|
Getting your Trinity Audio player ready...
|
Da’awa: Wata da’awa da aka wallafa a shafin Facebook ta nuni da cewa idan mata suka jika ‘ya’yan hulba ana shan ruwan sau uku ko hudu a sati wannan na sanyawa su samu kwan haihuwa mai inganci, jikinsu zai daidaita da sinadarai gami da kara samun sha’awa.

Hukunci: Karya ce. Babu wata sheda a kimiyance da ta nuna cewa idan aka jika ‘ya’yan Hulba aka sha yana inganta kwan haihuwa da samun daidaito na jiki ko kara samun ni’ima kamar yadda mai da’awar ya nunar.
Duk da cewa ‘ya’yan hulba na da irin alfanunsu ga jikin dan Adam kamar yadda bincike da aka yi ya nunar, amma babu wani nazari da aka yi a dangane da wannan da’awar.
Babu wata sheda da ta nunar da cewa idan aka jika hulba aka sha na inganta kwan haihuwa da daidaita sinadaran jiki da kara sha’awa kamar yadda mai da’awar ya nuna. Duk da cewa ‘ya’yan na Hulba na da alfanu a jikin dan’Adam babu wata sheda a binciken masana da ya nuna cewa da’awar haka take.
Cikakken Labari
Batun lafiyar mata abu ne da ya shafi rayuwar miliyoyin mutane, sai dai ana samun ra’ayoyi mabanbanta da yadda wasu ke ba da labarin abin da ya shafi tasu lafiyar da shawarwari mabanbanta a dangane da lafiyarsu.Haka dai ake ci gaba da muhawara a dangane da batun na mata a shafukan intanet, har ila yau haka nan yada labarai da da’awa da ta shafi lafiya, wannan ya sanya ya zama wajibi a banbance tsakanin karya da gaskiya. Wannan ya nuna irin batutuwa da suka shafi lafiyar mata da aka yi da’warsu DUBAWA ke tantancewa tsawon shekaru.
Wani mai amfani da shafin Facebook, @Erinma Food Challenge, yayi da’awa cewa mata da suke jika ‘ya’yan Hulba suke sha kamar yadda (aka alkinta anan) suna da damar samun ingantattun kwayoyin halitta da daidaito a jikinsu haka nan yana kara masu sha’awa.
Ga ma karin wani rubutun da aka yi a dangane da wannan wallafa “Kalli abin da ke faruwa idan mata suka sha jiko na ‘ya’yan Hulba sau uku zuwa hudu a mako: Za ki kara samun sha’awa idan ba kya jin dadin tarawa da miji ; kwan haihuwarki za su inganta, sinadaran jiki kuma za su samu daidaito. Bayan an jika ‘ya’yan na Hulba tsawon sa’oi 24 ana iya kwashe su daga cikin ruwan ko kuma a sauya masu ruwa har sai sun salamce.”
Ya zuwa ranar 7 ga watan Yuli,2026 wannan wallafa ta samu masu nuna sha’awarsu 1,600 da masu tsokaci 603 da wadanda suka sake yadawa 165.
DUBAWA ta duba cikin tsokacin da ake yi don ganin me tunin mutane ke nunawa a dangane da wannan wallafar.
Daya daga cikin masu wallafar, @Mercy Agbo, ta nuna zakuwa ne ta neman karin bayani inda ta yi tambaya da cewa “ Ni nama daka ‘ya’yan Hulbar kafin na ga wannan wallafar, zai iya zama mai tasiri idan na sha a cikin shayi? Da ruwan sanyi ko na zafi? Mintuna nawa ya kamata ayi kafin a sha?
Ya ya kamata a sha, kafin cin abinci ko bayan kammala cin abinci?”
@Mere Ngozi ta yi nata tsokaci da cewa, “Ina da ‘ya’yan Hulba da ‘ya’yan Kubewa amma bansan yaya zan yi amfani da su ba, da Allah ayi min bayani kan yadda ake amfani da su.”
@Doyin Otor tambaya ta yi da cewa “Ina neman karin bayani a dangane da ‘ya’yan Hulba; za a iya yi min karin haske?”
