Yadda binciken gano gaskiyar labari ke ci gaba da kare rayuka duk da kuwa da tarin kalubalen da ke tattare da yin hakan

A duniyar mu ta yau karya na bazuwa kamar wutar daji fiye da gaskiya, Karya na samun yaduwa da jan hankali tsawon lokaci kafin wani yayi tambaya “Shin wannan da gaske ne?” Duk da haka masu aikin gano gaskiyar labari na ci gaba da gudanar da ayyukansu, suna ci gaba da nazari da tantancewa su fito da komai a faifai, ba abu ne mai sauki ba, ba ko da yaushe ne ake kambamawa ba, amma dai tana ci gaba da tasiri ga rayuwar al’umma.

Yadda labaran da ba haka suke ba ke kara samun gindin zama

A aikin gano gaskiyar labari a yau yana tare da yawan kalubale, intanet ta cika da labaran karya daga labaran da ba na gaskiya ba, a fannin siyasa zuwa lafiya zuwa bidiyo da ake hadawa da fasahar AI wadanda ake gani kamar na gaskiya ….Mutane da dama na fama da fargabar shin wa za su amince da shi. Masu aikin gano gaskiyar labari na fama da kalubale na kudaden daukar nauyin ayyukansu (struggle with limited funding,) ga matsi na bukatar ganin suna ayyukan da yawa ba tare da samun tallafin ba sosai.

Duk da irin wannan kalubale aikin gano gaskiyar labari na ci gaba. Duk aikin gano gaskiyar da duk aikin bincike da duk wani ilimantar da kafafan yada labarai na ci gaba da bayyana dalilai da suka sanya wannan aiki ya zama dole a ci gaba da yin sa.

Ya tasirin yake a zahiri

Hakikanin tasirin aikin gano gaskiya ba ana auna shi a mizanin lambobi bane. Ana ganinsa ne ta sauyin da ake gani bayan gaskiya ta bayyana.

A lokacin da editar DUBAWA Simbiat Bakare, ta gano cewa mata a shafin Facebook ana yaudararsu a sanya su cikin aiki mai hadari na goyon ciki. Ta so ta fahimci hakikanin abin da ke faruwa, sai ta fara gudanar da bincike kan batun na aikin goyon ciki a Najeriya ta hanyar intanet abin da kuma ta gano abin tashin hankali ne (what she found was heartbreaking.) Bata yi tunini za ta bankado shafukan da ake ci da ganin matan ba da labaran karya da rufe baki, mata da dama ana masu alkawura na samun tallafi daga karshe sai a zambace su ta hanyar wani gungu ko guruf a intanet wadanda ke buya bayan aikin tallafi da jinkai na karya suma samun riba.

Hoto da ke nuna labarin goyon ciki. Hoto:  Dubawa.org

Bayan wallafa labarin a manyan jaridu a Najeriya da suka hadar da DUBAWA, Premium Times, da The Guardian, binciken ya bude kofar muhawara conversations a kasashen Afurka da ke magana da harshen Ingilishi da masu magana da Faransanci. Wannan ya sanya mutane su sauya tunani people to rethink their stance kan batun na goyon ciki. Labarin ya haifar da muhawara a gidajen rediyo kamar West Africa Democracy Radio da Wazobia FM da Abuja Info da Police Radio da Trust Radio

Yadda binciken gano gaskiyar labari ke ci gaba da kare rayuka duk da kuwa da tarin kalubalen da ke tattare da yin hakan

Simbiat Bakare na tattaunawa ta hanyar intanet kan binciken da ta gudanar a kafar yada labaran Nigeria Info.  Hoto: DUBAWA

Baya ga haka wannan bincike ya jawo sauyi: inda kamfanin Meta ya goge guruf 9 na masu wannan harka ta yaudarar mata su shiga aikin goyon ciki (deleted nine surrogacy groups) wadanda ke ci da gumin yara da mata. Gaba dayansu suna dauke da mambobi 38,000 a duniya.Wasu kungiyoyi kuma masu fafutukar yaki da ci da gumin matan ta hanyar dashen kwan haihuwar (Several surrogacy support groups) suma sun fara aikin sanya idanu tare da kawar da duk wani talla da ke jan hankali kan ribatar matan shiga aikin dashen kwan haihuwar ana ci da guminsu.

Tasirin bai tsaya anan ba. Rahoton ya samu kulawar kwararru daga Majalisar Dinkin Duniya Mai ba da rahoto na musamman a Majalisar Dinkin Duniya kan take hakkin mata da yara  Reem Alsalem, ta kara kambama labarin, haka nan kungiyoyi na kasa da kasa da na cikin gida sun ci gaba da kiraye-kiraye na ganin a matakin duniya an haramta ci da gumin mata ta hanyar amfani da su a batun dashen haihuwar.

