ciki wa wasu ma’aurata wadanda ke bukatar haihuwa dan samun kudin da zai taimaka mata wajen ceton mijin nata.  Da farko ta yi tunanin sayar da kodarta ne, amma da ba ta sami mai bukata ba sai ta yanke hukuncin daukar cikin. Daukar cikin da ba naka ba ko kuma Surrogacy kamar yadda aka fi sani a turance wata hanya ce ta taimakawa wadanda ba su iya haihuwa da kansu inda mace (wadda ake kira surrogate da turanci) ta kan dauki juna biyu a madadin wasu wadanda ba za su iya yi da kansu ba wadanda yawanci sune iyayen –  Ya tanadi hada kwan namiji da na namace a sa a mahaifar wata mata wadda ba ta da wata alaka iyayen kwayayen, dan ta dauki cikin na tsawon watanni tara yadda ya kamata domin wasu ba su iya yin hakan. Wannan harka ce ta kasuwanci tsantsa, inda ake biyan surrogate din, wato wadda ta dauki cikin. 

Masana’antar Surrogacy a duniya baki daya ta na da darajar dalar Amurka biliyan 27.9, kuma Majalisar Dinkin Duniya ta kawatanta shi a matsayin wani nau’i na cin zarafin mata da kananan yara. A Najeriya yanzu harkar ta fara yawaita, musamman a tsakanin taurari irin su  Nancy Umeh, Ini Edo, da Chimamanda Adichie duk sun yi amfani da shi. Shahararriyar infuluwensa kan harkokin rayuwa Ife Agoro ita ma ta bayyana sha’awar yin amfani da shi duk kuwa da irin kalubalen lafiyar da ke tattare da shi. 

To amma wani yanayi ne masu shiga wannan sana’ar ke fuskanta a kasar da ta fi yawan al’umma a nahiyar Afirka, kuma yaya aka yi har ya fara samun karbuwa haka? Na bibiyi cikin Temitope tun daga sadda ta fara laulayi har bayan haihuwa ta hanyar tattaunawa da ita manhajar sakonni na Facebook messenger, inda ta bayyana mun duka abubuwan da ta fuskanta dalla-dalla. Zan kuma sadu da ita ido da ido nan gaba dan samun karin bayani

Temitope ta fara aikin daukar cikin ne a watan Mayun 2024. A lokacin an biya ta kimainin N2,233,000, kuma wannan adadin ya kunshi kudin mota, da alawus na haya, da kudin nakuda, da kayayyakin sawa. 

Yadda shafin Facebook, bayanan da ba daidai ba, da gazawar dokoki ke jefa matan Najeriya cikin sarkakiya in sun je daukar ciki wa wadanda ba su iya dauka da kansu dan samun kudi
Hoton da ke bayyana yadda aka kasafta kudin da aka biya Temitope’s payment plan. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA ta Temitope.

To sai dai wannan kudin bai yi la’akari da yanayin rayuwa a Najeriya yanzu ba. Kudin motar da aka bata na N3,000 ba zai ishe ta yin kai kawon da ta ke bukata ba. Ta na zama ne a Sango Ota, wanda ke kan hanyan Oju ore a jihar Ogun, kuma daga nan zuwa asibitin da ta ke zuwa a Ikorodu akwai tazarar kilometa 41.9. 

Duk da cewa  an kara kudin motar zuwa N5,000  bayan da ta yi ta musu korafi, sun kara ne da sharadin cewa za ta fara zuwa wani asibitin na daban da ke Ikeja a jihar Legas wanda ya fi na Ikorodun nisa. Cikin hawaye Temitope ta bayyana mana cewa a hakan ma sai ta sake kara wani N1,000 daga cikin kudinta kafin ta kai asibitin ga kuma wahalan da za ta ji da shi saboda nisan da aka kara. Bacin haka da kyar ta ke samun kudin abinci bayan ta biya haya da kudin makarantar yaranta.

Nan da nan hawayenta suka koma fushi yayin da ta ke bayanin yadda mai shiga tsakani ko kuma agent dinta ya karbi N450,000 a sunan kudin zirga-zirga daga iyayen, ya na da’awan cewa sun yi amfani da motar hayar Uber ne wajen zuwa asibiti

“‘Yan Najeriya sun iya amfani da jama’a” ta bayyana cikin murya cike da hawaye. “Sukan yi amfani da mutane ba tare da la’akari da matsalolin da suke fuskanta ba. Ba su ma damu da nauyin cikin da na ke fama da shi ba, da laulayi da amai da sauransu. Amfani da mu kawai su ke yi kamar bayi domin sun yi imanin cewa idan har kai baka yi ba wani zai yi.”