Irin wannan da’awa dai ga ta ma a nan da nan.
Ganin yadda matan ke ta neman karin haske kan wannan da’awa ga kuma batu ne da ya shafi kula da lafiya, DUBAWA ta ga ya zama wajibi gudanar da bincike kan da’awar.
Tantancewa
Me ake nufi da ‘ya’yan Hulba?
’Ya’yan Hulba dan itace ne da ake samu daga itaciyar ta Hulba wadanda ke zama kalar makuba mai haske kuma kanana ne, sun fito ne daga iyalan shuka na (Trigonella foenum-graecum) a Turancin Kimiya, ana samun wannan ‘ya’yan Hulba duk shekara kuma tana nan kamar ‘ya’yan lambu. An fi samunta daga yankin Meditareniya da yankin Asiya ta Yamma da wasu yankuna na Nahiyar Turai. Yanzu ana shuka ta a sassa daban-daban na duniya.
‘Ya’yan na Hulba ana amfani da shi cikin sinadaran abinci musamman a yankin Asia ta Kudu da Gabas ta Tsakiya da yankin Afurka ta Arewa. Ana kuma amfani da su wajen magani tsawon karni da dama.
A cewar Cibiyar kula da Harkokin Lafiya Wadanda ba na Turawa ba ta (NCCIH), ana amfani da kwayoyi ko ‘ya’yan Hulba domin neman karin ruwan nono ko idan mutum na fama da cushewar ciki. A littafin nan na Encyclopaedia Britannica shima ya nuna cewa ana amfani da ‘ya’yan Hulba kan abin da ya shafi abinci da hada magunguna da suke taimakawa wajen samun ruwan nono a wajen mata.
Duba da wannan ne DUBAWA ta duba batun da’awar cewa ‘ya’yan Hulba suna taimakawa wajen inganta kwan haihuwa da samun daidaiton jiki da karawa mace sha’awa ko ni’ima don gani ko a kimiyance haka abin yake.
Shin a Kimiya an tabbatar da hakan?
DUBAWA ta nazarci bincike na kimiya da aka yi a kan batun amma babu inda ta gano cewa jika ‘ya’yan Hulba na inganta kwayoyin halitta ga mata. An yi nazari kan ‘ya’yan na Hulba amma babu inda DUBAWA ta gano cewa a kimiyance ana inganta kwayoyin haihuwar ko alkinta mahaifa da wannan.
Haka nan binciken ya nuna cewa babu wata sheda da ta nuna cewa jika ‘ya’yan na Hulba na kara sha’awa a wajen mata kamar yadda mai wallafar a Facebook ya nunar.
Shima da’awar cewa wannan jiko na samar da daidaiton sinadarai a jiki na din-din-din na bukatar kara yin bincike, ganin cewa binciken masana kimiya ya gano cewa akwai wasu sinadarai ko kayan abinci da ke tasiri ga yadda jiki ke dabi’arsa.
DUBAWA ta gano cewa yayin da wasu nazarce-nazarce kadan suka nuna cewa ana samun tasirin sauyi a yanayin jiki kan abin da ya shafi halittar kasancewar namiji ko mace (estradiol and free testosterone), wasu nazarce-nazarcen sun nunar da cewa wannan bincike bai yi zurfi ba, kasancewar a wadancan an yi amfani da jikon ne da ya dade ya tsimu sosa,i sabanin irin wannan na hulba da za a jika ‘ya’yanta.
DUBAWA ta kuma gano wani nazari da aka yi kan wasu mata da suke da wata cuta ta daban, kamar Polycystic Ovary Syndrome (PCOS), inda aka yi amfani da sinadarin na Hulba tare da hadawa da maganin Bature, ko da dai an ga samun sauki amma shi ma wannan ai wasu rukuni ne na masu cuta ba za a yi jimulla ba cewa ‘ya’yan Hulba na samar da daidaito na halittar a jikin mace.
Baki daya DUBAWA ta gano cewa shedu da aka tattara ba su nuna goyon baya ga fadin cewa jika ‘ya’yan Hulba na wadannan ayyuka ba da aka bayyana a wallafar da aka yi.A duk lokacin da aka ce ga wani bincike, yana takaita ne akan wani abu, za a ce ana wani shiri sabanin gaba gadi a ce ga wani magani da ake yi da shi.