Idan ba a manta ba a kwai bincike da aka yi kan Baba Aisha investigation, inda editan aikin binciken na DUBAWA’ Kemi Busari,ya fallasa aikin wani mutum da ke kira “Baba Aisha” wanda ya bayyana kansa a matsayin likita. 

Ya kuma yi alkawari na ba da abin mamaki ta hanyar warkar da marasa lafiya da masu neman bukata ta gaggawa? Wannan aikin bincike ya fito da gaskiya daban-daban, ya gano kurari na Baba Aisha karya ne, kuma kwalbar magungunansa game-game ne kawai wanda ke da hadari ga lafiyar al’umma.

Labari ne da ya taba zuciya, haka kuma ya fallasa wani abu da yake bukatar kai hankalin al’umma game da lafiya da bai kamata a yi watsi da shi ba.

Hoton wani dan tebir da ke siyar da magungunan Baba Aisha.  Wanda ya dauki hoto: DUBAWA

Kwanaki bayan fitar da wannan labari Hukumatr Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa a Najeriya NAFDAC ta shiga aiki. Hukumar ta shiga aikin bincike (an investigation), tare da kai simame wuraren da ake hada magungunan aka rufe (sealed off the building),aka kama mutane biyu tare da kama kayayyakin da suke yi, duk wannan cikin sa’oi 24. Shima Baba Aisha aka bibiye shi aka kama tare da tsare shi.

Ba da dadewa ba kuma hukumar ta NAFDAC ta bayyana a fadin kasa a kawar (mop-up) da duk wadannan magunguna a fadin Najeriya. Tasirin bai tsaya anan ba 

Sai da ma’aikatar lafiya ta tarayya ta yi alkawari na samar da sashi a ma’aikatar pledged to create a dedicated department wanda zai rika bibiyar ayyukan masu magungunan gargajiya a Najeriya don ba wa al’umma kariya.

A can ma kasar Laberiya wani yanki na Monrovia Whein Town inda anan al’umma ke cike da bacin rai sanadiyar tarin shara a kusa da wani tsauni, iyalai na rayuwa a wannan yanki a cikin yanayi na shara da hayaki ga barazanar cutuka a ko da yaushe.

Yadda binciken gano gaskiyar labari ke ci gaba da kare rayuka duk da kuwa da tarin kalubalen da ke tattare da yin hakan

 Yanki na Whein Town. Hoton: DUBAWA.

 A lokacin da Laymah Kolie, mai bincike a DUBAWA, ta ziyarci al’ummar ta bayyana yanayin wajen jibge sharar ta kuma kalli yadda al’umma ke rayuwa yau da kullum, ta ga yadda al’ummar ke ganin tasku duk rana bincikenta ya taba zuciya ya kuma kawo sauyi (her investigationtouched hearts and stirred action).

Jim kadan bayan wallafa labarin, Sanata Saah Joseph na yankin Montserrado ya kira taro da hukumomin da abin ya shafa don warware matsalar al’ummar yankin na Whein, nan da nan hukumar da ke ba da kariya ga muhalli  (EPA) ta shiga aiki na nazartar yanayin da gyara muhallin al’ummar (initiated a detailed feasibility study to explore safer landfill management and environmental recovery).

Haka nan aka ci gaba da samun tagomashi. Magajin garin Monrovia ya ba da tabbaci cewa gwamnati tayi aiki na gyara kasa a Chessmanburg, a yankin Bomi aka sauya wajen ajiye shara. A karon farko a tsawon shekaru  al’ummar Whein sun shaki tatacciyar iska, yaransu na fitowa su yi wasa ba tare da wata fargaba ba. 

Baya ga tarin binciken da ake yi, mun kuma ga tasiri na irin horo da muke samar wa al’umma a DUBAWA  ta hanyar taron karawa juna sani da horon kwarewa ga ‘yanjarida daga kasashen Afurka ta Yamma ta yadda suke iya gane labari na karya take, su tantance da’awa, su kuma koyawa wasu yadda za su yi aikin ta hanyar amfani da wasu kayan aiki kamar  DUBAWA Audio platform da manhajar binciken gano asalin labari ta chatbot, muna amfani da ci gaban fasaha ta yadda gaskiya za ta zama abin samuwa cikin sauki.

Aikin gano gaskiyar labari ba lalle ba ne sai ya zama babban labari a tsakanin kafafan yada labarai ko abin da ake magana a kansa a shafukan sada zumunta, amma dai yana cimma nasara duk wani labari da aka goge kamar a wadannan wurare (here da here da here) da duk wani bayani da aka gyara kamar yadda aka tattara a wadannan wurare (here da here, da here) da duk wani mutum da ya dakata ya tabbatar da labari kafin ya yada duka wadannan nasara ce ga aikin gano gaskiya.

Sun nuna cewa gaskiya na bayyana ko da kuwa an yi kokarin boye ta a baza karya kamar wutar daji, don haka ne masu aikin gano gaskiyar labari ke ci gaba da gudanar da ayyukansu.!  

Exit mobile version