Duk da cewa an bayyanawa Temitope yawan kudin da za’a ba ta dalla-dalla tun daga farko, ba’a fayyace mata sharuddan da ke tattare da su sai can daga baya. Kwantitraginta mai dauke da kwanan watan 26 ga watan Agustan 2024, ba ita ta sa hannu a kai ba sai bayan da cikin ya kai watanni uku cif-cif. Daga cikin sharuddan akwai ma inda aka ce ta fahimci cewa tana iya mutuwa. Wani rahoton BBC  ya bayyana cewa Najeriya ce kasar da ta fi muni wajen haihuwa, inda ake kiyasin cewa cikin kowani minti bakwai sai mace daya ta hallaka wajen haihuwa. Bacin haka, bisa tanadin kwantiragin, da likita da su wadanda ake daukar wa cikin ne kadai su ke da hakkin yanke hukunci kan irin matakan da za’a dauka idan har aka lura cewa cikin na tattare da hadari ga lafiyar ita wadda ta ke dauke da shi. Haka nan kuma an hana ta tattaunawa da manema labarai.

Surrogacy Agreement by Temitope Afolabi

Lokacin da ta ke dauke da cikin, an haramtawa Temitope barin gida da cin wadansu nau’o’in abinci na tsawon makwanni biyu, wadanda suka gada da: taliya (irin na indomie) lemu, abarba, lemun kwalba, da duk wani abun da ke konewa. Haka nan kuma tilas ne ta je asibiti a kai-a kai, ko tana so ko bata so ko da kuwa yaranta ne ba su da lafiya.

Bayan da ta haihu ranar 24 ga watan Fabrairun 2025, Temitope ta yi fama da wasu matsaloli. Ta fara ganin jinin hailanta sau uku cikin wata daya, ta kuma sami karin mahaifa (fibroid) da kuma tsiro a mahaifa (ovarian cyst). Sa’annan kuma ta rika jin jiri a kai-a kai. Da ta yi korafi sai aka ce mata wa’adin samun kulawa daga wajensu makwanni shidda ne kadai bayan haihuwa, dan haka wannan lokacin ya wuce.

“Ina ji kamar an yi amfani da ni ne kawai, kamar wata wawiya kuma ina yawan tunani,” ta ce tana nadamar yin wannan aikin. “A karshe, duk da abubuwan da suka faru, sai da miji na ya tafi kurkuku ranar 18 ga watan Disemban 2024.”

Kamar Temitope, wata wadda ita ma ta dauki cikin haka wadda na zanta ta ita ta shaida mun cewa ta yi fama da ire-iren wadannan matsalolin da Temitope ta yi fama da su bayan da ta haihu. Matar wadda daluba ce a jami’ar Benin kuma ta bukaci da a sakaya sunanta, ta haifi ‘yan biyu ne. A cewarta jinyar da ta yi bayan haihuwa ya ba ta wahala sosai kuma rabin kudin da ta samu ya kare  ne a kan jinyar da ta yi. 

Dr Sunday Olarenwaju, babban darektan asibitin Mother and Child Hospital, ya ce daukar cikin tagwaye na da hadarin gaske. 

Yadda shafin Facebook, bayanan da ba daidai ba, da gazawar dokoki ke jefa matan Najeriya cikin sarkakiya in sun je daukar ciki wa wadanda ba su iya dauka da kansu dan samun kudi
Dr Sunday Olarenwaju, babban darektan asibitin Mother and Child Hospital. Hakkin mallakar hoto: DUBAWA.

Ya bayyana cewa idan har mace ta dauki cikin yara biyu ko fiye, hadarin kamuwa da cututtuka kan karu, kama daga hawan jini, zubar da jini da ma mutuwa duk abubuwa ne da ka iya faruwa da ita. Masu binciken kimiya su ma sun bayyana cewa idan har mace ta dauki cikin da kwayayen sun banbanta da na ta kwayoyin halittan ta na iya samun cututtukan da ke da nasaba da mahaifa, da hawan jinin da ke iya kai ga mutuwa da sauran cututtuka makamantan su.

“‘Yan Najeriya ba su fahimci abun ba,” a cewar Temitope, yayin da ta ke bayanin cewa ta taba kokarin yin tsokaci kan abubuwan da ta fuskanta a kan shafukan sada zumunta na soshiyal mediya. “Cewa suka yi mu muka amince mu yi. Idan ba dan talauci ba wa zai taba amincewa da irin wanann abun? Babu wanda zai taya mu kwatar hakkinmu,” ta bayyana.