Matsayar Kwararru
Aisha Muhammed, kwararriya a nazartar halayyar dabi’ar sinadarai a jikin dan Adam a asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano ta fadawa DUBAWA cewa a tsawon shekaru da ta yi tana gudanar da aikinta, bata taba jin cewa akwai wani danitaciya da ke iya daidaita jikin mace na din-din-din ba. Ta kara da cewa shi kula da daidaita yadda sinadaran jikin mace ke aiki yana bukatar yin abubuwa da dama gami da yanayin da jikin mutum yake ya danganta da jikin mutum.
“A bangaren mata ni na kula da yadda halayyar sinadaran jikin mace yake da yadda yake sassauyawa, don haka ba hanya daya ce ake bi ba.Bisa al’ada ya danganta da yanayin rayuwar mace da yadda take rayuwa da ya hadar da irin abinci da take ci da yadda ake motsa jiki da irin magungunan da ake bawa mace a inda ya dace, ana kuma rika bibiya don ganin irin ci gaba da ake samu.
Idan akwai wani dan itace da zai iya daidaita sinadaran jikin mutum su zama daidai da tuni an sanya shi cikin tsarin kula da lafiya.” a cewar liktar.
Ta kara da tsokaci kan da’awar cewa jika ‘ya’yan hulba na inganta samun ni’ima ko sha’awa inda anan ma tace babu wata sheda a kimiyance da za ta mara baya ga wannan da’awa.
”Sha’awa ba cuta ba ce wannan dabi’a ce da ake halittar dan Adam da ita ta kuma danganta daga mutum zuwa mutum.
Duk da cewa ana iya samun mutum ya samu karancin sha’awa wannan na iya faruwa ta dalilin gajiya da kuma batu na lafiya ko rashin samun fahimta tsakanin mace da miji ko wani dalili da ya shafi kwakwalwa.
Don haka ba wani abu guda daya tilo da zaa ce yana magance irin wannan kuma babu wata hujja da zaa ce ‘ya’yan Hulba na kara sha’awa kamar yadda mai da’awar ya nunar.” A cewar likitar Aisha Muhammad.
Ta kara da cewa haka shima batun na inganta kwan haihuwa, shima ya danganta da abubuwa da dama ,musamman shekaru na mace da kuma lafiyar da take da ita ta bangaren haihuwa.
Jeremiah Jonathan, masani kan harkar abinci ya fadawa DUBAWA cewa ‘ya’yan Hulbar a tsawon lokaci a tarihi ana amfani da shi a cikin abinci da ma yin magunguna da ita na gargajiya. A cewarsa abinci ne mai harza da ake kira (Fibre) a Turance kuma yana dauke da sinadarai masu yawa don haka ne masana da masu bincike suka dauki lokaci mai tsawo suna duba alfanu da yake tattare da su a tsawon shekaru.
“Hulba na da sinadarai masu kyau wanda ake amfani da shi don kara inganta lafiyar jiki baki daya. kamar sauran nau’ikan abinci suna taimakawa a lafiya, kar ace ga wani abu da yake magani a likitance, don haka ba zaa ce yana daidaita sinadarai a jikin mutum ba, ko a ce yana inganta kwan haihuwa na mace ko wani abu mai kama da haka.” a cewar Jonathan.
Ya kara da cewa bincike na mayar da hankali ne kan wani sashi na ‘ya’yan hulbar a sanya a dakin gwaji ba wai ace kawai a jika hulba ba a cikin gida. Yace saboda shi a tsarin kimiya ana daukar komai ne bisa adadi, don an ga wani abu daga wani waje ba za a ce kowa ma haka yake ba ace magani ne kamar yadda mai da’awar ta Facebook ya nunar.
A karshe
DUBAWA ta gano cewa babu wata sheda da ta nuna jika ‘ya’yan Hulba a sha don inganta kwan haihuwa na mace ko daidaita sinadaran da ke jikinta. Kwararru sun nunar da cewa akwai abubuwa da dama da ke tasiri a lafiyar jikin mace.
