Babu hujjar cewa sojojin Najeriya sun kai wa ‘yan ta’adda hari kamar yadda aka nuna cikin wani bidiyon da aka wallafa

No evidence Nigerian soldiers attacked terrorists in viral video
Getting your Trinity Audio player ready...

Da’awa: Wani a shafinsa na X ya wallafa wani bidiyo da ya nuna cewa sojojin Najeriya sun kai wa ‘yan ta’adda hari.

Babu hujjar cewa sojojin Najeriya sun kai wa ‘yan ta’adda hari kamar yadda aka nuna cikin wani bidiyon da aka wallafa

Hukunci: Babu isasshen hujja. Bidiyon bai nuna sojojin Najeriya ba sannan bidiyon bai nuna wai ana kai wa ‘yan ta’adda ko ma su ‘yan bindiga hari ba kamar yadda bidiyon ke nunawa.

Cikakken Labari

Wani Crusader (@Armylucifer001) a shafinsa na X ya wallafa wani bidiyo da ya nuna cewa sojojin Najeriya na tunkarar ‘yan ta’adda infda har basu basu damar gyara halinsu. Bidiyon ya kuma nuna yadda wanu soja ke amfani da na’urar hangen nesa wato ‘Binoculars’domin hango abin dake faruwa daga nesa sannan wani soja na rike da babban bindiga kirar ‘Rocket Launcher’.

 An saka wannan bidiyo a yanar gizo ranar 10 ga Yuli 2026 da da’awar “Ku duba domin gamawa da abin dake gaban ku. Aikar da duk abin dake gaban ku lahira (Valhalla). Sojojin Najeriya basa wasa da ‘yan ta’adda. Babu damar gyara hali”.

Zuwa ranar 25 ga Agusta 2026 mutum 45,000 ne suka kalli bidiyon, 80 sun sake wallafawa, 19 sun maida martani, 519 sun nuna shi’awar su na bidiyon sannan 34 sun saka alamar takarda.

A fannin mai da martani mutane sun nuna alamun cewa sun amince da abin da bidiyon ke nunawa wasu kuwa sun nuna rashin amincewar su inda har suke bukatan sanin inda aka samu bidiyon.

ADINOYI a shafinsa nan X saboda ya amince da abinda bidiyon ke nunawa ya ce “Gawanwakin mutane ne muke gani. Su je su hadi da mahallicin su”.

Mr. Ayo a shafinsa na X ya rubuta cewa “Allah ya yi muka albarka!!!! Ku kashe duk wasu maharan da suka gani!!! Babu damar gyara hali.

Sai dai kuma Blvcko a shafinsa na X da bai amince a abin da bidiyon ke nunawa ba ya ce “Wadannan ba sojojin Najeriya ba ne. Basu ma da harsasai lol”.

ispeedtweets a shafinsa na X shima ya bukaci sanin inda aka samu bidiyon inda ya ce “wannan da gaske ne ko dai ana horar da jami’an tsaro? Ina ce wanda ke daukan bidiyon ya kamata ya nuna wanda ya kamata a kai wa harin.

DUBAWA ta gudanar da bincike domin tabbatar da gaskiyar lamarin.

Tantancewa 

A binciken da DUBAWA ta gudanar kan bidiyon dake da tsawon sakan 15 ta gano wasu abubuwa da take bukatan karin harske a kai.

Da farko dai DUBAWA ta kula cewa babu kara a bidiyon sannan duk da cewa bibiyon bashi da tsawo hakan ba shi ne ya tabbatar cewa bidiyon ba an yi amfani da dabarar AI ba wajen hada shi ba musamman yadda giudan jaridar ta kasa gano ainihin bidiyon.

Gidan jaridar ta gudanar da bincike domin tabbatar da ba a yi amfani da dabarar AI wajwn hada shi ba inda sakamakon ya nuna an yi amfani da dabarar AI kashi 20.7% wajen hada bidiyon.

No evidence Nigerian soldiers attacked terrorists in viral video 

Gidan jaridar ya yi amfani da wani dabarar Al ‘TruthScan’ inda sakamakon ya nuna an yi amfani da kashi 15% na AI.

No evidence Nigerian soldiers attacked terrorists in viral video 

Sakamakon TruthScan. 

Daga nan DUBAWA ta kwatanta rigar sojojin da mutanen dake cikin bidiyon ke sanye da shi da rikar sojojin Najeriya.

No evidence Nigerian soldiers attacked terrorists in viral video 

Daga hagu sojan Najeriya. Dama hoto ne na mutanen dake cikin bidiyon.

Idan aka kula za a ga cewa rigar sojojin Najeriya na dauke da tutar Najeriya sannan rigar sojojin dake bidiyon na da tuta mai launin kore da ja wanda wadannan launika ba sune sojojin Najeriya ke amfani da su ba.

Wannan ya nuna cewa sojojin dake bidiyon ba sojojin Najeriya bane kuma gidan jaridar ta kasa gano sojojin wani kasa ne.

A Karshe

Sakamakon binciken da DUBAWA ta gudanar ya nuna cewa sojojin dake bidiyon ba sojojin Najeriya bane sannan babu huja a bidiyon dake nuna ana kai wa ‘yan ta’adda hari.

Wannan bincike an gudanar da shi ne a karkashin shirin Cibiyar Bunkasa Aikin Jarida da Kirkire-kirkire (CJID) tare da tallafin Tarayyar Turai (European Union).