Rawar da Meta ke takawa wajen yada Surrogacy a Najeriya

Yayin da masu daukan cikin dan kudin da na zanta da su sun banbanta a yawan shekaru, abu daya da ya hada su shi ne wani shafi a Facebook da ake kira Facebook Surrogate group: Egg donor and surrogate mother in Nigeria, wato shafin masu daukar ciki dan kudi: bayar da kwai da kuma daukar ciki wa wadanda ba su iya wa a Najeriya. Ranar biyar ga watan Janairun 2023 aka kirkiro shafin kuma yana da mambobi 4,800 cikin shekaru biyu kadai.

Yadda shafin Facebook, bayanan da ba daidai ba, da gazawar dokoki ke jefa matan Najeriya cikin sarkakiya in sun je daukar ciki wa wadanda ba su iya dauka da kansu dan samun kudi
Hoton da ke nuna yawan mambobin da ke amfani da shafin daga biyar ga wtan Mayun 2025. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA.

Tallace-tallacen da ba’a iya ma kidanyawa sun cika shafin dangane da batun. Wasu daga cikinsu kan bukaci mutane su tura musu sakonni na samun karin bayani kai tsaye ko ta shafin sakonnin Facebook na Facebook Messenger ko kuma WhatsApp.

Yadda shafin Facebook, bayanan da ba daidai ba, da gazawar dokoki ke jefa matan Najeriya cikin sarkakiya in sun je daukar ciki wa wadanda ba su iya dauka da kansu dan samun kudi
Wasu daga cikin tallace-tallacen da ake wallafawa a shafin. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA.

Meta shi ne babban kamfanin da ya mallaki shafukan Facebook, Instagram, WhatsApp, da Messenger. Ana kiyasin cewa cikin kowani wata babban kamfanin fasahar na kasa da kasa na da akalla mutane biliyan 3.98 wadanda ke amfani da shi kan manhajojin shi kuma ya na da sharuddan da ke kula da wadannan dandalolin.

Babban shafin shi na bayanin cewa “ya na da nauyin inganta abubuwan da jama’a za su iya yi tare, ta hanyar tabbatar da lafiyarsu da kare su daga hadari da ma duk wani abun da zai cutar da su.” Dokokin Al’umma, wadanda ke kula da tallace-tallacen Facebook su ma sun hana yada abubuwn da za su yi sanadin cin zarafin mutane, kamar sayar da yara ko cutar da su wajen sanya su yin ayyukan da bai kamata su yi ba.  

Na tuntubi Meta ta adireshinsu na imel din suka bai wa ‘yan jarida su rika tuntubarsu da shi. Na tambaye su ko suna la’akari da surrogacy ko kuma daukar ciki dan kudi a matsayin wani nau’i na cin zarafin dan adam, kuma idan har haka ne, me ya sa kungiyoyin da ke habbaka wannan abun irin su Egg donors and surrogate mothers in Nigeria, wadanda suka yaudari mata irinsu Temitope, su ke kan shafin har yanzu. Bayan da ya rufe shafin, kamfanin ya mayar da martani, “talla da kungoyoyin da ke cin zarafin dan adam ta hanyar sayarwa ko kuma samun yara ta haramtattun hanyoyin sun keta dokokinmu, kuma mukan cire ire-iren wadannan kungiyoyin idan har aka gano su – kamar yadda muka yi a wannan karon.”

Yadda shafin Facebook, bayanan da ba daidai ba, da gazawar dokoki ke jefa matan Najeriya cikin sarkakiya in sun je daukar ciki wa wadanda ba su iya dauka da kansu dan samun kudi
Hoton shafin da Meta ya goge bayan wannan binciken. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA.

To sai dai Olivia Maurel, mai magana a madadin Yarjejeniyar Casablanca, wata kungiyar kasa da kasa mai zaman kanta wadda ta ke aiki dan haramta surrogacy ta shawarci cewa baya ga rufe shafuka, kamata ya yi a ce Facebook ya aiwatar da wata manufa wadda za ta haramta duk wani nau’i na tallar surrogacy musamman a yankunan da ake iya saurin yaudarar jama’a kamar Najeriya.

