Shin gwamnati ta gaza yin komai bayan kisan gilla a Majami’ar Owo?

Da’awa: Wani mai amfani da shafin Facebook, George Udom, yayi da’awar cewa babu wanda aka kama ko aka kai kotu bayan harin da aka kai a majami’ar St. Francis Catholic Church da ke Owo, jihar Ondo. 

Shin gwamnati ta gaza yin komai bayan kisan gilla a Majami’ar Owo?

Hukunci: Karya ce. Binciken DUBAWA ya gano cewa hukumomin tsaro sun kama wadanda ake zargi ana kuma gudanar da shari’a, ba a kai ga kammalawa ba.

Cikakken Sako

Shugaban kasar Amurka Donald Trump a baya-bayan nan ya fitar da wata wallafa post inda yake cewa “Kirista na fuskantar barazanar kawar da su a Najeriya” sannan ya bayyana Najeriya a matsayin ‘kasa da ya kamata a bata kulawa ta musamman’, yace Amurka za ta sake nazari kan taimakon da take ba wa Najeriya muddin mahukuntan kasar suka gaza yin abin da ya dace na ba da kariya ga al’umma mabiya addinin Kirista.

Da take mayar da martani Gwamnatin Najeriya (Federal Government) tayi fatali da zargin cewa ana kisan kiyashi, tana mai cewa da’awar Amurka ba cikakkiya bace ta dogara ne da bayanai da aka tattara wadanda ba cikakku ba ko ma na yaudara. Ta kara da cewa gwamnatin Najeriya tana aiki da kundin tsarin mulkin kasa wanda ya ba wa kowa tabbaci na damar gudanar da addininsa.

Bayan faruwar wannan sai aka samu wasu hare-haren irin wadannan suka sake bayyana a shafin sada zumunta, inda a wasu lokutan aka rika sake kanun labaran zuwa kisan kiyashi a shafukan sada zumunta. Daya daga cikin irin wadannan shine abin da ya faru a ranar 5 ga watan Yuni, 2022 inda aka kai hari a Cocin  Katolika ta St. Francis a Owo jihar Ondo.

A sake duba wannan labarin tashin hankali ne wani mai amfani da shafin Facebook  George Udom yayi ikirarin cewa hari ne aka tsara shi a kokarin kawar da Kiristoci a doran kasar Najeriya sannan gwamnatin Najeriya ta gaza daukar matakin shari’a ga wadanda suka kitsa harin. Ya rubuta cewa “Sun zo Owo, jihar Ondo a wata ranar Lahadi kamar haka, sun aikata kisan gilla kan abokaina da iyayensu. Fiye da mutane 50 ne aka halaka. Ka san abin mamaki? Babu wanda aka kama ko aka gurfanar a gaban shari’a. Na so ace na shiga sojan Amurka da na san wasu matsaloli kadan da zan yi maganinsu. ”

An dai rika samun mabanbantan martani kan wannan Umoh Bassey kuma “har yanzu Musulmi na cewa babu kisan kiyashi ga mabiya addinin Kirista a Najeriya..!”

Richards Junior Amana ya mayar da martanmi da cewa “An kama akalla mutum biyr daga cikinsu, kuma mambobi ne na kungiyar ISWAP,” 

Don Onoja U. Samuel  ya yi martani ne da cewa “Kisa ne na kasa don haka ne ma babu wanda aka kama” yayin da  Brave Udofia yayi tambaya da cewa , “Ina gwamnan jihar a wannan lokaci?” 

Fola Ramsey ya kara da cewa, “George Udom, a karon farko dana yarda da abin da kake wallafawa, ina ga mun yi tarayya da kai muna da abokin gaba guda daya duk da banbancin siyasa da ke tsakaninmu. Najeriya ita ce kasa daya tilo da muke da ita kuma za mu yi duk mai yiwuwa don tabbatar da ganin ta ci gaba da wanzuwa. Gaba dai gaba dai Najeriya.”  Wannan wallafa an yada ta sau 61 ya zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba, sannan ta samu martani da dama.

DUBAWA ya ga dacewar gudanar da binciken gano gaskiya kan harin na Owo kasancewarsa babban abin tashin hankali da ya shafi iyalai da dama da mabiya darikar ta Katolika da ‘yan Najeriya baki daya. Wannan lamari  an cukurkuda shi da ma danganta shi da wata da’awa mara tushe wato shigar da mahukunta na kasa wajen goyon bayan kisan kiyashi, wannan karfafa gwiwa ce wajen yada labaran da ba haka ba ko jita-jita, abin da ka iya harzuka rikici na addini  da jawo daukar ramuwa ta wani bangare da jawo rashin mutuntawa ga bangaren shari’a. 

Tantancewa

Sabanin abin da mai da’awar ke fadi “babu wanda aka kama da gurfanarwa a gaban shari’a.” Mahukunta sun kama tare da gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a wannan hari.

A watan Agusta,2025, mahukunta a Najeriya sun gurfanar da mutane 5 da ake zargi a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja saboda alakantasu da harin da aka kai a ranar 5 ga watan Yuni,2022 wadannan mtane da ake zargi kamar yadda aka ba da rahoto sune  Idris Omeiza da Al Qasim Idris da Jamiu Abdulmalik da Abdulhaleem Idris da Momoh Otuho Abubakar wadanda suka ce basu aikata laifin komai ba an kuma ci gaba da tsare su (remanded) a wajen jami’an tsaro na farin kaya (DSS).

An gurfanar da su a gaban kuliya ne bisa tuhumar aikata laifi na ta’addanci sauran abubuwa da suka biyo baya sun hadar da neman beli da sauran zaman kotu sannan an dage zaman kotun zuwa  10 ga Satumba,Sept. 2025 inda anan ne kotu ta hana beli bisa kafa hujjar kasancewarsu barazana ga tsaro. A watan Nuwamba, jami’an na DSS a bayyane sun tabbatar da cewa sun gabatar da wadanda ake zargi da harin na Owo a gaban kuliya, a wani yunkuri na gurfanar da mutanen bisa tuhumar ta’addanci

A Karshe

Da’awar cewa babu wanda aka kama ko aka gurfanar a gaban shari’a a dangane da harin ta’addancin na Owo wannan ba gaskiya ba ne.Rahotanni da aka tabbatar sun nunar da cewa wadanda ake zargin jami’an tsaro sun kama su kuma an gurfanar da su a gaban babbar kotun shari’a ta tarayya, ana dai shari’a ba kammala ba, don haka wani yace babu abin da ake daga bangare gwamnati wannan kuskure ne ya sabawa abin da yake na zahiri wanda kuma irin hakan na haifar da rura wutar rikici na addini da yada jita-jita.  

Exit mobile version