Kifi mafi girma da aka kama a bana, hoto daga Hajiya Halima Hassan Kamba: Kwamishiniyar Mata ta jihar Kebbi
|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
TARIHI
Bikin Kamun Kifi na Argungu na daga cikin manyan al’adu na wannan masarauta ta Arugungu da ke jihar Kebbi Arewa maso Yammacin Najeriya, tun kafuwarta. Masarautar ta ci gaba da zama mai cin gashin kanta kimanin shekaru 509. Kafin wannan lokaci masarautar ta kasance gunduma ce karkashin daular Songhai ta Afurka ta Yamma, kuma lardin na Kebbi ya hadar da kasashen Nijar da Benin da Burkina Faso da wani bangare na Ghana. “A shekarar 1515 an samu matsala tsakanin gwamna na wannan yanki Muhammadu Kanta da shugaban kasa na Daular ta Songhai Muhammad Askia Toure inda Muhammad Kanta tare da sojojinsa suka hada kai suka yi bore suka ce sun fita daga karkashin mulkin Askia kana bin da suka bayyana da rashin yi masu adalci.” A cewar Sarkin Argungu Sama’ila Muhammad Mera. Hakanan, wannan shekara, za a gudanar da bikin Kamun Kifi na Argungu a shekara ta 2026, wanda zai kara jawo hankalin masu halarta daga ko’ina cikin duniya, musamman ma ga masoya wannan shahararren taron na argungu fishing festival 2026.
Kamar yadda yake cikin littafan tarihi Askia yayi kokari kamar wajen sau hudu yayi duk abin da zai iya na yaki a kokarin ganin ya maida Kebbi karkashin mulkinsa amma Allah bai nufa ba.
Dalilin wannan ya sanya Daular Songhai ta waste, sauran kwamandoji da ke rike da wasu daulolin suma suka bi sahun Kebbi suka ware. Tun daga wancan lokacin sarkin Kebbi na farko da sauran sarakuna suka hada wannan biki don tabbatar da adalci a tsakanin masarautunsu. Tun daga wancan lokaci ne duk shekara bayan an kare noma na shekara sai sarki ya tanadi wani gulbi ko kudiddifi guda sai a gayyaci duk wani mai sana’ar su ko kamun kifi kasancewar it ace sana’a ta biyu mafi girma , ana gayyatar dukkanin masunta su shiga gasar daga ko’ina wanda ya kama kifi mafi girma a karrama shi. A yi jawabai na cewa albarkatun kasa da gulabe ba mallakin wani mutum guda ba ne na al;umma ne. Ayi maganar tsaron kasa da sauran abubuwa da za su samar da ci gaban kasa.
A wannan shekara ta 2026 an yi wannan biki na kasa da kasa wato (Argungu International Fishing Festival) tsakanin ranakun 11 zuwa 14 ga Fabrairu,2026 a garin na Argungu a jihar Kebbi Arewa maso Yammacin Najeriya.
WASANNI DA AKA GABATAR
Bikin kamun kifin na bana ya samu halartar masu wasanni kala-kala, kama daga masu sukuwar dawaki da sukuwar rakuma da sukuwar jakai da wasan kwallon dawaki da dambe da kokawa da wasan jan igiya don gwada karfi tsakanin masunta da mahauta da gasar saurin iya fidan fatar akuya tsakanin mahauta da gasar kamun kifi da hannu ta manya da yara da linkaya don ceton rai da wasan shako da babban bikin kamun kifi da aka yi a ranar karshe ta wasannin.
An dai yi wasannin da suka kayatar inda mahalarta suka je da kallo daga sassa daban-daban na Najeriya da Afurka da sauran sassa na duniya.
HAWAN DABA

Hoto: Yusuf Nayaya
A rana ta uku ta wadannan wasanni da yammacin ranar Juma’a an gudanar da gagarumin hawan Daba inda mahaya dawakai suka nuna kwarewa wajen bayyana ado da kwalliyarsu da ma dawakansu.
Masu hawan dawakan sun samu rakiyar makada da busa kala-kala aka yi hawan cikin nishadi shi ma wannan biki ya samu halartar manyan mutane daga ciki da wajen Najeriya ciki kuwa harda Sarkin Argungu da wasu masu sarauta sama da 20 da gwamnan Kebbi da wasu kusoshi na gwamnatin jiha da tarayya da ministar al’adu da yawon bude ido Hannatu Musa Musawa da ta bayyana bikin kamun kifin na Argungu a matsayin abin alfahari da za su hada kai tsakanin gwamnatin tarayya da ta jihar Kebbi don kara bunkasa shi.
WADANDA SUKA SAMU NASARA A GASAR KAMUN KIFI TA BIKIN ARGUNGU 2026
An kammala bikin kamun kifi na Argungu da ya nuna irin al’adu da Najeriya ke da su da ke kara daukar hankalin al’ummar duniya. Bikin na kwanaki hudu ya zo karshe ne da gagarumin bikin kamun kifi a kogin Matan Fada mai tarihi da ya samu masunta sama da 50,000 da suka zo daga sassa daban-daban na Najeriya da ma wajen kasar.
Shugaban Kwamitin shirya gasar kuma mataimakin gwamnan jihar ta Kebbi Alhaji Umar Tafida, ya yaba wa duk masu ruwa da tsaki da suka sa hannu aka tabbatar da samun nasarar wannan gagarumin bikin da kasa ke alfahari da shi.
A wannan gasar kamun kifi Abubakar Usman daga Maiyama shi ya kasance wanda yayi nasara ta kama kifi mai nauyin kilogram 59 inda ya samu kyautar motoci sabbi kirar Toyota daga gwamnatin Kebbi da wata motar daga kamfanin shinkafa na WACOT hadi da Naira miliyan daya.Sai wanda yayi na biyu Abdullahi Garba daga Argungu da ya samu mota da kujerar aikin Hajji da kudi Naira dubu dari bakawai da hamsin, da kuma wasu guda biyu da suka yi na uku inda aka basu kyautar mashin.
Abubakar Usman daga Maiyama wanda ya kama kifi mafi girma a gasar Argungu 2026: Hoto daga Hajiya Halima Hassan Kamba: Kwamishiniyar Mata ta jihar Kebbi
Bikin kamun kifi na Argungu na shekarar 2026 ya kafa tarihi inda aka samu mahalartar daga sassa daban-daban na duniya da suka hadar da al’umma yankin Asiya da yankin Turai da sauran sassa na duniya. Mazauna garin na Arugungu dai sun bayyana cewa an dade ba a yi cikowa ba irin a wannan shekara kasancewar shekaru shida kenan rabon da a yi wannan biki.