Yawaitar bayanan da ba daidai ba

Baya ga dokokin shi kan cin zarafin dan adam, Meta ya bayyana yadda ko daya ba ya jimirin bayanan da ba dai dai ba. Amma duk da haka, tattaunawar da na yi da masu shiga tsakanin masu neman haihuwa da wadanda ke daukar cikin dan kudi a WhatsApp na cike da rashin gaskiya, wasu karya ne ma kai tsaye da ma dai wadana ke rufa-rufa dan dai kawai su sami matan da za su yi abin da su suke so su yi.

Daya daga cikinsu wata tattaunawa ce da na yi da wata mai suna, Omobolanle Oguntolu, a WhatsApp. Na ga tallar da ta yi ne a shafin Surrogate Mothers Nigeria, mai mambobi 5,600. Ta sanya lambarta a bayanin ta kuma bukaci da a tuntube ta kai tsaye ta ofishinta mai suna, Regal Surrogate Services.

Yadda shafin Facebook, bayanan da ba daidai ba, da gazawar dokoki ke jefa matan Najeriya cikin sarkakiya in sun je daukar ciki wa wadanda ba su iya dauka da kansu dan samun kudi
Hagu-Dama: Tallar Surrogate Mothers Nigeria group & Regal Surrogate Services. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA.

Ita ma wannan kungiyar ta Surrogate Mothers Nigeria, na ja hankalin Meta a kai kuma sun cire shi. Ko da shi ke, da na tuntubi Omobolanle a kan WhatsApp a kan cewa ni ma ina da sha’awar zama surrogate in dauki ciki, ta yi da’awar cewa ta taimaki mata sama da 35 zama surrogates din.

Ta fada mun cewa za’a biya ni kusan N2,243,000 sa’annan ta turo mun cikakken bayanin yadda aka kasafta kudin.

Yadda shafin Facebook, bayanan da ba daidai ba, da gazawar dokoki ke jefa matan Najeriya cikin sarkakiya in sun je daukar ciki wa wadanda ba su iya dauka da kansu dan samun kudi
Hoton lissafin yadda aka kasafta kudin N2,243,000 da yadda za’a biya. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA.

Na yi kokarin yin ciniki da ita dan ta kara mun kudin da ma sauran masu shiga tsakani irinta, amma nan da nan na fahimci cewa sha’anin ko ka dauka ne ko ka bai. Daya daga cikinsu ma wadda ta bayyana mun sunanta a matsayin Sophia, ta ma kara kare kanta daga daukar wani nauyi bayan da ta bayyana mun farashin da za ta ba ni. “Ki yi kokari ki karanra dokokin tsarin biyan; Da zarar ki ka sa hannu ba mu so mu ji wani korafi.”

Daga nan sai na koma ga Omobolanle. Na fada ma cewa ban taba yin wannan aikin ba dan haka ta bayyana mun duk abubuwan da ya kamata in sani. A cewarta dai, ban da kudin da ake biya babu wani abun da ya kamata a sani sai dai idan ina da karin tambayoyi tana iya amsawa.

 “Tunda wannan ne karon ki na farko, ya kamata ki san abin da ki ke kokarin sa kan ki a ciki,” ta ce. 

Amma da na tambaye ta asibitin da zan yi amfani da shi, sai ta kada baki ta ce mun bai kamata ta fada mun wannan ba kuma ma ba za ta iya mun karin bayani a kai ba har sai lokacin da na kama hanyar zuwa wurin. Wannan ya ba ni mamaki sosai, har ma na tambaye ta yadda za’a yi in gudanar da bincike kan asibitin da ke rike da makoma ta; ita dai ta hakikance kan cewa ba za ta fada ba. Sai na tambaye ta ko mai zai faru idan har na gamu da matsaloli yayin da na ke dauke da cikin ko kuma ma ya kasance mun ajali.  Nan da nan ta ce tabbatar mun da kariya 100 bisa 100 ta na cewa ba abin da zai faru da n.i

Jumoke Falade, wata nas a asibitin koyarwa ta Jami’ar Jihar Legas, ta yi mamakin cewa akwai daukar cikin wanin da za’a iya kira “mara hadari” inda ta ce yana dauke da hadarruruka sosai har da yiwuwar mutuwa.

Omobolanle ta kuma ce idan har na dauki cikin, ba ni zan haifa da kai na ba tiyara zai a yi mun tun da ya fi kayu kuma zai fi ba ni irin kariyar da na ke bukata fiye da idan da zan haifa ne da kai na. Ti sai dai Dr Olarenwaju, wanda likitan mata ne a asibitin Mother and Child Hospital, ya ce idan dai irin wannan cikin ne, mace ta haihu da kanta ya fi a maimakon yin tiyata domin za ta fi warkewa da sauri kuma ba zai bar mata alamar yanka ba.

Kwararren likitan ya kuma kara fayyace cewa irin wannan cikin ba mahaifar mace ne kadai ya ke amfani da shi ba.

“Da huhun mace mai juna biyun jariri/jaririya ke numfashi. Jinin da ke yawo a jikin mace, da duk sauran sinadaran da ke jikinta ne ake amfani da shi wajen ci da shin jariri/jaririya a ciki,” ya bayyana. “Mahaifar tamkar daki ne kawai na jaririn/jaririyar.”

Bacin irin wadannan bayanan wadanda ba daidai ba da ke yaudarar jama’a dangane da lafiya, Omobolanle ta sake bayar da tabbacin cewa daukar ciki dan kudi ya halata a Najeriya kuma shi ya sa ake amfani da shi sosai a kasar.

Amma, kwararren lauya  Marvellous Igbineweka ya ce dokar lafiya ta kasa ta shekarar 2014 wato National Health Act of 2014 ta bayar da tanadin da ya haramta daukar ciki dan kudi. Wannan dokar ce ta hana bayar da gabobin jikin dan adam, da kwayoyin halitta ko fatan jiki dan samun kudi ko alfarma ko samun riba. Kwararren ya kuma sake hadawa da dokar kare hakkin kananan yara ta shekarar 2003 ko kuma Child Rights Act of 2003, tare da sashe na 13 na dokar da ta haramta fataucin mutane wato Trafficking in Persons (Prohibition) Enforcement and Administration Act, da ma doka ta 23 na dokokin tabbatar da da’ar likitoci wato Order 23 of the Code of Medical Ethics in Nigeria wadanda duk za’a iya amfani da su wajen kalubalantar sahihancin wannan aikin.

Wata lauyar ita ma, Dogo Joy Njeb, ta jaddada cewa wannan matsaya ce da wasu ke dauka domin a cewarta, “duk wani abun da doka ba ta fito fili ta haramta ba ya halata.” ta kare da cewa Najeriya ta halatawa ‘yan kasa shiga yarjeniyoyi, kuma a karkashin irin wadannan yarjeniyoyin ne ake yin na daukar ciki dan kudi.

Dan haka ne na tambayi Omobolanle dalilin da ya sa na gaza samun bayani a kan kamfaninta na Regal Surrogate Services a yanar gizo dan tabbatar da sahihancinta ban ga komai ba. Sai ta kayar da baki ta ce mun sunan da ita ta ke kiran shi ke nan “ita da kanta”

Hadin kan gwamnatin Najeriya

Kamfanin Omobolanle ba shi da rajista, amma kuma babu dokar Najeriyar da ta tilasta mata yin hakan. Har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta fito fili ta yi bayani kan irin wannan daukar cikin ba, dan haka halaccin shi abu ne da za’a iya yin mahawara kansa. Mambobin Majalisar Dokoki wadanda ke nauyin yin dokokin kasar sun yi yunkurin zartar da doka sai da yunkurinsu ya ci tura. Kudurin dokar samar da hukumar sa ido kan masu neman taimako wajen haihuwa (2012) da na samar da fasahar taimakawa masu neman haihuwa (2016) ba su sami wucewa ba domin ‘yan majalisar da suka hada dokokin ba su sami goyon baya ba.

Na tuntubi Christiana Eguma, shugaban sashen kula da jinsi ko kuma GTU a Majalisar Dokoki dangane da rashin kudurin dokar samun taimako wajen haihuwa ta hanyar samun wani na daban ya dauki cikin. Christiana ce shugabar kungiyar WRAPA ko kuma Kungiyar Wanzar da Cigaban Hakkokin Mata da Kare Zabin da suke da shi. Ta ce GTU za ta taka rawar gani ta hanyar samar da daftarin manufofin da za su ja hankali kan jinsi, da’a da tasirin da ya ke da shi kan kiwon lafiya idan har ba’a sanya ido kan yadda ake gudanar da shi ba.

Sai dai Hon. Olamijuwonlo Alao-Akala, mamba a majalisar wakilan da ke wakilitar mazabun arewaci da kudancin Ogbomoso, da Oriire na daukar nauyin kudrin dokar National Surrogacy Regulatory Commission Bill (2024) wanda ke kokarin samar da hukumar sanya ido kan batun surrogacy dan dakile matsalar da rashin doka takamaimai dangane da batun a kasar. Kudurin dokar ta wuce sauraro na biyu a majalisar wakilai cikin watan Oktoban 2024. Ana sa ran dokar za ta sanya ido ta kuma bayar da damar yin rajistan kamfanonin, ta yadda aikin zai halatta. Zai kuma hana musayar kudi cikin yarjeniyoyin daukar cikin. Wannan na nufin cewa za’a haramta yin shi a matsayin kasuwanci sai dai yin shi a kyauta.

Dangane da mahimmancin wannan dokar, Hon. Olamijuwonlo ta yi bayani kamar haka “dokar dan sa ido ne da tantance batun sirrogacy a Najeriya dan tabbatar da cewa na takaita karya dokokin likita da na kiwon lafiya.”

Haka nan kuma, Hon. Uchenna Okonkwo, wanda ke wakiltar mazabun Idemili Arewa/Idemili Kudu a jihar Anambra, shi ma ya na daukar nauyin kudurin dokar da ake kira “Kudurin dokar samar da dokar da za ta kare lafiyar mata, musamman ta la’akari da batun Surrogacy da sauran batutuwan da suka shafe shi.” Idan har kudurin ya zama doka shi ma zai haramta daukar cikin dan kudi.

Sai dai, Olivia, wadda aka haife ta ta hanyar yin surrogacy din, a yayin wata hirar da muka yi ta hanyar imel ta kushe irin wadannan kudurorin dokar

“Bai kamata mu banbanta tsakanin daukar ciki dan kudi da yin shi kyauta ba domin babu wani banbanci sosai tsakaninsu. Duka biyu na dogaro ne da abu daya: amfani da jikin na mace dan cimma burin wasu, yawancin lokutan kuma ta kan rasa lafiyarta, ‘yancin kanta da mutuncinta.”

Mai fafutukar kare hakkin jima’i da haihuwa Tobiloba Akanni ma ta yi tsokaci makamancin haka inda ta ce bai kamata a halatta duk wani nau’i na surrogacy ba, musamman a yayin da muke “wa’azin mutunci da daidaito wa mata.”

Majalisar Dinkin Duniya na bai wa kasashe shawarar kawar da duk wani nau’i na daukar wa wani ciki, da kuma hukunta duk hukumomin da suke taimakawa, a soke duka kwangwalolin da aka riga aka yi, a ba su tallafin da ya dace su cigaba da daukan yaran a matsayin na su.

Na tuntubi Hon. Olamijuwonlo ta shafin X (shafin da ake kira Twitter a baya), da WhatsApp da imel duk dangake da kudurin dokar da ya ke daukar nauyi dangane da damuwar masu rajin kare harkokin jinsi, sai dai bai amsa ko daya ba. Daga nan sai na yi magana da Hon. Uchenna Okonkwo kan tattauna na sa kudurin dokar. Dan majalisar ya ce in sake bugawa cikin sa’o’i biyu sai dai bai sake amsa wayoyi, sakonnin tes da imels din da na tura bayan nan ba.

A waje guda kuma Olivia na gargadin cewa, Idan har Najeriya ba ta dauki mataki yanzu ba, akwai hadafin cewa kasar za ta zama wani dandalin amfani da jikin mata dan samun yara kamar wadansu kayayyakin saye da sayarwa.”

Ungulu ta koma gidanta na tsamiya

Yayin da Temitope ke cigaba da fama da matsalolin kiwon lafiya sakamakon haihuwar da ta yi, kudin da aka biya N1.3 na haihuwa ya kare bak daya watanni uku kadai bayan haihuwar.

Ta yi amfani da mafi yawan kudin wajen ciyar da yaranta hudu da biya musu kudin makaranta da kuma turawa mai gidanta wanda ke kurkuku, sa’annan kuma ta biya sauran basussukan da ake bin ta.

Yadda shafin Facebook, bayanan da ba daidai ba, da gazawar dokoki ke jefa matan Najeriya cikin sarkakiya in sun je daukar ciki wa wadanda ba su iya dauka da kansu dan samun kudi
Temitope ta na shanya ganda (fatan shanun) da take saidawa. Hakkin mallakar hoton: DUBAWA.

Yanzu da duk kudin ya kare, Temitope ta koma sayar da ganda (fatar shanu), da fatan za ta sami abin da zai ishe ta ta kula da yaranta.

Bayanin Edita: Ku na Iya karanta wannan binciken a Yarbanci da Turanci. Ku na kuma iya ganin fim din da aka hada kan batun a nan.

Exit mobile version